Zabura 124
Waƙar haurawa. Ta Dawuda. 
 
1 Da ba don Ubangiji ya kasance a gefenmu ba,  
bari Isra’ila yă ce,   
2 da ba don Ubangiji ya kasance a gefenmu ba  
sa’ad da aka auka mana,   
3 sa’ad da fushinsu ya ƙuna a kanmu,  
ai, da sun haɗiye mu da rai;   
4 da rigyawa ta kwashe mu,  
da ambaliya ta rufe mu.   
5 Da ruwa mai hauka  
ya share mu ƙaf.   
   
 
6 Yabo ya tabbata ga Ubangiji,  
wanda bai bari aka yayyage mu da haƙoransu ba.   
7 Mun tsira kamar tsuntsu  
daga tarkon mai farauta;  
an tsinke tarko,  
muka kuwa tsira.   
8 Taimakonmu yana a sunan Ubangiji,  
Wanda ya yi sama da ƙasa.