11
Ƙaunar Allah domin Isra’ila 
 
1 “Sa’ad da Isra’ila yake yaro, na ƙaunace shi,  
daga Masar kuma na kira ɗana.   
2 Amma yawan kiran da na yi wa Isra’ila  
haka nesa da ni da suke ta yi.  
Suka miƙa hadaya ga Ba’al  
suka kuma ƙona turare ga siffofi.   
3 Ni ne na koya wa Efraim tafiya  
ina kama su da hannu;  
amma ba su gane  
cewa ni ne na warkar da su ba.   
4 Na bishe su da linzamin alheri da tausayi,  
da ragamar ƙauna;  
Na cire karkiya daga wuyansu  
na kuma rusuna na ciyar da su.   
   
 
5 “Ba za su koma Masar ba  
Assuriya kuma ba za tă yi mulki a bisansu ba  
saboda sun ƙi su tuba ba?   
6 Takuba za su yi ta wulgawa a biranensu,  
za su hallaka sandunan ƙarafan ƙofofinsu  
su kuma kawo ƙarshen ƙulle-ƙullensu.   
7 Mutanena sun ƙudura su juye daga gare ni.  
Ko da ma suka yi kira ga Mafi Ɗaukaka,  
ta ko ƙaƙa ba zai girmama su ba.   
   
 
8 “Yaya zan ba da kai, Efraim?  
Yaya zan miƙa ka, Isra’ila?  
Yaya zan yi da kai kamar Adma?  
Yaya zan yi da kai kamar Zeboyim?  
Zuciyata ta canja a cikina;  
dukan tausayina ya huru.   
9 Ba zan zartar da fushina mai zafi ba,  
ba kuwa zan juya in ragargaza Efraim ba.  
Gama ni Allah ne, ba mutum ba,  
Mai Tsarki a cikinku.  
Ba zan zo cikin fushi ba.   
10 Za su bi Ubangiji;  
zai yi ruri kamar zaki.  
Sa’ad da ya yi ruri,  
’ya’yansa za su zo da rawan jiki daga yamma.   
11 Za su zo da rawan jiki  
kamar tsuntsaye daga Masar,  
kamar kurciyoyi daga Assuriya.  
Zan zaunar da su a cikin gidajensu,”  
in ji Ubangiji.   
Zunubin Isra’ila 
 
12 Mutanen Efraim sun kewaye ni da ƙarairayi,  
gidan Isra’ila da ruɗu.  
Mutanen Yahuda kuma suna yi wa Allah ƙin ji,  
har ma a kan Mai Tsarkin nan mai aminci.