25
Yabo ga Ubangiji
Ya Ubangiji, kai ne Allahna; zan ɗaukaka ka in kuma yabi sunanka,
gama cikin cikakken aminci ka yi abubuwa masu banmamaki,
abubuwan da aka shirya tun da.
Ka mai da birnin tsibin tarkace,
ka lalatar da gari mai katanga,
birnin baƙi mai ƙarfi, ta ɓace; ba za a ƙara gina ta ba.
Saboda haka mutane masu ƙarfi za su girmama ka;
biranen mugayen al’ummai za su ji tsoronka.
Kai ka zama mafakar matalauta, mafaka don mabukata cikin damuwa,
wurin ɓuya daga hadari, inuwa kuma daga zafin rana.
Gama numfashin mugaye yana kamar da hadari mai bugun bango
kuma kamar zafin hamada.
Ka kwantar da hayaniyar baƙi;
kamar yadda inuwar girgije kan rage zafin rana, haka ake kwantar da waƙar mugaye.
 
A kan wannan dutse Ubangiji Maɗaukaki zai shirya bikin abinci mai kyau don dukan mutane,
liyafar ajiyayyen ruwan inabi da nama mafi kyau da ruwan inabi mafi kyau.
A wannan dutse zai kawar da
baƙin cikin da ya lulluɓe dukan mutane,
ƙyallen da ya rufe dukan al’ummai;
zai haɗiye mutuwa har abada.
Ubangiji Mai Iko Duka zai share hawaye
daga dukan fuskoki;
zai kawar da kunyar mutanensa
daga dukan duniya.
Ubangiji ne ya faɗa.
A wannan rana za su ce,
“Tabbatacce wannan shi ne Allah;
mun dogara a gare shi, ya kuma cece mu.
Wannan shi ne Ubangiji, mun dogara a gare shi;
bari mu yi murna mu kuma yi farin ciki a cikin cetonsa.”
 
10 Hannun Ubangiji zai zauna a kan wannan dutse;
amma za a tattake Mowab a ƙarƙashinsa
kamar yadda ake tattaka kara a cikin taki.
11 Za su buɗe hannuwansa a cikinsa,
yadda mai iyo kan buɗe hannuwansa don yă yi iyo.
Allah ya ƙasƙantar da girmankansu
duk da wayon* hannuwansu.
12 Zai rurrushe manyan katangar kagaru
ya kuma ƙasƙantar da su;
zai rushe su har ƙasa,
su zama ƙura.
* 25:11 Ma’anar kalmar Ibraniyancin nan babu tabbas.