31
1 “A lokacin nan, zan zama Allah na dukan kabilan Isra’ila, za su kuma zama mutanena,” in ji Ubangiji.
2 Ga abin da Ubangiji yana cewa,
“Mutanen da suka tsere wa takobi
za su sami tagomashi a hamada;
zan zo don in ba da hutu ga Isra’ila.”
3 Ubangiji ya bayyana mana a dā, yana cewa,
“Na ƙaunace ku da madawwamiyar ƙauna;
na janye ku da ƙauna marar iyaka.
4 Zan sāke gina ki
za ki kuwa sāke ginuwa, ya Budurwar Isra’ila.
Za ki kuma ɗauki ganganki
ki fita don ki yi rawa da masu farin ciki.
5 Za ki sāke dasa gonakin inabi
a kan tussan Samariya;
manoma za su yi shuka a kansu
su kuma ji daɗin amfaninsu.
6 Za a yi ranar da matsara za su tā da murya
a kan tuddan Efraim su ce,
‘Ku zo, bari mu haura Sihiyona,
zuwa wurin Ubangiji Allahnmu.’ ”
7 Ga abin da Ubangiji yana cewa,
“Ku rera don farin ciki wa Yaƙub;
ku yi sowa don al’ummai da suke nesa.
Ka sa a ji yabanku, ku kuma ce,
‘Ya Ubangiji ka ceci mutanenka,
raguwar Isra’ila.’
8 Ga shi, zan kawo su daga ƙasar arewa
in tattara su daga iyakar duniya.
A cikinsu makafi da guragu za su kasance,
mata masu ciki da matan da suke naƙuda;
jama’a mai yawan gaske za su komo.
9 Za su zo da kuka;
za su yi addu’a yayinda nake komo da su.
Zan bishe su kusa da rafuffukan ruwa
a miƙaƙƙiyar hanya inda ba za su yi tuntuɓe ba,
domin ni ne mahaifin Isra’ila,
Efraim kuma ɗan farina ne.
10 “Ku ji maganar Ubangiji, ya al’ummai;
ku yi shelarta a gaban teku masu nesa cewa,
‘Shi wanda ya watsar da Isra’ila zai tattara su
zai kuma lura da garkensa kamar makiyayi.’
11 Gama Ubangiji zai fanshi Yaƙub
zai cece su daga hannun waɗanda suka fi su ƙarfi.
12 Za su zo su yi sowa don farin ciki a ƙwanƙolin Sihiyona;
za su yi farin ciki cikin yalwar Ubangiji
hatsi, sabon ruwan inabi da mai,
’ya’yan garken tumaki da na shanu.
Za su zama kamar gonar da aka yi wa banruwa,
ba za su ƙara yin baƙin ciki ba.
13 ’Yan mata za su yi rawa su kuma yi murna,
haka ma samari da tsofaffi.
Zan mai da makokinsu farin ciki;
zan ta’azantar da su in kuma sa su yi farin ciki a maimakon baƙin ciki.
14 Zan ƙosar da firistoci da yalwa,
mutanena kuma za su cika da yalwa,”
in ji Ubangiji.
15 Ga abin da Ubangiji yana cewa,
“An ji murya daga Rama,
makoki da kuka mai zafi,
Rahila tana kuka domin ’ya’yanta
ta kuma ƙi a ta’azantar da ita
domin ’ya’yanta ba su.”
16 Ga abin da Ubangiji yana cewa,
“Hana muryarki kuka
da kuma idanunki hawaye,
gama za a sāka wa aikinki,”
in ji Ubangiji.
“Za su komo daga ƙasar abokin gāba.
17 Saboda haka akwai sa zuciya domin nan gaba,”
in ji Ubangiji.
“’Ya’yanki za su komo ƙasarsu.
18 “Tabbatacce na ji gurnanin Efraim yana cewa,
‘Ka hore ni kamar ɗan maraƙi mai ƙin ji,
na kuwa horu.
Ka mayar da ni, zan kuwa dawo,
domin kai ne Ubangiji Allahna.
19 Bayan na kauce,
sai na tuba;
bayan na gane,
sai na sunkuyar da kaina.
Na ji kunya da ƙasƙanci
domin ina ɗauke da kunyar ƙuruciyata.’
20 Efraim ba ƙaunataccen ɗana ba ne,
ɗan da nake jin daɗinsa?
Ko da yake sau da dama ina maganar gāba a kansa,
duk da haka nakan tuna da shi.
