7
a duka sa’ad da zan warkar da Isra’ila,
zunuban Efraim za su tonu
za a kuma bayyana laifofin Samariya.
Suna ruɗu,
ɓarayi sukan fasa su shiga gidaje,
’yan fashi sukan yi fashi a tituna;
amma ba su gane
cewa na tuna da dukan ayyukan muguntarsu ba.
Zunubansu sun kewaye su;
kullum suna a gabana.
 
“Suna faranta wa sarki zuciya da muguntarsu,
shugabanni kuma da ƙarairayinsu.
Dukansu mazinata ne
suna ƙuna kamar matoya
wadda mai gashin burodi ba ya bukata yă tura mata wuta
daga cuɗe kullu har kumburinsa.
A ranar bikin sarkinmu
shugabanni sukan bugu da ruwan inabi,
yă yi cuɗanya da masu ba’a.
Zukatansu suna kamar matoya;
sukan kusace shi da wayo.
Muguwar aniyarsu takan yi ta ci dukan dare;
da safe sai ta ƙuna kamar harshen wuta.
Dukansu suna da zafi kamar matoya;
suna kashe masu mulkinsu.
Dukan sarakunansu sukan fāɗi,
kuma babu waninsu da yake kira gare ni.
 
“Efraim yana cuɗanya da al’ummai;
Efraim waina ne mai fāɗi da ba a juye ba.
Baƙi sun tsotse ƙarfinsa,
amma bai gane ba.
Gashi kansa ya cika da furfura,
amma bai lura ba.
10 Girmankan Isra’ila ya ba da shaida a kansa,
amma duk da haka
bai dawo ga Ubangiji Allahnsa
ko yă neme shi ba.
 
11 “Efraim yana kama da kurciya,
marar wayo, marar hankali,
yanzu yana kira ga Masar,
yanzu yana juyewa ga Assuriya.
12 Sa’ad da suka tafi, zan jefa ragata a kansu;
zai janye su ƙasa kamar tsuntsayen sararin sama.
Sa’ad da na ji suna tafiya tare,
zan kama su.
13 Kaitonsu,
domin sun kauce daga gare ni!
Hallaka za tă aukar musu,
domin sun tayar mini!
Na ƙudura in cece su
amma suna faɗar ƙarya a kaina.
14 Ba sa yin mini kuka da zuciyarsu
amma suna ihu a kan gadajensu.
Sukan taru wurin ɗaya don hatsi da ruwan inabi
amma su juya mini baya.
15 Na horar da su na kuma ƙarfafa su,
amma sun ƙulla mini maƙarƙashiya.
16 Ba sa juya ga Mafi Ɗaukaka;
suna kama da tanƙwararren baka.
Za a kashe shugabanninsu da takobi
saboda banzan maganganunsu.
Saboda wannan za a wulaƙanta su
a ƙasar Masar.