51
Ubangiji ya ce,
“Ga shi, zan zuga ruhun mai hallakarwa
a kan Babilon da mutanen Leb Kamai.
Zan aika da baƙi zuwa Babilon
su casa ta su kuma yi kaca-kaca da ƙasarta;
za su yi hamayya da ita a kowane gefe
a ranar masifarta.
Kada ku bar maharbi yă ja bakansa,
kada kuma ku bari yă sa kayan yaƙinsa.
Kada ku rage samarinta,
ku hallaka sojojinta ƙaf.
Za su fāɗi matattu a ƙasar Babilon,
da munanan raunuka a titunanta.
Gama Ubangiji Maɗaukaki, Allah na Isra’ila da Yahuda
bai yashe su ba,
ko da yake ƙasarsu* cike da take da laifi
a gaban Mai Tsarki na Isra’ila.
 
“Ku gudu daga cikin Babilon!
Bari kowa yă ceci ransa!
Kada a hallaka saboda zunubanta.
Gama lokaci ne don ramuwar Ubangiji,
zai sāka mata bisa ga alhakinta.
Babilon ta zama ƙoƙon zinariya a hannun Ubangiji,
ta sa dukan duniya ta yi maye.
Ƙasashe sun sha ruwan inabinta,
saboda haka yanzu sun haukace.
Farat ɗaya Babilon za tă fāɗi ta farfashe.
Ku yi kuka dominta!
Ku samo mata magani saboda azabarta;
wataƙila za a iya warkar da ita.
 
“ ‘Da mun warkar da Babilon,
amma ba za tă warke ba;
mu ƙyale ta kowane yă koma garinsu,
gama hukuncinta ya kai sammai,
ya yi tsawo kamar gizagizai.’
 
10 “ ‘Ubangiji ya baratar da mu;
zo mu tafi mu yi shelarsa a Sihiyona
mu faɗa abin da Ubangiji Allahnmu ya yi.’
 
11 “Ku wasa kibiyoyi,
ku ɗauko garkuwoyi!
Ubangiji ya zuga sarakunan Medes,
domin niyyarsa ce yă hallaka Babilon.
Ubangiji zai yi ramuwa,
zai yi ramuwa saboda haikalinsa.
12 Ku tā da tuta gāba da katangan Babilon!
Ku ƙara matsara,
ku kafa masu tsaro,
ku shirya kwanto!
Ga shi, Ubangiji zai aikata abin da ya faɗa
umarninsa a kan mutanen Babilon.
13 Ke da kike zama kusa da ruwaye
da kike kuma wadatar dukiya,
ƙarshenki ya zo,
lokaci ya yi da za a kau da ke.
14  Ubangiji Maɗaukaki ya rantse da zatinsa, ya ce
Tabbatacce zan cika ka da mutane kamar fāra,
za su kuwa yi sowa don nasara a kanka.
(Irmiya 10.12-16)
15 “Ya halicci ƙasa ta wurin ikonsa;
ya kafa duniya ta wurin hikimarsa,
ya kuma shimfiɗa sammai ta wurin fahiminsa.
16 Sa’ad da ya yi tsawa ruwan da suke sammai sukan yi ruri;
yakan sa gizagizai su tashi daga ƙarshen duniya.
Yakan tura walƙiya tare da ruwan sama
yakan kuma saki iska daga cikin taskokinsa.
 
17 “Kowane mutum marar azanci ne kuma ba shi da sani;
kowane maƙerin zinariya yakan sha kunya daga wurin gumakansa.
Siffofinsa na ƙarya ne;
babu numfashi a cikinsu.
18 Su marasa amfani ne, abubuwan ba’a ne kawai;
sa’ad da lokacin hukuncinsu ya kai, za su hallaka.
19 Wanda yake na wajen Yaƙub ba kamar waɗannan ba ne,
gama shi ne Mahalicci dukan abu,
har da kabilar abin gādonsa,
Ubangiji Maɗaukaki ne sunansa.
 
