24
Yin kaca-kaca da duniyar da Ubangiji zai yi
Duba, Ubangiji zai wofinta duniya
ya kuma yi kaca-kaca da ita;
zai ɓata fuskarta
ya watsar da mazaunanta,
zai zama abu ɗaya
ga firist kamar yadda yake ga mutane,
ga maigida kamar yadda yake ga bawa,
ga uwargijiya kamar yadda yake ga baiwa,
ga mai sayarwa kamar yadda yake ga mai saya,
ga mai karɓan rance kamar yadda yake ga mai ba da rance,
ga mai karɓan bashi kamar yadda yake ga mai ba da bashi.
Za a wofinta duniya ƙaƙaf
a kuma washe ta sarai.
Ubangiji ne ya faɗa haka.
 
Duniya ta bushe ta kuma yanƙwane,
duniya tana shan azaba ta kuma raunana,
masu daraja na duniya suna shan azaba.
Duniya ta ƙazantu ta wurin mutanenta
sun ƙi yin biyayya da dokoki,
sun keta farillai
suka kuma karya madawwamin alkawari.
Saboda haka la’ana za tă auko wa duniya;
dole mutanenta su ɗauki hakkin laifinsu.
Saboda haka aka ƙone mazaunan duniya,
kuma kaɗan ne kurum suka rage.
Sabon ruwan inabi ya bushe kuringar inabi kuma sun yanƙwane;
dukan masu farin ciki suna nishi.
Kaɗe-kaɗen garayu sun yi shiru,
surutun masu murna ya daina,
garayan farin ciki ya yi shiru.
Babu sauran shan ruwan inabi suna rera waƙa;
barasa ya zama da ɗaci ga masu shanta.
10 Birnin da aka birkice ta zama kango;
an kulle ƙofar shiga kowane gida.
11 A tituna suna kukan neman ruwan inabi;
dukan farin ciki ya dawo baƙin ciki,
an hana dukan kaɗe-kaɗe a duniya.
12 An bar birnin kango,
aka yi kaca-kaca da ƙofofinta.
13 Haka zai zama a duniya
da kuma a cikin al’ummai,
kamar sa’ad da akan karkaɗe itacen zaitun,
ko kuma kamar sa’ad da ake barin kala bayan an girbe inabi.
 
14 Sun daga muryoyinsu, sun yi sowa ta farin ciki;
daga yamma sun furta darajar Ubangiji.
15 Saboda haka a gabas sun ɗaukaka Ubangiji,
a ɗaukaka sunan Ubangiji, Allah na Isra’ila,
a cikin tsibiran teku.
16 Daga iyakokin duniya mun ji waƙoƙi,
“Ɗaukaka ga Mai Adalcin nan.”
 
Amma na ce, “Na lalace, na lalace!
Kaitona!
Munafukai sun ci amana!
Da munafunci munafukai sun ci amana!”
17 Razana da rami da tarko suna jiranku,
Ya mutanen duniya.
18 Duk wanda ya yi ƙoƙarin tserewa daga ƙarar razana
zai fāɗa cikin rami;
wanda kuma ya tsere daga rami
za a kama shi a tarko.
 
An buɗe ƙofofin ambaliyar ruwan sama,
harsashen ginin duniya suna rawa.
19 An tsage duniya,
duniya ta farfashe ta wage,
an girgiza duniya ƙwarai.
20 Duniya tana tangaɗi kamar mashayi,
tana lilo kamar rumfa a cikin iska;
laifin tayarwarta ya yi nauyi sosai
har ta fāɗi ba kuwa za tă ƙara tashi ba.
 
21 A wannan rana Ubangiji zai hukunta
ikokin da suke cikin sama
da kuma sarakunan da suke a duniya.
22 Za a tattara su tare
kamar ɗaurarru a kurkuku;
za a rufe su a kurkuku
a kuma hukunta su* bayan kwanaki masu yawa.
23 Sa’an nan wata zai ruɗe, rana ta ji kunya;
gama Ubangiji Maɗaukaki zai yi mulki
a kan Dutsen Sihiyona da kuma a cikin Urushalima,
da kuma a gaban dattawanta, da ɗaukaka.
* 24:22 Ko kuwa a sāke su