30
Maidowa da Isra’ila
Ga maganar da ta zo wa Irmiya daga Ubangiji. “Ga abin da Ubangiji, Allah na Isra’ila, yana cewa, ‘Ka rubuta a cikin littafi dukan maganganun da na yi maka. Kwanaki suna zuwa,’ in ji Ubangiji, ‘sa’ad da zan komo da mutanena Isra’ila da Yahuda daga bauta in kuma maido da su ga ƙasar da na ba wa kakanninsu mallaka,’ in ji Ubangiji.”
Ga kalmomin Ubangiji da ya yi game da Isra’ila da Yahuda, “Ga abin da Ubangiji yana cewa,
“ ‘Ana jin kukan tsoro,
razana, ba salama ba.
Ku tambaya ku ji.
Namiji zai iya haifi ’ya’ya?
To, me ya sa kuke ganin kowane mai ƙarfi
da hannuwansa a kwankwaso kamar mace mai naƙuda,
kowace fuska ta koma fari?
Kaito, gama wannan rana za tă zama mai girma!
Babu kamar ta.
Zai zama lokacin wahala wa Yaƙub,
amma za a cece shi daga cikinta.
 
“ ‘A wannan rana,’ in ji Ubangiji Maɗaukaki,
‘Zan karya karkiya daga wuyansu
zan kuma cire musu kangi;
baƙi ba za su ƙara bautar da su ba.
A maimakon haka, za su bauta wa Ubangiji Allahnsu
Dawuda sarkinsu kuwa,
wanda na tayar musu.
 
10 “ ‘Saboda haka kada ka ji tsoro, ya Yaƙub bawana;
kada ka karai, ya Isra’ila,’
in ji Ubangiji.
‘Tabbatacce zan cece ka daga wuri mai nesa,
zuriyarka daga ƙasar zaman bautansu.
Yaƙub zai sami salama da zaman lafiya,
kuma ba wanda zai sa ya ji tsoro.
11 Ina tare da kai zan kuma cece ka,’
in ji Ubangiji.
‘Ko da yake na hallakar da dukan al’umma gaba ɗaya
a inda na warwatsa ku,
ba zan hallaka ku gaba ɗaya ba.
Zan hore ku amma da adalci kaɗai;
ba zan ƙyale ku ku tafi gaba ɗaya ba hukunci ba.’
12 “Ga abin da Ubangiji yana cewa,
“ ‘Mikinku marar warkewa ne,
raunin da kuka ji ya sha ƙarfin warkarwa.
13 Babu wanda zai yi roƙo saboda damuwarku,
ba magani domin mikinku
babu warkarwa dominku.
14 Dukan abokanku sun manta da ku;
ba su ƙara kulawa da ku.
Na buge ku kamar yadda abokin gāba zai yi
na kuma hukunta ku yadda mai mugunta zai yi,
domin laifinku da girma yake
zunubanku kuma da yawa suke.
15 Me ya sa kuke kuka a kan mikinku,
wahalarku da ba ta da magani?
Domin laifinku da girma yake da kuma zunubanku masu yawa
na yi muku waɗannan abubuwa.
 
16 “ ‘Amma duk wanda ya cinye ku za a cinye shi;
dukan abokan gābanku za su tafi zaman bauta.
Waɗanda suka washe ku su ma za a washe su;
dukan waɗanda suka mai da ku ganima su ma zan mai da su ganima.
17 Amma zan mayar muku da lafiya
in kuma warkar da mikinku,’ in ji Ubangiji,
‘domin ana ce da ku yasassu,
Sihiyona wadda ba wanda ya kula da ita.’
18 “Ga abin da Ubangiji yana cewa,
“ ‘Zan mayar da wadatar tentin Yaƙub
in kuma ji tausayin wuraren zamansa;
za a sāke gina birnin a kufansa,
fadar kuwa za tă tsaya a wurin da ya dace da ita.
19 Daga gare su waƙoƙi za su fito na godiya
da kuma sowa ta farin ciki.
Zan riɓaɓɓanya su,
ba za su kuwa ragu ba;
zan kawo musu ɗaukaka,
ba kuwa za a ƙasƙanta su ba.
20 ’Ya’yansu za su kasance kamar a kwanakin dā
jama’arsu kuma za su kahu a gabana;
zan hukunta duk wanda ya zalunce su.
21 Shugabansu zai zama ɗaya daga cikinsu;
mai mulkinsu zai taso daga cikinsu.
Zan kawo shi kusa zai kuma zo kusa da ni,
gama wane ne zai miƙa kansa
don yă yi kusa da ni?’
In ji Ubangiji.
22 ‘Saboda haka za ku zama mutanena,
ni kuwa in zama Allahnku.’ ”
 
23 Ga shi, hadarin Ubangiji
zai fasu cikin hasala,
iskar guguwa mai hurawa
a kan kawunan mugaye.
24 Fushi mai zafi na Ubangiji ba zai kawu ba
sai ya cika
manufofin zuciyarsa gaba ɗaya.
A kwanaki masu zuwa
za ku gane wannan.