24
1 Bayan kwanaki biyar, sai Ananiyas babban firist, Wasu dattawa da wani masanin shari'a mai suna Tartilus, sun tafi can. Suka kai karar Bulus gaban gwamna.
2 Lokacin da Bulus ya tsaya gaban gwamna, Tartilus ya fara zarginsa yace wa gwamnan, “Saboda kai mun sami zaman lafiya; sa'annan hangen gabanka ya kawo gyara a kasarmu;
3 don haka duk abin da ka yi mun karba da godiya, ya mai girma Filikus.
4 Domin kada in wahalsheka, ina roko a yi mani nasiha don in yi magana kadan.
5 An iske mutumin nan yana barna irir iri, yana kuma zuga jama'ar Yahudawa a dukan duniya su yi tayarwa.
6 Har ma ya yi kokarin kazantar da haikali; saboda haka muka kama shi. [Mun so mu shari'anta masa bisa ga dokarmu.]
7 Amma Lisiyas jami'i ya zo ya kwace shi da karfi daga hannunmu.
8 Idan ka binciki Bulus game da wadannan al'amura, kai ma, zai tabbatar maka abin da muke zarginsa a kai.
9 Dukan Yahudawa suna zargin Bulus cewa wadannan abubuwa gaskiya ne.
10 lokacin da gwamnan ya alamta wa Bulus ya yi magana sai yace, “Yanzu na fahimci cewar da dadewa kana mulkin kasarnan, don haka da farin ciki zan yi maka bayani.
11 Zaka iya tabbatarwa cewa bai kai kwana sha biyu ba tun da nake zuwa Urushalima don yin sujada.
12 Da suka same ni a haikali, ban yi jayayya ko kawo rudami a tsakanin jama'a ba.
13 Don haka ba su da tabbas akan abinda suke zargina a kansa yau.
14 Amma na sanar da kai, bisa ga abin da suke kira darika, haka ni ma nake bautawa Allah na kakanninmu. Na yi aminci wajen kiyaye dukan abin da ke a rubuce a Attaurat da litattafan annabawa.
15 Ina sa bege ga Allah, kamar yadda za a yi tashin matattu, masu adalci da miyagu;
16 a kan haka kuma, nake kokarin zama mara abin zargi a gaban Allah da mutane ina yin haka cikin dukan al'amura.
17 Bayan wadansu shekaru na zo in kawo wasu sadakoki da baikon yardar rai.
18 Cikin kudurin yin haka, sai wasu Yahudawa daga kasar Asiya suka iske ni a cikin ka'idodin tsarkakewa a haikali, ba da taro ko ta da hargitsi ba.
19 Yakamata wadannan mutanen su zo gabarka a yau, har idan suna da wani zargi a kai na.
20 In kuwa ba haka ba bari mutanennan su fada in sun taba iske ni da wani aibu a duk lokacin da na gurfana a gaban majalisar Yahudawa;
21 sai dai ko a kan abu daya da na fada da babbar murya sa'adda na tsaya a gabansu, 'Wato batun tashin matattu wanda ake tuhumata ake neman yi mani hukunci yau.'”
22 Filikus yana da cikakken sanin tafarkin Hanyar, shi yasa ya daga shari'ar. Yace da su, “Duk sa'anda Lisiyas mai ba da umarni ya zo daga Urushalima, zan yanke hukunci.”
23 Sa'annan ya umarci jarumin ya lura da Bulus, amma ya yi sassauci, kada ya hana abokansa su ziyarce shi ko su taimake shi.
24 Bayan wadansu kwanaki, Filikus da mai dakinsa Druskila, ita Bayahudiya ce, ya kuma aika a kira Bulus ya saurare shi game da bangaskiya cikin Kristi Yesu.
25 Amma sa'adda Bulus yake bayyana zancen adalci, kamunkai, da hukunci mai zuwa, Filikus ya firgita ya ce, “Yanzu ka tafi. Amma idan na sami zarafi an jima, zan sake neman ka.”
26 A wannan lokacin, yasa zuciya Bulus zai bashi kudi, yayi ta nemansa akai-akai domin yayi magana da shi.
27 Bayan shekaru biyu, Borkiyas Festas ya zama gwamna bayan Filikus, domin neman farin jini a wurin Yahudawa, ya ci gaba da tsaron Bulus a gidan yari.