Zabura 112
1 Yabi Ubangiji.  
   
 
Mai albarka ne mutumin da yake tsoron Ubangiji,  
wanda yakan sami farin ciki mai girma a umarnansa.   
   
 
2 ’Ya’yansa za su zama manya a ƙasar;  
tsaran masu aikata gaskiya za su sami albarka.   
3 Wadata da arziki suna a cikin gidansa,  
adalcinsa zai dawwama har abada.   
4 Ko a cikin duhu haske kan haskaka wa mai aikata gaskiya,  
mai alheri mai tausayi da kuma mai adalci.   
5 Abu mai kyau zai zo masa shi da yake kyauta yake kuma ba da bashi hannu sake,  
shi da yake yin al’amuransa cikin gaskiya.   
   
 
6 Tabbatacce ba zai taɓa jijjigu ba;  
za a tuna da mai adalci har abada.   
7 Ba zai ji tsoron labari marar daɗi ba;  
zuciyarsa tsayayyiya ce, tana dogara ga Ubangiji.   
8 Zuciyarsa tana da kāriya, ba zai ji tsoro ba;  
a ƙarshe zai zama mai nasara a kan maƙiyansa.   
9 Ya rarraba kyautansa ga matalauta,  
adalcinsa zai dawwama har abada;  
za a ɗaga ƙahonsa sama da bangirma.   
   
 
10 Mugun mutum zai gani yă kuma yi fushi,  
zai ciza haƙora yă kuma lalace;  
sha’awace-sha’awacen mugaye za su zo ga ƙarshe.