Zabura 130
Waƙar haurawa. 
 
1 Daga cikin zurfafa na yi kuka gare ka, ya Ubangiji;   
2 Ya Ubangiji, ka ji muryata.  
Bari kunnuwanka su saurara  
ga kukata ta neman jinƙai.   
   
 
3 In kai, ya Ubangiji, za ka lissafta zunubai,  
Ya Ubangiji, wa zai tsaya?   
4 Amma tare da kai akwai gafartawa,  
saboda haka ake tsoronka.   
   
 
5 Zan jira Ubangiji, raina zai jira,  
kuma a cikin maganarsa na sa zuciyata.   
6 Raina na jiran Ubangiji  
fiye da yadda mai tsaro yakan jira safiya,  
fiye da yadda mai tsaro yakan jira safiya.   
   
 
7 Ya Isra’ila, sa zuciya ga Ubangiji,  
gama tare da Ubangiji akwai ƙauna marar ƙarewa  
kuma tare da shi akwai cikakkiyar fansa.   
8 Shi kansa zai fanshi Isra’ila  
daga dukan zunubansu.