52
Fāɗuwar Urushalima
(2 Sarakuna 24.18–25.30; 2 Tarihi 36.11-21)
Zedekiya yana da shekara ashirin da ɗaya sa’ad da ya ci sarauta. Ya yi mulki a Urushalima shekara goma sha ɗaya. Sunan uwarsa Hamutal, ’yar Irmiya, wanda yake zaune a Libna. Sarki Zedekiya ya aikata abin da yake mugu a gaban Ubangiji kamar yadda Sarki Yehohiyakim ya yi. Al’amarin ya zama da muni ƙwarai a cikin Isra’ila da Yahuda, don haka Ubangiji ya husata har ya sa aka kai mutanen bautar talala.
Zedekiya kuwa ya tayar wa Sarkin Babilon.
A kan rana ta goma ga watan goma, a shekara ta tara ta mulkin Zedekiya, Sarkin Yahuda, sai Nebukadnezzar, Sarkin Babilon, ya zo yaƙi da Urushalima tare da dukan sojojinsa. Suka kewaye ta da yaƙi, suka gina katanga kewaye da ita. An kewaye birnin da yaƙi har shekara ta goma sha ɗaya ta mulkin Zedekiya.
A kan rana ta tara a watan huɗu na wannan shekara, yunwa ta tsananta ƙwarai a birnin. Mutane suka rasa abin da za su ci. Sai aka huda katangan birnin, sojojin kuwa suka gudu, suka fita daga cikin birnin da dare ta hanyar ƙofar da take tsakanin bango biyu, kusa da gonar sarki, sa’ad da Babiloniyawa suke kewaye da birnin. Sojojin suka nufi wajen Araba. Amma sojojin Babiloniyawa suka runtumi sarki Zedekiya, suka ci masa a filayen Yeriko. Dukan sojoji suka yashe shi.
Da aka kama Zedekiya, sai aka kai shi wurin Sarkin Babilon a Ribla a ƙasar Hamat, a nan ne Sarkin Babilon ya yanke masa shari’a. 10 Sarkin Babilon ya kashe ’ya’yan Zedekiya a idonsa. Ya kuma kashe dukan shugabannin Yahuda a Ribla. 11 Sa’an nan ya ƙwaƙule idanun Zedekiya, ya kuma sa masa ƙuƙumi, aka kai shi Babilon inda aka sa shi a kurkuku har ran da ya mutu.
12 A kan rana ta goma ga watan biyar a shekara ta goma sha tara ta sarautar Nebukadnezzar, Sarkin Babilon, sai Nebuzaradan shugaban matsara da kuma ɗan majalisar sarki, ya zo Urushalima. 13 Sai ya ƙone haikalin Ubangiji, da gidan sarki, da dukan gine-gine masu alfarman da suke Urushalima. 14 Sojojin Babiloniyawa da suke tare da shugaban matsara, suka rushe dukan katangan Urushalima. 15 Sa’an nan Nebuzaradan shugaban matsara ya kwashe waɗansu matalauta, da sauran mutane da aka bari a birnin, da waɗanda suka gudu zuwa wurin Sarkin Babilon, da sauran masu sana’a, ya kai su bautar talala a Babilon. 16 Amma ya bar waɗansu matalauta na gaske a ƙasar don su yi aiki a gonakin inabi, da sauran gonaki.
17 Babiloniyawa kuwa suka farfasa ginshiƙan tagulla, da dakalai, da babbar kwatarniya, waɗanda suke a haikalin Ubangiji. Suka kwashe tagulla duka suka kai Babilon. 18 Suka kwashe tukwanen ƙarfe, da manyan cokula, da hantsuka, da daruna, da tasoshin ƙona turare, da kayayyakin tagulla waɗanda ake amfani da su domin hidimar haikali. 19 Suka kuma kwashe ƙananan kwanonin sha, da farantan wuta, da daruna, da tukwane, da alkukai, da tasoshin ƙona turare, da kwanonin miƙa hadayar sha. Duk abin da yake na zinariya da azurfa, shugaban matsara ya kwashe.
20 Tagullar da sarki Solomon ya yi wa haikalin Ubangiji da ita, wato, ginshiƙai biyu, da ƙaton kwano mai suna Teku na tagulla, da bijimai goma sha biyu, waɗanda suke ɗauke da kwatarniya, da dakalai, ta fi ƙarfin a auna. 21 Tsawon kowane ginshiƙi kamu goma sha takwas ne, kewayensa kuwa kamu goma sha biyu ne, kaurinsa kuma huɗu ne. Kowannensu yana da rami a ciki. 22 A kan kowane ginshiƙi, an yi masa dajiyar tagulla, tsayinta kamu biyar. A bisa kan kowace dajiya akwai raga da siffofin rumman na tagulla kewaye da dajiyar. Ginshiƙi na biyu ma haka yake da siffofin rumman. 23 Akwai siffofin rumman tasa’in da shida da ake gani a gefen. Dukan siffofin rumman da suke a kan ragar kewaye, guda ɗari ne.
24 Shugaban matsara kuma ya ɗauki Serahiya babban firist, da Zefaniya wanda yake biye da babban firist, da mutum uku masu tsaron ƙofar, ya tafi da su. 25 Daga cikin birnin kuma ya ɗauki shugaban sojojin, da mutum bakwai ’yan majalisar sarki, da magatakardan shugaban sojojin wanda yakan tara sojojin ƙasar, da mutane sittin na ƙasar, waɗanda aka same su a birnin, ya tafi da su. 26 Nebuzaradan shugaban matsara ya tafi da waɗannan mutane wurin Sarkin Babilon a Ribla, 27 Sarkin Babilon kuwa ya kashe su a Ribla a ƙasar Hamat.
Haka aka tafi da mutanen Yahuda bautar talala, daga ƙasarta.
 
28 Wannan shi ne yawan mutanen da Nebukadnezzar ya kai su bauta.
 
A shekara ta bakwai ta sarautarsa, ya tafi da Yahudawa 3,023;
29 a shekara ta goma sha takwas ta sarautar Nebukadnezzar,
ya tafi da Yahudawa daga Urushalima 832;
30 a shekara ta ashirin da uku ta sarautarsa,
Nebuzaradan shugaban matsara ya tafi da Yahudawa 745.
 
Jimillarsu duka 4,600 ne.
An saki Yehohiyacin
(2 Sarakuna 25.27-30)
31 A shekarar da Ewil-Merodak ya zama Sarkin Babilon, sai ya nuna wa Yehohiyacin Sarkin Yahuda alheri. Ya fisshe shi daga kurkuku. Wannan ya faru ran ashirin da biyar ga watan goma sha biyu a shekara ta talatin da bakwai bayan da aka kai Yehohiyacin bauta. 32 Ewil-Merodak ya nuna wa Yehohiyacin alheri, ya ba shi matsayi na daraja fiye da waɗansu sarakunan da aka kai su bautar talala a Babilon tare da shi. 33 Yehohiyacin ya tuɓe tufafin kurkuku, ya riƙa cin abinci kullum a teburin sarki, har dukan sauran kwanakin ransa. 34 Kowace rana akan ba shi kyauta bisa ga umarnin sarkin Babilon, saboda bukatarsa. Haka aka yi masa har rasuwarsa.