Zabura 150
Yabi Ubangiji.*
 
Yabi Allah a cikin wurinsa mai tsarki;
yabe shi a cikin sammai na ikonsa.
Yabe shi saboda ayyukansa masu iko;
yabe shi saboda mafificin girmansa.
Yabe shi da ƙarar kakaki,
yabe shi da garaya da molo,
yabe shi da ganga kuna taka rawa,
yabe shi da kayan kiɗi na tsirkiya kuna kuma busa,
yabe shi da kuge mai ƙara,
yabe shi da kuge masu ƙara sosai.
 
Bari kowane abu mai numfashi yă yabi Ubangiji.
 
Yabi Ubangiji.
* Zabura 150:1 Da Ibraniyanci Hallelu Ya; haka ma a aya 6.