Zabura 12
Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Da kayan kiɗi. Bisa ga sheminit. Zabura ta Dawuda. 
 
1 Ka taimaka, Ubangiji, gama masu tsoron Allah ba sa nan kuma;  
masu aminci sun ɓace daga cikin mutane.   
2 Kowa yana yi wa maƙwabcinsa ƙarya;  
zaƙin bakinsu maganar ƙarya ce  
suna cike da ruɗu a zukatansu.   
   
 
3 Bari Ubangiji yă yanke dukan zaƙin bakinsu  
da kuma kowane harshe mai fariya,   
4 masu cewa,  
“Da harsunanmu za mu yi nasara;  
leɓunanmu za su kāre mu, wane ne maigidanmu?”   
   
 
5 “Saboda danniyar marasa ƙarfi da kuma nishin masu bukata,  
zan tashi yanzu,” in ji Ubangiji.  
“Zan kāre su daga masu yin musu sharri.”   
6 Kalmomin Ubangiji kuwa ba su da kuskure,  
kamar azurfan da aka tace cikin matoyan yumɓu,  
aka tsabtacce sau bakwai.   
   
 
7 Ya Ubangiji, za ka kiyaye mu lafiya  
ka tsare mu daga irin mutanen nan har abada.   
8 Mugaye suna yawo a sake  
sa’ad da ake girmama abin da ba shi da kyau a cikin mutane.