12
Efraim yana kiwo a kan iska;
yana fafarar iskar gabas dukan yini
yana riɓaɓɓanya ƙarairayi da rikici.
Ya yi yarjejjeniya da Assuriya
ya kuma aika wa Masar man zaitun.
Ubangiji yana da ƙarar da zai kawo a kan Yahuda;
zai hukunta Yaƙub bisa ga hanyoyinsa
zai sāka masa bisa ga ayyukansa.
A cikin mahaifa ya cafke ɗiɗɗigen ɗan’uwansa;
a matsayin mutum ya yi kokawa da Allah.
Ya yi kokawa da mala’ika ya kuma rinjaye shi;
ya yi kuka ya kuma yi roƙo don tagomashi.
Ya same shi a Betel
ya kuma yi magana da shi a can,
Ubangiji Allah Maɗaukaki,
Ubangiji ne sunansa sananne!
Amma dole ku koma ga Allahnku;
ku ci gaba da ƙauna da yin gaskiya,
ku kuma saurari Allahnku kullum.
 
Ɗan kasuwa yana amfani da mudu marar gaskiya;
yana jin daɗin cuta.
Efraim yana fariya yana cewa,
“Ni mai arziki ne ƙwarai; na azurta.
Da dukan wadatata ba za a sami
wani laifi ko zunubi a gare ni ba.”
 
“Ni ne Ubangiji Allahnku,
wanda ya fitar da ku daga* Masar;
zan sa ku sāke zauna a tentuna,
kamar a kwanakin ƙayyadaddun bukukkuwanku.
10 Na yi magana da annabawa,
na ba su wahayi da yawa
na kuma ba da misalai ta wurinsu.”
 
11 Gileyad mugu ne?
Mutanensa mutanen banza ne!
Suna miƙa bijimai a Gilgal?
Bagadansu za su zama tsibin duwatsu.
A gonar da aka nome.
12 Yaƙub ya gudu zuwa ƙasar Aram;
Isra’ila ya yi bauta don yă sami mata,
domin kuma yă biya, sai da ya yi kiwon tumaki.
13 Ubangiji ya yi amfani da annabi don yă fitar da Isra’ila daga Masar
ta wurin annabi ya lura da shi.
14 Amma Efraim ya yi muguwar tsokana da ta sa ya yi fushi;
shugabansa zai ɗora musu hakkin jini a kansa
kuma zai sāka masa saboda wulaƙancinsa.
* 12:9 Ko kuwa Allah / tun kuna cikin 12:12 Wato, Arewa maso yamma Mesofotamiya