Zabura 125
Waƙar haurawa. 
 
1 Waɗanda suke dogara ga Ubangiji suna kama da Dutsen Sihiyona,  
wanda ba ya jijjiguwa amma dawwammame ne har abada.   
2 Kamar duwatsun da sun kewaye Urushalima,  
haka Ubangiji ya kewaye mutanensa  
yanzu da har abada kuma.   
   
 
3 Sandar mulkin mugaye ba zai ci gaba da kasance  
a kan ƙasar da take rabon adalai ba,  
domin kada masu adalci su yi amfani  
da hannuwansu su aikata mugunta.   
   
 
4 Ka yi alheri, ya Ubangiji, ga waɗanda suke nagartattu,  
ga waɗanda suke masu aikata gaskiya a zuciyarsu.   
5 Amma waɗanda suka juye ga karkatattun hanyoyi  
Ubangiji zai kore su tare da masu aikata mugunta.  
   
 
Salama tă kasance tare da Isra’ila.