Zabura 110
Ta Dawuda. Zabura ce. 
 
1 Ubangiji ya ce wa Ubangijina,  
“Zauna a hannun damana,  
sai na sa abokan gābanka  
su zama matashin sawunka.”   
   
 
2 Ubangiji zai fadada ikon sandan mulkinka daga Sihiyona  
za ka yi mulki a tsakiyar abokan gābanka.   
3 Rundunarka za su so yin yaƙi  
a ranarka ta yaƙi.  
Saye cikin ɗaukaka mai tsarki,  
daga cikin ciki na safiya  
za ka karɓi raɓar ƙuruciyarka.   
   
 
4 Ubangiji ya rantse  
ba zai kuma canja zuciyarsa ba,  
“Kai firist ne har abada,  
bisa ga tsarin Melkizedek.”   
   
 
5 Ubangiji yana a hannun damanka;  
zai murƙushe sarakuna a ranar fushinsa.   
6 Zai hukunta al’ummai, yana tarawa gawawwaki  
yana kuma murƙushe masu mulkin dukan duniya.   
7 Zai sha daga rafin da yake kusa da hanya;  
saboda haka zai ɗaga kansa sama.