Zabura 123
Waƙar haurawa. 
 
1 Na tā da idanuna gare ka,  
gare ka da kursiyinka yake cikin sama.   
2 Kamar yadda idanun bayi suna duban hannun maigidansu,  
kamar yadda idanun baiwa suna duban hannun uwargijiyarta,  
haka idanunmu suna duban Ubangiji Allahnmu,  
sai ya nuna mana jinƙansa.   
   
 
3 Ka yi mana jinƙai, ya Ubangiji, ka yi mana jinƙai,  
gama mun jimre da reni mai yawa.   
4 Mun jimre da wulaƙanci  
daga masu girman kai,  
reni mai yawa daga masu fariya.