Zabura 111
1 Yabi Ubangiji.  
   
 
Zan ɗaukaka Ubangiji da dukan zuciyata  
a cikin majalisar masu aikata gaskiya da kuma a cikin taro.   
   
 
2 Ayyukan Ubangiji da girma suke;  
dukan waɗanda suke farin ciki da su suna tunaninsu.   
3 Ayyukansa masu ɗaukaka da kuma daraja ne,  
adalcinsa kuma zai dawwama har abada.   
4 Ya sa a tuna da abubuwa masu banmamaki nasa;  
Ubangiji mai alheri ne mai tausayi kuma.   
5 Yana ba da abinci ga waɗanda suke tsoronsa;  
yakan tuna da alkawarinsa har abada.   
   
 
6 Ya nuna wa mutanensa ikon ayyukansa,  
yana ba su ƙasashen waɗansu al’ummai.   
7 Ayyukan hannuwansa masu aminci ne da kuma gaskiya;  
dukan farillansa abin dogara ne.   
8 Tsayayyu ne har abada abadin,  
ana yinsu cikin aminci da kuma gaskiya.   
9 Yana ba da ceto ga mutanensa;  
ya kafa alkawarinsa har abada,  
tsarki da banrazana ne sunansa.   
   
 
10 Tsoron Ubangiji ne mafarin hikima;  
dukan waɗanda suke bin farillansa suna da ganewa mai kyau.  
Gare shi ne madawwamin yabo.