Zabura 149
1 Yabi Ubangiji.
Ku rera sabuwar waƙa ga Ubangiji,
yabonsa a cikin taron tsarkaka.
2 Bari Isra’ila su yi farin ciki da Mahaliccinsu;
bari mutanen Sihiyona su yi murna da Sarkinsu.
3 Bari su yabi sunansa tare da rawa
suna kuma yin kiɗi gare shi da ganga da garaya.
4 Gama Ubangiji yana jin daɗin mutanensa;
yakan darjanta masu sauƙinkai da ceto.
5 Bari tsarkaka su yi farin ciki a wannan bangirma
su kuma rera don farin ciki a kan gadajensu.
6 Bari yabon Allah yă kasance a bakunansu
takobi mai kaifi kuma a hannuwansu,
7 don su ɗau fansa a kan al’ummai
da kuma hukunci a kan mutane,
8 don su ɗaura sarakuna da sarƙoƙi,
manyan garinsu da sarƙoƙin ƙarfe,
9 don su yi hukuncin da aka rubuta a kansu.
Wannan ne ɗaukakar dukan tsarkakansa.
Yabi Ubangiji.