20 “Kai ne kulkin yaƙina,
kayan yaƙina,
da kai ne na ragargaza ƙasashe,
da kai ne na hallaka mulkoki,
21 da kai ne na ragargaza doki da mahayi,
da kai ne na ragargaza keken yaƙin da matuƙi,
22 da kai ne na ragargaza miji da mata,
da kai ne na ragargaza tsoho da saurayi,
da kai ne na ragargaza saurayi da budurwa,
23 da kai ne na ragargaza makiyayi da garke,
da kai ne na ragargaza manoma da dawakan noma,
da kai ne na ragargaza masu mulki da shugabanni.
24 “Zan sāka wa Babilon da dukan mazaunan Babilon a idanunku saboda dukan muguntar da suka aikata a Sihiyona,” in ji Ubangiji.
25 “Ga shi, ina gāba da kai, ya ke dutse mai hallakarwa,
wadda ta hallaka duniya duka,”
in ji Ubangiji.
“Zan miƙa hannuna gāba da ke,
zan mirgina ƙasa daga ƙwanƙolin dutse,
zan maishe ki ƙonannen dutse.
26 Ba za a ɗauki dutsen yin kusurwa daga gare ki ba
ko na kafa harsashen gini,
gama za ki zama marar amfani har abada,” in ji Ubangiji.
 
27 “Ku tā da tuta a ƙasa!
Ku busa ƙahoni a cikin ƙasashe!
Ku shirya ƙasashe don yaƙi da ita,
ku kira waɗannan mulkokin gāba da ita.
Ararat, Minni, da Ashkenaz.
A naɗa shugaba gāba da ita;
ku shirya dawakai kamar fāra.
28 Ku shirya ƙasashe don yaƙi da ita,
sarakunan Medes,
gwamnoninsu da dukan masu shugabancinsu
da kowace ƙasar da take ƙarƙashin mulkinsu.
29 Ƙasa ta girgiza tana makyarkyata
saboda nufin Ubangiji na gāba da Babilon ya tabbata,
nufinsa na mai da ƙasar Babilon kufai
don kada kowa yă zauna a can.
30 Sojojin Babilon sun daina yaƙi,
suna zaune a cikin kagaransu.
Ƙarfinsu ya ƙare,
sun zama mata.
An sa wa wuraren zamanta wuta,
an karya ƙyamaren ƙofofin garinta.
31 Maguji yana biye da maguji a guje,
jakada yana biye da jakada,
don su faɗa wa sarkin Babilon,
cewa an ci birninsa a kowane gefe.
32 An ƙwace mashigai
aka ƙone fadamu da wuta,
sojoji kuma suka giggice.”
33 Ni Ubangiji Maɗaukaki, Allah na Isra’ila na ce,
“’Yar Babilon kamar daɓen masussuka
a lokacin da ake sussuka,
ba da daɗewa ba lokacin girbe ta zai zo.”
 
34 “Nebukadnezzar sarkin Babilon ya cinye mu,
ya sa muka rikice,
ya maishe mu kamar tulun da babu kome a cikinsa.
Ya cinye mu kamar yadda dodon ruwa yakan yi
ya kuma cika cikinsa da kayan marmarinmu,
sa’an nan kuma ya yi amanmu.
35 Bari abin da aka yi wa jikinmu yă kasance a bisa Babilon,”
in ji mazaunan Sihiyona.
“Bari jininmu yă kasance a kan waɗanda suke zama a Babilon,”
in ji Urushalima.
36 Saboda haka ga abin da Ubangiji ya ce,
“Duba, zan tsaya muku,
zan ɗaukar muku fansa,
zan sa tekunta kafe
in kuma sa maɓulɓulanta su ƙafe.
37 Babilon za tă zama tarin juji,
wurin zaman diloli,
abin ƙyama da abar ba’a,
inda ba kowa.
38 Mutanenta duk suna ruri kamar zakoki,
suna gurnani kamar ’ya’yan zaki.
39 Amma sa’ad da aka farkar da su,
zan yi musu biki
in sa su sha su bugu,
domin yi sowa da dariya,
sa’an nan su shiga barcin da ba za su farka ba,”
in ji Ubangiji.
40 “Zan sauko da su
kamar tumaki zuwa mayanka,
kamar raguna da bunsurai.
 
41 “Yadda za a ci Sheshak,
taƙamar duniya duka za tă daina!
Babilon za tă zama abar ƙyama
a cikin al’ummai!
42 Teku zai malalo a kan Babilon,
raƙumansa masu hauka za su rufe ta.
43 Garuruwanta sun zama abin kufai,
za tă zama hamada inda ba ruwa,
ƙasar da ba mazauna,
ba kuma mutumin da zai ratsa ta cikinta.
44 Zan hukunta Bel a Babilon,
in sa ya yi aman abin da ya haɗiye.
Ƙasashe ba za su ƙara bumbuntowa wurinsa ba.
Katangan Babilon kuwa za tă rushe!
 
