5
1 Mun san cewa idan wannan gidan da muke zaune a ciki ya rushe, muna da wani ginin daga wurin Allah. Gida ne wanda ba hannuwan mutane suka gina ba, amma madawwamin gida ne a cikin sama.
2 Domin a cikin wannan jiki muna gurnani, muna jira a suturta mu da wurin zaman mu na samaniya.
3 Muna jiran wannan ne domin ta wurin suturtar da mu ba za a same mu tsirara ba.
4 Gama babu shakka yayinda muke cikin wannan alfarwa, muna gurnani, muna nawaita. Ba mu so muyi zaman hutanci. Maimakon haka, muna so a suturtar da mu, domin rai ya hadiye abu mai mutuwa.
5 Wanda kuwa yake shirya mu domin ainihin wannan abu Allah ne, wanda ya ba mu Ruhu a matsayin alkawarin abinda ke zuwa.
6 Domin wannan mu zama da gabagadi koyaushe. Mu lura da cewa yayinda muka shagala cikin jiki, muna nesa da Ubangiji.
7 Gama bisa ga bangaskiya muke tafiya, ba bisa ga ganin ido ba.
8 Don haka muna da gabagadi. Mun gwammace mu rabu da jiki domin mu zauna tare da Ubangiji.
9 Sai muka maishe shi burinmu, ko muna cikin jiki ko nesa, mu gamshe shi.
10 Domin tilas dukanmu mu hallara a gaban kursiyin shari'a na Almasihu, saboda kowa ya karbi sakamakon abubuwan da yayi cikin jiki, ko masu kyau ne ko marasa kyau.
11 Don haka, domin mun san tsoron Ubangiji, muna rinjayar mutane. Allah na ganin yadda muke a fili. Ina fatan hakan a fili take ga lamirinku.
12 Ba muna kokarin mu rinjaye ku domin ku kalle mu a matsayin amintattun mutane ba. Maimakon haka, muna ba ku dalilin yin takama da mu, domin ku sami amsar da za ku bada ga wadanda ke fahariya da kasancewarsu amma ba game da abinda ke zuciya ba.
13 Gama idan mun fita daga hankulanmu, saboda Allah ne. Kuma idan muna cikin hankalinmu, domin ku ne.
14 Domin kaunar Almasihu ta tilas ta mu, domin mun tabbatar da wannan: cewa mutum daya ya mutu domin kowa, kuma domin wannan duka sun mutu.
15 Kuma Almasihu ya mutu domin kowa, domin wadanda ke raye kada su sake rayuwa domin kansu. A maimakon haka, su yi rayuwa domin shi wanda ya mutu kuma aka tashe shi.
16 Domin wannan dalili, daga yanzu ba za mu kara shar'anta kowa bisa ga ma'aunin 'yan'adam ba, ko da yake a baya mun taba duban Almasihu a haka. Amma yanzu mun daina shar'anta kowa ta haka.
17 Saboda haka, duk wanda ke cikin Almasihu, sabon halitta ne. Tsofaffin al'amura sun shude. Duba, sun zama sababbi.
18 Dukan wadannan abubuwa daga Allah ne. Ya sulhunta mu da kansa ta wurin Almasihu, ya kuma ba mu hidimar sulhu.
19 Wato, cikin Almasihu, Allah na sulhunta duniya zuwa gare shi, ba tare da lissafin zunubansu a kansu ba. Yana damka mana sakon sulhu.
20 Don haka an zabe mu a matsayin wakilan Almasihu, kamar dai Allah na kira ga mutane ta wurin mu. Muna rokon ku, saboda Almasihu: ''ku sulhuntu ga Allah!''
21 Shi ya maida Almasihu ya zama hadaya domin zunubinmu. Shine wanda bai taba zunubi ba. Ya yi haka ne don mu zama adalchin Allah a cikin sa.