4
1 Don haka, domin muna da wannan hidima, da kuma yadda muka karbi jinkai, ba mu karaya ba.
2 Maimakon haka, sai muka rabu da dukan hanyoyin da ke na kunya, kuma na boye. Ba mu rayuwar makirci, kuma bamu yiwa maganar Allah rikon sakaci. Ta wurin gabatar da gaskiya, muna mika kanmu ga lamirin kowa a gaban Allah.
3 Amma, idan bishararmu a rufe take, tana rufe ne ga wadanda ke hallaka.
4 A al'amarinsu, allahn wannan duniya ya makantar da zukatansu marasa bada gaskiya. A sakamakon haka, ba su iya ganin hasken bisharar daukakar Almasihu ba, wanda shine surar Allah.
5 Gama ba mu yin shelar kanmu, amma Almasihu Yesu a matsayin Ubangiji, mu kuma bayinku saboda Yesu.
6 Gama Allah shine wanda ya ce, “Haske zai haskaka daga cikin duhu.” Ya haskaka cikin zukatanmu don ya bada hasken sanin daukakar Allah a gaban Yesu Almasihu.
7 Amma muna da wannan dukiya a randunan yunbu, yadda zai zama a bayyane cewa mafi girman iko na Allah ne ba namu ba.
8 Muna shan tsanani ta kowace hanya, ba a ci mu dungum ba. Mun rikice amma ba mu karaya ba, an tsananta mana amma ba a watsar da mu ba.
9 Ana tsananta mana amma ba a yashe mu ba. Aka doddoke mu amma ba mu lalace ba.
10 Mu dai a kullayaumin muna dauke da mutuwar Yesu a jikkunanmu, saboda a bayyana rayuwar Yesu a jikkunanmu kuma.
11 Mu da muke a raye kuwa a kulluyaumin ana mika mu ga mutuwa saboda Yesu, domin rayuwar Yesu ta zama a bayyane a jikunanmu na mutuntaka.
12 Saboda haka, mutuwa tana aiki a cikinmu, amma rai na aiki a cikinku.
13 Amma dai muna da wannan Ruhu na bangaskiya kammar yadda aka rubuta: “Na gaskata, saboda haka na furta.” Mu ma mun gaskata, haka kuwa muke fada.
14 Mun sani cewa wanda ya tada Ubangiji Yesu daga matattu za ya sake tada mu tare da Yesu. Mun san cewa zai gabatar da mu tare da ku a gabansa.
15 Dukan abubuwa sabili da ku suke domin, yayin da aka baza alheri ga mutane dayawa, bada godiya ta karu ga daukakar Allah.
16 Don haka ba mu karaya ba. Kodashike daga waje muna lalacewa, daga ciki ana sabunta mu kulluyaumin.
17 Domin wannan 'yar wahala ta dan lokaci tana shirya mu zuwa ga nauyin madauwamiyar daukaka wadda ta wuce gaban aunawa.
18 Domin ba muna kallon abubuwan da ake gani bane, amma abubuwan da ba a gani. Abubuwan da muke iya gani ba masu dawwama ba ne, amma abubuwan da ba a gani madawwama ne.