17
“An rubuta zunubin Yahuda da alƙalamin ƙarfe,
an rubuta da tsinin dutse,
a kan allunan zukatansu
da kuma a kan ƙahonin bagadansu.
Har ’ya’yansu ma sun tuna
bagadansu da ginshiƙan Asheransu
kusa da itatuwa masu duhuwa
da kuma a kan tuddai masu tsayi.
Dutsena a ƙasar
da* dukiyarku na ƙasar da dukan arzikinku
za a ba da su ganima,
tare da masujadanku na kan tuddai,
saboda zunubi ko’ina a ƙasarku.
Saboda laifinku za ku rasa
gādon da na ba ku.
Zan bautar da ku ga abokan gābanku
a ƙasar da ba ku sani ba,
domin kun husata ni,
zai kuwa ci har abada.”
Ga abin da Ubangiji yana cewa,
“La’ananne ne mutumin da yake dogara ga mutum,
wanda ya dogara ga jiki don ƙarfi
wanda kuma zuciyarsa ta juya wa Ubangiji baya.
Zai zama kamar ɗan kurmi a ƙasar da take kango;
ba za su ga arziki sa’ad da ya zo ba.
Za su zauna a busassun wuraren hamada,
a cikin ƙasar gishiri inda ba kowa.
 
“Amma mai albarka ne mutumin da yake dogara ga Ubangiji,
wanda ƙarfin halinsa yana daga Ubangiji.
Za su zama kamar itacen da aka dasa kusa da ruwa
wanda ya miƙa saiwoyinsa zuwa cikin rafi.
Ba ya jin tsoro sa’ad da zafi ya zo;
ganyayensa kullum kore suke.
Ba shi da damuwa a shekarar fări
ba ya taɓa fasa ba da ’ya’ya.”
 
Zuciya ta fi kome ruɗu
ta fi ƙarfin warkewa.
Wa zai iya gane ta?
 
10 “Ni Ubangiji nakan bincike zuciya
in gwada tunani,
don in sāka wa kowane mutum bisa ga halinsa,
bisa ga ayyukansa.”
 
11 Kamar makwarwar da ta kwanta a kan ƙwan da ba ita ta zuba ba
haka yake da mutumin da ya sami arziki a hanyar da ba daidai ba.
A tsakiyar rayuwarsa za su rabu da shi,
a ƙarshe kuma zai zama wawa.
 
12 Kursiyi mai daraja, da aka ɗaukaka tun daga farko,
shi ne wuri mai tsarkinmu.
13 Ya Ubangiji, sa zuciyar Isra’ila,
duk waɗanda suka rabu da kai za su sha kunya.
Waɗanda suka juya maka baya za a rubuta su a ƙura
domin sun yashe Ubangiji,
maɓulɓular ruwan rai.
 
14 Ka warkar da ni, ya Ubangiji, zan kuwa warke;
ka cece ni zan kuwa cetu,
gama kai ne nake yabo.
15 Sun riƙa ce mini, “Ina maganar Ubangiji take?
Bari tă cika yanzu!”
16 Ban gudu zaman mai yin maka kiwo ba;
ka sani ban marmarin ranan nan ta masifa ba.
Abin da ya fito daga leɓunana kuwa, a bayyane suke gare ka.
17 Kada ka zama mini abin razana;
kai ne mafakata a ranar masifa.
18 Bari masu tsananta mini su sha kunya,
amma ka kiyaye ni daga shan kunya;
bari su tsorata,
amma ka kiyaye ni da razana.
Ka kawo musu ranar masifa;
ka hallaka su da hallaka riɓi biyu.
Kiyaye Asabbaci da tsarki
19 Ga abin da Ubangiji ya ce mini, “Ka je ka tsaya a ƙofar mutane, inda sarakunan Yahuda sukan shiga su fita; ka tsaya kuma a dukan sauran ƙofofin Urushalima. 20 Ka ce musu, ‘Ku ji maganar Ubangiji, ku sarakunan Yahuda, da dukan mutanen Yahuda da dukan mazaunan Urushalima waɗanda suke bi ta waɗannan ƙofofi. 21 Ga abin da Ubangiji yana cewa, ku yi hankali kada ku ɗauki kaya a ranar Asabbaci ko ku shigar da shi ta ƙofofin Urushalima. 22 Kada ku fitar da kayan gidajenku ko ku yi wani aiki a ranar Asabbaci mai tsarki, yadda na umarci kakanni-kakanninku. 23 Duk da haka ba su saurara ba, ba su kuwa mai da hankali ba; suka taurare ba su kuwa saurara ko su karɓi horo ba. 24 Amma in kuka yi hankali kuka yi mini biyayya, in ji Ubangiji, ba ku kuwa shigar da kaya ta ƙofofi a ranar Asabbaci ba, amma kuka kiyaye ranar Asabbaci da tsarki ba tare da yin wani aiki a cikinta ba, 25 sa’an nan sarakuna da suke zama a kursiyin Dawuda za su shiga ta ƙofofin wannan birni tare da fadawansu. Su da fadawansu za su shiga a kan kekunan yaƙi da kuma a kan dawakai, mutanen Yahuda suna musu rakiya tare da waɗanda suke zaune a Urushalima, wannan birni kuwa za tă kasance da mazauna har abada. 26 Mutane za su zo daga garuruwan Yahuda da ƙauyukan kewaye da Urushalima, daga iyakar Benyamin da gindin tuddan yamma, daga ƙasar tudu da kuma Negeb, suna kawo hadayun ƙonawa da hadayun gari, sadakokin turare da na godiya zuwa gidan Ubangiji. 27 Amma in ba ku yi mini biyayya ba, ba ku kiyaye ranar Asabbaci da tsarki ba, kuka ɗauki wani kaya yayinda kuke shiga ƙofofin Urushalima a ranar Asabbaci, to, sai in cinna wa ƙofofin Urushalima wutar da ba a iya kashewa, tă cinye kagaranta.’ ”
* 17:3 Ko kuwa tuddai 3 da duwatsun ƙasar. Naku