Zabura 11
Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Don busa. Ta Dawuda. 
 
1 A wurin Ubangiji ne nake samun mafaka.  
Yaya za ku ce mini,  
“Ka yi firiya kamar tsuntsu zuwa duwatsu.   
2 Gama duba, mugaye sun tanƙware bakkunansu;  
sun kuma ɗana kibiyoyinsu  
don su harbi mutanen kirki a zuciya  
daga cikin duhu.   
3 Sa’ad da aka tumɓuke tushe,  
me adali zai iya yi?”   
   
 
4 Ubangiji yana cikin haikalinsa mai tsarki;  
Ubangiji yana a kursiyinsa a sama.  
Yana kallon ’ya’yan mutane;  
idanunsa suna bincike su.   
5 Ubangiji yana bincike adalai,  
amma ransa yana ƙi mugaye  
da masu son rikici.   
6 A kan mugaye zai zuba  
garwashin wuta mai zafi da kuma kibiritu;  
iska mai zafi zai zama rabonsu.   
   
 
7 Gama Ubangiji mai adalci ne,  
yana ƙaunar gaskiya  
masu adalci za su ga fuskarsa.