18
A gidan mai ginin tukwane
1 Ga maganar da ta zo wa Irmiya daga wurin Ubangiji.
2 “Ka gangara zuwa gidan mai ginin tukwane, a can zan ba ka saƙona.”
3 Sai na gangara zuwa gidan mai ginin tukwane, na gan shi yana aiki a na’urar ginin tukwanen.
4 Amma tukunyar da yake ginawa ta lalace a hannuwansa, sai mai ginin tukwanen ya sāke gina wata tukunya dabam, yana gyara ta yadda ya ga dama.
5 Sai maganar Ubangiji ta zo mini cewa,
6 “Ya gidan Isra’ila, ashe, ba zan yi da ku yadda mai ginin tukwanen nan yake yi ba?” In ji Ubangiji. “Kamar yumɓu a hannun mai ginin tukwane, haka kuke a hannuna, ya gidan Isra’ila.
7 A duk lokacin da na yi shela cewa za a tumɓuke, a kakkarya a kuma hallaka wata al’umma ko mulki,
8 in wannan al’ummar da na yi wa gargaɗi ta tuba daga muguntarta, sai in janye in kuma fasa kawo mata masifar da na yi niyya aukar mata.
9 In kuma wani lokaci na yi shela cewa za a gina wata al’umma ko mulki a kuma kafa ta,
10 in ta yi mugunta a gabana ba tă kuwa yi mini biyayya ba, sai in janye alherin da na yi niyya in yi mata.
11 “Yanzu fa, sai ka faɗa wa mutanen Yahuda da waɗanda suke zaune a Urushalima, ‘Ga abin da Ubangiji yana cewa ga shi! Ina shirya muku masifa ina ƙirƙiro dabara a kanku. Saboda haka ku juya daga mugayen hanyoyinku, kowannenku, ku canja hanyoyinku da kuma ayyukanku.’
12 Amma za su amsa su ce, ‘Ba amfani. Za mu ci gaba da shirye-shiryenmu; kowannenmu zai bi taurin muguwar zuciyarsa.’ ”
13 Saboda haka ga abin da Ubangiji yana cewa,
“Ku tattambaya a cikin al’ummai.
Wa ya taɓa jin irin wannan abu?
Budurwa Isra’ila ta yi mugun abu
mafi banƙyama.
14 Dusar ƙanƙarar Lebanon
ta taɓa rabuwa da kan duwatsun Lebanon?
Ruwan mai sanyinsa daga rafuffukansa masu nesa
sun taɓa daina gudu?
15 Duk da haka mutanena sun manta da ni;
sun ƙone turare wa gumaka marasa amfani,
waɗanda suka sa su tuntuɓe a al’amuransu
a hanyoyin dā.
Sun sa suka yi tafiya a ɓarayin hanyoyi
a hanyoyin da ba a gina ba.
16 Ƙasarsu za tă zama kufai,
abin reni har abada;
dukan waɗanda suka wuce za su yi mamaki
su kaɗa kai.
17 Kamar iska daga gabas
zan warwatsa su a gaban abokan gābansu;
zan juya musu bayana, ba zan nuna musu fuskata ba
a ranar masifarsu.”
18 Suka ce, “Zo mu shirya wa Irmiya maƙarƙashiya; gama koyarwar doka da firist ya yi ba za tă ɓace ba, haka ma shawara daga mai hikima da kuma magana daga annabawa. Saboda haka ku zo, mu fāɗa masa da harsunanmu kada mu saurari wani abin da zai faɗa.”
Addu’ar Irmiya
19 Ka saurare ni, ya Ubangiji
ka ji abin da masu zargina suke cewa!
20 Ya kamata a sāka wa alheri da mugunta?
Duk da haka sun haƙa mini rami.
Ka tuna cewa na tsaya a gabanka
na kuma yi magana a madadinsu
don ka janye fushinka daga gare su.
21 Saboda haka ka kawo wa ’ya’yansu yunwa;
ka miƙa su ga ikon takobi.
Bari matansu su zama marasa ’ya’ya da gwauraye;
bari a kashe mazansu,
a kuma kashe samarinsu da takobi a yaƙi.
22 Bari a ji kuka daga gidajensu
sa’ad da ka kawo masu hari a kansu farat ɗaya,
gama sun haƙa rami don su kama ni
suka kuma kafa tarko wa ƙafafuna.
23 Amma Ya Ubangiji,
ka san duk maƙarƙashiyarsu, na neman su kashe ni.
Kada ka gafarta musu laifofinsu
ko ka shafe zunubansu daga gabanka.
Bari a tumɓuke su a gabanka;
ka yi da su sa’ad da kake fushi.