50
Saƙo game da Babilon
Ga maganar Ubangiji da ya yi ta wurin Irmiya annabi game da Babilon da kuma ƙasar Babiloniyawa.
“Ka yi shela ka kuma furta a cikin al’ummai,
ka tā da tuta ka kuma furta;
kada ku ɓoye kome, amma ku ce,
‘Za a ci Babilon da yaƙi;
za a kunyata Bel,
Marduk ya cika da tsoro.
Siffofinta za su sha kunya
gumakanta za su cika da tsoro.’
Al’umma daga arewa za tă fāɗa mata
su mai da ƙasar kango.
Ba wanda zai zauna a cikinta;
mutane da dabbobi za su gudu.
 
“A kwanakin nan, a wannan lokaci,”
in ji Ubangiji,
“mutanen Isra’ila da mutanen Yahuda gaba ɗaya
za su tafi cikin hawaye su nemi Ubangiji Allahnsu.
Za su tambayi hanyar zuwa Sihiyona
su kuma juya fuskokinsu wajenta.
Za su zo su haɗa kansu ga Ubangiji
a madawwamin alkawari
da ba za a manta da shi ba.
 
“Mutanena sun zama ɓatattun tumaki;
makiyayansu sun bauɗar da su
suka sa suna ta yawo a cikin duwatsu.
Sun yi ta yawo a bisa dutse da tudu
suka manta wurin hutunsu.
Duk wanda ya same su ya cinye su;
abokan gābansu suka ce, ‘Ba mu da laifi,
gama sun yi zunubi wa Ubangiji, wurin kiwonsu na gaske,
Ubangiji, abin sa zuciyar kakanninsu.’
 
“Ku gudu daga Babilon;
ku bar ƙasar Babiloniyawa,
ku zama kamar awakin da suke bi da garke.
Gama zan kuta in kuma kawo a kan Babilon
haɗinkan manyan al’ummai na arewa.
Za su ja dāgār gāba da ita,
kuma daga arewa za a ci ta da yaƙi.
Kibiyoyinsu za su zama kamar na gwanayen jarumawa
waɗanda ba sa dawowa hannu wofi.
10 Saboda haka za a washe Babiloniyawa;
dukan waɗanda suka washe ta za su ƙoshi,”
in ji Ubangiji.
 
11 “Saboda kuna farin ciki kuna kuma murna,
ku da kuka washe gādona,
domin kuna tsalle kamar karsana mai sussuka hatsi
kuna kuma haniniya kamar ingarmu.
12 Mahaifiyarku za tă sha babbar kunya;
ita da ta haife ku za tă sha kunya.
Za tă zama mafi ƙanƙanta na al’ummai,
jeji, busasshiyar ƙasa, hamada.
13 Saboda fushin Ubangiji ba za tă zauna a cikinta ba
amma za tă zama kufai gaba ɗaya.
Duk waɗanda suka wuce Babilon za su ji tsoro su kuma yi tsaki
saboda dukan mikinta.
 
14 “Ku ja dāgā kewaye da Babilon,
dukanku waɗanda kuke jan baka.
Ku harbe ta! Kada ku rage kibiyoyi,
gama ta yi zunubi ga Ubangiji.
15 Ku yi kuwwa a kanta a kowane gefe!
Ta miƙa wuya, hasumiyarta ta fāɗi,
katangarta sun rushe.
Da yake wannan sakayya ce ta Ubangiji,
ku ɗauki fansa a kanta;
yi mata yadda ta yi wa waɗansu.
16 Ku datse wa Babilon mai shuka,
da mai girbi lauje a lokacin girbi.
Saboda takobin mai zalunci
bari kowa ya koma ga mutanensa,
bari kowa ya gudu zuwa ga ƙasarsa.
 
17 “Isra’ila garke ne da ya watse
da zakoki suka kora.
Na farkon da ya cinye shi
sarkin Assuriya ne;
na ƙarshen da ya ragargaza ƙasusuwansa
Nebukadnezzar sarkin Babilon ne.”
18 Saboda haka ga abin da Ubangiji Maɗaukaki, Allah na Isra’ila, yana cewa,
“Zan hukunta sarkin Babilon da ƙasarsa
yadda na hukunta sarkin Assuriya.
19 Amma zan komo da Isra’ila zuwa wurin kiwonsa
zai kuwa yi kiwo a Karmel da Bashan;
zai ƙosar da marmarinsa
a tuddan Efraim da Gileyad.
20 A kwanakin nan, da kuma a lokacin nan,”
in ji Ubangiji,
“za a yi bincike don laifin Isra’ila,
amma ba za a samu ba,
kuma don zunubin Yahuda,
amma ba za a sami wani abu ba,
gama zan gafarta wa raguwar da na rage.
 
