Zabura 129
Waƙar haurawa.
Sun yi mini danniya ƙwarai tun ina ƙarami,
bari Isra’ila yă ce,
sun yi mini danniya ƙwarai tun ina ƙarami,
amma ba su yi nasara a kaina ba.
Manoma sun nome bayana
suka yi kunyoyinsu da tsayi.
Amma Ubangiji mai adalci ne;
ya ’yantar da ni daga igiyoyin mugaye.
 
Bari dukan waɗanda suke ƙin Sihiyona
a juye da su baya da kunya.
Bari su zama kamar ciyawa a kan rufi,
wadda takan bushe kafin tă yi girma;
da ita mai girbi ba ya iya cika hannuwansa,
balle wanda yake tarawa yă cika hannuwansa.
Kada masu wuce su ce,
“Albarkar Ubangiji ta kasance a kanku;
muna sa muku albarka a cikin sunan Ubangiji.”