23
1 Bulus ya kura wa yan majalisa ido yace, '''Yan'uwa, na yi rayuwa tare da Allah da lamiri mai kyau har wannan ranan.''
2 Babban firist Hannaniya ya ba wandanda suke tsaye tare da shi urmarni su buge bakinsa.
3 Bulus ya ce, “Allah zai buge ka, kai munafiki. Kana zama domin ka shari'anta ni da shari'a, kuma ka umarce a buge ni, gaba da sharia?''
4 Wanda suka tsaya a gefe suka ce, ''Kada ka zage babban firis na Allah.'' Bulus yace, ''Ban sani ba, 'yan'uwa, cewa shi babban firis ne.
5 Domin a rubuce yake, Ba za ku zargi shugaban mutanenku ba.''
6 Da Bulus ya ga cewa, daya bangaren Sadukiyawa ne dayan kuma Farisawa, ya yi magana da karfi a majalisa, '''Yan'uwa, ni Bafarise ne, dan Farisawa. Don tabbacin tashin matattu ne kuna shari'anta ni.''
7 Daya fadi haka, mahawara ta fara a tsakanin Farisawa da Sadukiyawa, sai taron ya rabu kashi biyu.
8 Don Sadukiyawa suka ce babu tashin matattu, babu mala'iku, babu kuma ruhohi, amma Farisawa suka ce dukan abubuwan nan sun kasance.
9 Sai mahawara ta tashi, wadansu marubutan Farisawa suka tashi da mahawara cewa, ''Ba mu same mutumin nan da laifi ba sam. Ko mala'iku da ruhohi ne suka yi masa magana?''
10 Da jayayya ta tashi, babban hafsa ya ji tsoro kada su yayaga Bulus, sai ya umarce sojoji suje su kwato shi da karfi daga 'yan majalisa, su tafi da shi farfajiya.
11 Da dare Ubangiji ya tsaya kusa da shi yace, ''Kada ka ji tsoro, kamar yadda ka ba da shaida game da ni a Urushalima, dole zaka sake zama shaida a Roma.''
12 Da gari ya waye, wadansu Yahudawa sun yi yarjejeniya suka dauka wa kansu la'ana: suka ce ba za su ci ba ba za su sha ba sai sun kashe Bulus.
13 Mutane fiye da arba'in suka kulla wannan makirci.
14 Suka je wurin manyan firistoci da dattawa suka ce, ''Mun sa wa kanmu la'ana, ba za mu ci ba, ba za mu sha ba sai mun kashe Bulus.
15 Yanzu, bari majalisa ta ba wa babban hafsa izini a kawo shi a gaba, kamar zai yanke hukunci. Mu kam, a shirye muke mu kashe shi kafin ya iso nan.
16 Amma dan yar'uwan Bulus ya ji suna labe, sai ya tafi ya shiga farfajiyar ya fada wa Bulus.
17 Bulus ya kira daya daga cikin jarumai yace, ''Dauki saurayin nan ka kai shi wurin babban hafsa, don yana da abin da zai fada masa.''
18 Jarumin ya dauke saurayin ya kai shi wurin babban hafsa yace, ''Bulus dan sarka ne yace in kawo saurayin nan a gaban ka. Yana da abin da zai fada maka.''
19 Babban hafsa ya kai shi wani lungu, sai ya tambaye shi, “Menene kake so ka fada mani?''
20 Saurayin yace, ''Yahudawa sun yarda su roke ka ka kawo Bulus gobe a majalisa, kamar zasu kara bincike a kan al'amarin.
21 Amma kada ka yarda da su, mutane fiye da arba'in suna jiransa. Sun sa wa kansu la'anna, ba za su ci ba ba za su sha ba sai dai sun kashe shi. Yanzu a shirye suke; suna jira ka ba su izini.''
22 Sai babban hafsa yace wa saurayin ya tafi, da ya gama masa magana, ''Kar ka fada wa wani al'amuran.''
23 Sai ya kira jarumai biyu yace, ''Ku shirya sojoji dari biyu, yan dawakai saba'in, masu daukar mashi dari biyu su tafi kaisariya karfe uku na dare.''
24 Ya umarta a shirya dabbobin da Bulus zai hawo da zasu kai shi lafiya wurin Filikus gwamna.
25 Sai ya rubuta wasika a misalin haka:
26 Gaisuwa zuwa Kuludiyas Lisiyas zuwa ga mai martaba gwamna Filikus.
27 Yahudawa sun kama wannan mutumin suna shirin kashe shi, na abko masu da sojoji na kwace shi, bayan da na ji shi Barome ne.
28 Inna son sani dalilin zarginsa, sai na kai shi majalisa.
29 Na gane cewa ana zarginsa ne a kan tambayoyi game da shari'ansu, amma ba wani zargi da ya cancanci dauri ko mutuwa.
30 Da aka sanar da ni shirin makircin, sai na tura shi wurinka ba da bata lokaci ba, na umarce masu zarginsa su kawo zarginsu wurinka. Huta lafiya.”
31 Sai sojoji suka yi biyayya da umarni da aka basu: suka dauki Bulus suka kawo shi dadare a wurin Antibatris.
32 Da gari ya yawe, yan dawakai suka tafi tare da shi kuma sauran sojoji suka koma farfajiya.
33 Bayan da yandawakan suka isa Kaisiririya sun mika wasika ga gwamna, suka kuma danka Bulus a hanunsa.
34 Da gwamna ya karanta wasikar, sai ya tambaye su daga wani yanki ne Bulus ya fito; da ya ji daga yankin kilikiya ne,
35 Yace zan saurare ka sosai lokacin da masu zargin ka sun zo. Sai ya umarta a tsare shi a fadar Hiridus.