21 “Ku fāɗa wa ƙasar Meratayim
da waɗanda suke zama a Fekod.
Ku fafara, ku kashe kuma hallaka su sarai,”
in ji Ubangiji.
“Ku aikata dukan abin da na umarce ku.
22 Hargowar yaƙi tana a ƙasar,
hargowar babbar hallaka!
23 Dubi yadda aka karya aka kuma ragargaza
gudumar dukan duniya!
Dubi yadda Babilon ta zama kufai
a cikin al’ummai!
24 Na sa miki tarko, Babilon,
kika kuwa kamu kafin ki sani;
aka same ki aka kuma kama ki
domin kin tayar wa Ubangiji.
25  Ubangiji ya buɗe taskar makamansa
ya fitar da makaman fushinsa,
gama Maɗaukaki Ubangiji Mai Iko Duka yana da aikin da zai yi
a ƙasar Babiloniyawa.
26 Ku zo ku yi gāba da ita daga nesa.
Ku buɗe rumbunanta;
ku jibga ta kamar tsibin hatsi.
Ku hallaka ta sarai
kada ku bar mata raguwa.
27 Ku kashe dukan ’yan bijimanta
bari su gangara zuwa mayanka!
Kaitonsu! Gama ranansu ta zo,
lokaci ya yi da za a hukunta su.
28 Ku saurari masu gudun hijira da masu neman mafaka daga Babilon
suna furtawa a Sihiyona
yadda Ubangiji Allahnmu ya ɗauki fansa,
fansa domin haikalinsa.
 
29 “Ku kira ’yan baka a kan Babilon,
dukan waɗanda suke jan baka.
Ku yi sansani kewaye da ita duka;
kada ku bar wani ya tsira.
Ku sāka mata don ayyukanta;
ku yi mata yadda ta yi.
Gama ta tayar wa Ubangiji,
Mai Tsarkin nan na Isra’ila.
30 Saboda haka, samarinta za su fāɗi a tituna;
za a kawar da dukan sojojinta a wannan rana,”
in ji Ubangiji.
31 “Ga shi, ina gāba da ke, ya ke mai girman kai,”
in ji Ubangiji, Ubangiji Maɗaukaki,
“gama ranarki ta zo,
lokacin da za a hukunta ki.
32 Mai ɗaga kai za tă yi tuntuɓe ta kuma fāɗi
kuma ba wanda zai taimake ta tă tashi;
zan hura wuta a garuruwanta
da za tă cinye duk waɗanda suke kewaye da ita.”
33 Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki yana cewa,
“An danne mutanen Isra’ila, haka ma mutanen Yahuda.
Dukan waɗanda suka kama su suna riƙe su kankan,
suna kin barinsu su tafi.
34 Duk da haka Mai Fansarsu yana da ƙarfi;
Ubangiji Maɗaukaki ne sunansa.
Zai kāre muradunsu gabagadi
don yă kawo hutu ga ƙasarsu,
amma rashin hutu ga waɗanda suke zaune a Babilon.
 
35 “Akwai takobi a kan Babiloniyawa!”
In ji Ubangiji
“a kan waɗanda suke zama a Babilon
da kuma a kan fadawanta da masu hikimarta!
36 Akwai takobi a kan annabawan ƙaryanta!
Za su zama wawaye.
Akwai takobi a kan jarumawanta!
Za su cika da tsoro.
37 Akwai takobi a kan dawakanta da kekunan yaƙinta
da kuma dukan baƙin da suke cikin mayaƙanta!
Za su zama mata.
Akwai takobi a kan dukiyarta!
Za a washe su.
38 Fări a kan ruwanta!
Za su bushe ƙaf.
Gama ƙasa ce ta gumaka,
gumakan da za su haukace da tsoro.
 
39 “Saboda haka halittun hamada da kuraye za su zauna a can,
a can kuma mujiya za tă zauna.
Ba za a ƙara zauna
ko a yi zama a cikinta ba daga tsara zuwa tsara.
40 Yadda Allah ya tumɓuke Sodom da Gomorra
tare da maƙwabtan garuruwansu,”
in ji Ubangiji
“haka ma ba wanda zai zauna a can;
ba wani da zai zauna a cikinta.
 
41 “Duba! Ga sojoji suna zuwa daga arewa;
babbar al’umma da sarakuna masu yawa
suna tahowa daga iyakokin duniya.
42 Suna riƙe da baka da māshi;
mugaye ne marasa tausayi.
Amonsu ya yi kamar rurin teku
yayinda suke hawan dawakansu;
suna zuwa kamar mutane a dāgār yaƙi
don su fāɗa miki, ya Diyar Babilon.
43 Sarkin Babilon ya ji rahotanni game da su,
hannunsa kuma ya yi laƙwas.
Wahala ta kama shi,
zafi kamar na mace mai naƙuda.
44 Kamar zaki mai haurawa daga kurmin Urdun
zuwa wurin kiwo mai dausayi,
zan fafare Babilon daga ƙasan nan da nan.
Wane ne zaɓaɓɓen da zan naɗa domin wannan?
Wane ne kamar ni da zai kalubalance ni?
Kuma wanda makiyayi zai iya tsaya gāba da ni?”
 
45 Saboda haka, ku ji abin da Ubangiji ya shirya a kan Babilon,
abin da ya nufa gāba da ƙasar Babiloniyawa.
Za a kwashe ƙananan garkensu a tafi;
zai hallaka wurin kiwonsu sarai saboda su.
46 Da jin an ci Babilon da yaƙi sai duniya ta girgiza;
za a ji kukanta cikin al’ummai.