*
Zabura 10
Don me, ya Ubangiji, kake tsaya can da nesa?
Me ya sa kake ɓoye kanka a lokutan wahala?
 
Cikin fariyarsa mugun mutum yakan cuci marasa ƙarfi,
waɗanda yake kama cikin makircin da ya shirya.
Yakan yi taƙama da ƙulle-ƙullen zuciyarsa;
yana albarkaci mai haɗama yana kuma ƙin Ubangiji.
Cikin ɗaga kai mutum ba ya neman Allah;
cikin tunaninsa ba ya ba da wata dama saboda Allah.
Hanyoyinsa kullum sukan yi nasara;
yana da girman kai kuma dokokinka suna nesa da shi;
yakan yi wa dukan abokan gābansa duban reni.
Yakan ce wa kansa, “Ba abin da zai girgiza ni;
kullum zan yi murna ba zan taɓa shiga wahala ba.”
 
Bakinsa ya cika da zage-zage da ƙarairayi da kuma barazana;
wahala da mugunta suna a ƙarƙashin harshensa.
Yakan yi kwanto kusa da ƙauyuka;
daga kwanton yakan kashe marar laifi.
Yana kallon waɗanda za su shiga hannunsa a ɓoye.
Yakan yi kwanto a ɓoye kamar zaki.
Yakan yi kwanto don yă kama marasa ƙarfi;
yakan kama marasa ƙarfi yă ja su cikin ragarsa.
10 Yakan ragargaza waɗanda suka shiga hannu, su fāɗi;
sukan fāɗi a ƙarƙashin ƙarfinsa.
11 Yakan ce wa kansa, “Ai, Allah ya manta;
ya rufe fuskarsa ba ya gani.”
 
12 Ka tashi, Ubangiji! Ka hukunta miyagu, ya Allah.
Kada ka manta da marasa ƙarfi.
13 Don me mugun mutum zai ƙi Allah?
Don me yakan ce wa kansa,
“Allah ba zai nemi hakki daga gare ni ba”?
14 Amma kai, ya Allah, kana gani wahala da baƙin ciki;
kana lura da yadda suke ɗaukansu a hannu.
Marar taimako kan danƙa kansa gare ka;
kai ne mai taimakon marayu
15 Ka karye hannun mugaye da kuma mugun mutum;
ka nemi hakki daga gare shi saboda muguntar
da ba za a gane ba.
 
16 Ubangiji Sarkin har abada abadin ne;
al’ummai za su hallaka daga ƙasarsa.
17 Kakan ji, ya Ubangiji sha’awar mai shan wahala;
kakan ƙarfafa su, ka kuma saurari kukansu,
18 kana kāre marayu da waɗanda aka danne,
domin mutum, wanda yake na duniya
kada ƙara haddasa wata razana.
* Zabura 10: Mai yiwuwa Zabura 9 da 10 tun ainihi waƙa guda ce, ɓangarori mai ƙunshe da layi masu yawa waɗanda suka fara da harufan Ibraniyancin da suke bin juna. A Seftuwajin zabura guda ce.