Zabura 126
Waƙar haurawa. 
 
1 Sa’ad da Ubangiji ya dawo da kamammu zuwa Sihiyona,  
mun kasance kamar mutanen da suka yi mafarki.   
2 Bakunanmu sun cika da dariya,  
harsunanmu da waƙoƙin farin ciki.  
Sai ana faɗi a cikin al’ummai,  
“Ubangiji ya aikata manyan abubuwa dominsu.”   
3 Ubangiji ya aikata manyan abubuwa dominmu,  
mun kuwa cika da farin ciki.   
   
 
4 Ka maido da wadatarmu, ya Ubangiji  
kamar rafuffuka a Negeb.   
5 Waɗanda suka yi shuka da hawaye  
za su yi girbi da waƙoƙin farin ciki.   
6 Shi da ya fita yana kuka,  
riƙe da iri don shuki,  
zai dawo da waƙoƙin farin ciki,  
ɗauke da dammuna.