45 “Ku fito daga cikinta, jama’ata!
Ku tsere da ranku!
Ku tsere daga zafin fushin Ubangiji.
46 Kada zuciyarku tă yi suwu ko ku ji tsoro
sa’ad da aka ji labarin a ƙasar,
labari guda a wannan shekara, wani kuma a ta biye,
labarin hargitsi a ƙasar
mai mulki ya tasar wa mai mulki.
47 Gama kwanaki tabbatacce suna zuwa,
sa’ad da zan hukunta gumakan Babilon,
zan kunyatar da dukan ƙasar
kuma matattunta duk za su kwanta a cikinta.
48 Sa’an nan sama da ƙasa da dukan abin da yake cikinsu,
za su yi sowa ta murna a kan Babilon,
gama daga arewa
masu hallakarwa su auko mata,”
in ji Ubangiji.
 
49 “Babilon za tă fāɗi saboda kisassun mutanen Isra’ila,
kamar dai yadda kisassu dukan duniya
suka fāɗi saboda Babilon.
50 Ku waɗanda kuka tsere wa takobi,
ku gudu kada ku tsaya!
Ku tuna da Ubangiji a ƙasa mai nesa,
ku kuma yi ta tunani a kan Urushalima.”
 
51 “Mun sha kunya
saboda zargin da ake yi mana
kunya ta rufe mu,
domin baƙi sun shiga
tsarkakan wurare na gidan Ubangiji.”
 
52 “Amma kwanaki suna zuwa,” in ji Ubangiji,
“sa’ad da zan hukunta gumakanta,
da kuma a dukan ƙasarta
waɗanda aka yi wa rauni, za su yi nishi.
53 Ko da Babilon za tă kai sararin sama ne,
ta gina kagaranta mai ƙarfi,
duk da haka zan aiki masu hallakarwa a kanta,”
in ji Ubangiji.
 
54 “Ku ji muryar kuka daga Babilon,
Da hargowar babbar hallakarwa
daga ƙasar Babiloniyawa!
55 Gama Ubangiji zai rushe Babilon,
zai sa ta ƙame bakinta na alfarma.
Sojoji za su yi ta kutsawa kamar raƙuman ruwa;
suna tā da muryoyinsu.
56 Gama mai hallakarwa ya auka wa Babilon,
a kama sojojinta,
a kuma kakkarya bakkunansu.
Gama Ubangiji shi Allah ne mai sakayya;
zai yi sakayya sosai.
57 Zan sa mahukuntanta da masu hikimarta,
gwamnoninta, shugabanninta da sojojinta su sha su bugu;
za su dinga yin barcin da ba za su farka ba,”
in ji Sarkin, mai suna Ubangiji Maɗaukaki.
58 Ni Ubangiji Maɗaukaki, na ce,
“Za a baje katangan nan na Babilon mai kauri
za a kuma ƙone dogayen ƙyamarenta da wuta;
mutane sun wahalar da kansu a banza,
al’umma sun yi wahala kawai domin wutar lalata.”
59 Jawabin da annabi Irmiya ya ba Serahiya, ɗan Neriya, wato, jikan Ma’asehiya, lokacin da ya tafi tare da Zedekiya, Sarkin Yahuda, zuwa Babilon a shekara ta huɗu ta mulkinsa. Serahiya shi ne shugaba mai lura da gidajen saukar baƙi. 60 Irmiya ya rubuta a littafi dukan masifun da za su auko wa Babilon, wato, dukan wannan magana da aka rubuta a kan Babilon. 61 Irmiya kuwa ya ce wa Serahiya, “Lokacin da ka kai Babilon, sai ka karanta dukan maganan nan. 62 Ka kuma ce, ‘Ya Ubangiji, kai ne ka yi magana a kan wannan wuri, cewa za ka lalatar da shi, har ba abin da zai zauna a ciki, mutum ko dabba. Wurin zai zama kufai har abada.’ 63 Sa’ad da ka gama karanta wannan littafi, sai ka ɗaura wa littafin dutse, sa’an nan ka jefar da shi tsakiyar Kogin Yuferites. 64 Sa’an nan ka ce, ‘Haka Babilon za tă nutse, ba za tă ƙara tashi ba saboda masifar da zan kawo mata. Mutanenta kuwa za su fāɗi.’ ”
Wannan shi ne ƙarshen kalmomin Irmiya.
 
* 51:5 Ko kuwa / kuma ƙasar Babiloniyawa