Saboda haka zuciyata tana marmarinsa;
ina da jinƙai mai girma dominsa,”
in ji Ubangiji.
21 “Ki kafa alamun hanya;
ki sa shaidun bishewa.
Ki lura da babbar hanya da kyau,
hanyar da kika bi.
Ki komo, ya Budurwar Isra’ila,
ki komo zuwa garuruwanki.
22 Har yaushe za ki yi ta yawo,
Ya ’ya marar aminci?
Ubangiji zai ƙirƙiro sabon abu a duniya
mace za tă kewaye namiji.”
23 Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki, Allah na Isra’ila yana cewa, “Sa’ad da na komo da su daga bauta mutane a ƙasar Yahuda da cikin garuruwanta za su sāke yi amfani da waɗannan kalmomi. ‘Ubangiji ya albarkace ka, ya mazauni mai adalci, ya tsarkakan dutse.’
24 Mutane za su zauna tare a Yahuda da dukan garuruwansa, manoma da waɗanda suke yawo da garkunansu.
25 Zan wartsake waɗanda suka gaji in kuma ƙosar da waɗanda ransu ya yi yaushi.”
26 A kan wannan na farka na duba kewaye. Barcina ya yi mini daɗi.
27 “Kwanaki suna zuwa,” in ji Ubangiji, “sa’ad da zan kafa gidan Isra’ila da gidan Yahuda da ’ya’yan mutane da na dabbobi.
28 Kamar yadda na lura da su don su tumɓuke su kuma rusar, su lalatar, su hallaka su kuma kawo masifa, haka zan lura da su don su gina su kuma dasa,” in ji Ubangiji.
29 “A waɗannan kwanaki mutane ba za su ƙara ce,
“ ‘Ubanni suka ci ’ya’yan inabi masu tsami,
haƙoran ’ya’ya suka mutu ba.’
30 A maimako, kowa zai mutu saboda zunubinsa; duk wanda ya ci ’ya’yan inabi masu tsami, haƙoransa ne za su mutu.
31 “Lokaci yana zuwa,” in ji Ubangiji,
“sa’ad da zan yi sabon alkawari
da gidan Isra’ila
da kuma gidan Yahuda.
32 Ba zai zama kamar alkawarin
da na yi da kakanni kakanninsu ba
sa’ad da na kama su da hannu
na bishe su daga Masar,
domin sun take alkawarina,
ko da yake na zama miji a gare su,”
in ji Ubangiji.
33 “Ga alkawarin da zan yi da gidan Isra’ila
bayan wannan lokaci,” in ji Ubangiji.
“Zan sa dokata a tunaninsu
in kuma rubuta ta a zukatansu.
Zan zama Allahnsu,
za su kuma zama mutanena.
34 Mutum ba zai ƙara koya wa maƙwabci ba,
ko ya koya wa ɗan’uwansa cewa, ‘Ka san Ubangiji,’
domin duk za su san ni,
daga ƙaraminsu har zuwa babba,”
in ji Ubangiji.
“Gama zan gafarta muguntarsu
ba zan kuwa ƙara tuna da zunubansu ba.”
35 Ga abin da Ubangiji yana cewa,
shi da ya kafa rana
don tă yi haske a yini
shi da ya sa wata da taurari
su yi haske da dare,
shi da yake dama teku
don raƙuman ruwansa su yi ruri
Ubangiji Maɗaukaki ne sunansa.
36 “In dai wannan kafaffiyar ƙa’ida ta daina aiki a gabana,”
in ji Ubangiji,
“to, sai zuriyar Isra’ila ta daina
zama al’umma a gabana.”
37 Ga abin da Ubangiji yana cewa,
“In a iya auna sammai
a kuma bincike tushen duniya a ƙarƙas
to, sai in ƙi dukan zuriyar Isra’ila ke nan
saboda dukan abin da suka yi,”
in ji Ubangiji.
38 “Kwanaki suna zuwa,” in ji Ubangiji, “sa’ad da za a sāke gina wannan birni domina daga Hasumiyar Hananel zuwa Ƙofar Kusurwa.
39 Ma’auni zai miƙe daga can ya nausa kai tsaye zuwa tudun Gareb sa’an nan ya juya zuwa Gowa.
40 Dukan kwarin da ake zubar da toka da kuma gawawwaki, da dukan lambatun da suke can har zuwa Kwarin Kidron a gabas zuwa kusurwar Ƙofar Doki, za su zama mai tsarki ga Ubangiji. Ba za a ƙara tumɓuke birnin ko a rushe shi ba.”