*
Zabura 9
Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Ga muryar “Mutuwar Ɗa.” Zabura ta Dawuda.
Zan yabe ka, ya Ubangiji, da dukan zuciyata;
zan faɗa dukan abubuwan banmamakinka.
Zan yi murna in kuma yi farin ciki a cikinka;
zan rera yabo ga sunanka, ya Mafi Ɗaukaka.
 
Abokan gābana sun ja da baya;
suka yi tuntuɓe suka hallaka a gabanka.
Gama ka tabbata da gaskiyata da kuma abin da nake yi;
ka zauna a kujerarka, kana yin shari’a da adalci.
Ka tsawata wa ƙasashe ka kuma hallakar da mugaye;
ka shafe sunansu har abada abadin.
Lalaci marar ƙarewa ya cimma abokan gābanmu,
ka tuttumɓuke biranensu;
yadda ma ba aka ƙara tunaninsu.
 
Ubangiji yana mulki har abada;
ya kafa kujerarsa don shari’a.
Zai hukunta duniya da adalci;
zai yi mulkin mutane cikin gaskiya.
Ubangiji shi ne mafakan waɗanda ake danniya,
mafaka a lokutan wahala.
10 Waɗanda suka san sunanka za su dogara da kai,
gama kai, Ubangiji, ba ka taɓa yashe waɗanda suke nemanka ba.
 
11 Rera yabai ga Ubangiji, wanda yake zaune a kursiyi a Sihiyona;
yi shela a cikin al’ummai abin da ya aikata.
12 Gama shi da yakan ɗauki fansa a kan mai kisa yakan tuna;
ba ya ƙyale kukan masu wahala.
 
13 Ya Ubangiji, dubi yadda abokan gābana suna tsananta mini!
Ka yi jinƙai ka kuma ɗaga ni daga ƙofofin mutuwa,
14 don in furta yabanka
cikin ƙofofin ’Yar Sihiyona
a can kuwa in yi farin ciki cikin cetonka.
 
15 Al’umma sun fāɗa cikin ramin da suka haƙa wa waɗansu;
aka kama ƙafafunsu a ragar da suka ɓoye.
16 An san Ubangiji ta wurin gaskiyarsa;
an kama mugaye da aikin hannuwansu.
Haggayiyon.
Sela
17 Mugaye za su koma kabari,
dukan al’umman da suka manta da Allah.
18 Amma har abada ba za a manta da mai bukata ba,
ba kuwa sa zuciyar mai wahala zai taɓa hallaka.
 
19 Ka tashi, ya Ubangiji, kada ka bar wani yă yi nasara;
bari a hukunta al’ummai a gabanka.
20 Ka buge su da rawar jiki, ya Ubangiji;
bari al’ummai su sani su mutane ne kurum.
Sela
* Zabura 9: Mai yiwuwa Zabura 9 da 10 tun ainihi waƙa guda ce, ɓangarori mai ƙunshe da layi masu yawa waɗanda suka fara da harufan Ibraniyancin da suke bin juna. A Seftuwajin zabura guda ce. Zabura 9:16 Ko kuwa Tunani; mai yiwuwa salon kiɗi ne.