27
Makoki domin Taya
1 Maganar Ubangiji ta zo mini cewa,
2 “Ɗan mutum, ka yi makoki domin Taya.
3 Ka ce wa Taya, wadda take zaune a hanyar shiga zuwa teku, kasuwar masu yawa mutane a bakin teku, ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa,
“ ‘Kin ce, ya Taya,
“Ni kyakkyawa ce cikakkiya.”
4 Manyan tekuna ne wurin zamanki;
maginanki sun sa kyanki ya zama cikakke.
5 Sun yi dukan katakanki
daga itatuwan fir daga Senir;
sun kwaso itatuwan al’ul daga Lebanon
don su yi miki jigon jirgin ruwa.
6 Da oak daga Bashan
suka yi sandunan tuƙan jirgin ruwa
da itatuwan kasharina daga bakin tekun Saifurus
suka yi daɓe jirgin ruwanki, suka kuma manne masa hauren giwa.
7 Lilin mai kyau mai ado daga Masar ne filafilan jirgin ruwanki
suka kuma zama tutarki;
an yi tutarki da shuɗi da shunayya
daga bakin tekun Elisha.
8 Mutanen Sidon da Arfad su ne matuƙan jirgin ruwanki;
gwanayenki, ya Taya, suna ciki a matsayi matuƙan jiragen ruwa.
9 Masu hikima na Gebal suna ciki
a matsayin masu tattoshe mahaɗan katakon jirginki.
Dukan jiragen ruwa da matuƙansu
sukan zo wurinki don kasuwanci.
10 “ ‘Mutanen Farisa, Lidiya da Fut
su ne suka zama sojoji a cikin mayaƙanki.
Sun rataye garkuwoyinsu da hulunan kwano a katangarki,
suna kawo miki daraja.
11 Mutanen Arfad da Helek
sun yi tsaron katangar a kowace gefe;
mutanen Gammad
su ne a hasumiyoyinki.
Sun rataye garkuwoyinsu kewaye da katangarki;
sun sa kyanki ya zama cikakke.
12 “ ‘Tarshish ta yi ciniki da ke saboda yawan wadatar kayayyakinki; sun sayi kayan cinikinki da azurfa, ƙarfe, kuza da dalma.
13 “ ‘Girka, Tubal da Meshek sun yi kasuwanci da ke; sun sayi kayanki suka biya da bayi da kuma abubuwan da aka yi da tagulla.
14 “ ‘Mutanen Bet Togarma sun sayi kayan cinikinki da dawakai, dawakan yaƙi da alfadarai.
15 “ ‘Mutanen Dedan sun yi kasuwanci da ke, bakin teku masu yawa abokan cinikinki ne; sun biya ki da hauren giwa da katakon kanya.
16 “ ‘Mutanen Aram sun yi ciniki da ke saboda yawan kayanki; suka sayi kayan cinikinki da zumurrudu, da shunayya, da kayan ado, da lilin mai taushi, da murjani, da yakutu.
17 “ ‘Yahuda da Isra’ila sun yi kasuwanci da ke; sun sayi kayanki da alkama da Minnit da alawa, da zuma, da mai, da ganyaye masu ƙanshi.
18 “ ‘Mutanen Damaskus sun ga abin da za ki iya bayarwa sai suka yi ciniki da ke, ta sayi kayanki da ruwan inabi daga Helbon, da ulu daga Zahar.
19 Wedan da Yaban kusa da Uzal, suka sayi kayanki; wato gyararren ƙarfe da kayan yaji.
20 “ ‘Mutanen Dedan sun sayi kayanki da sirdin zama a kan dawakai.
21 “ ‘Mutanen Arabiya da dukan sarakunan Kedar abokan cinikinki ne; sun yi ciniki da ke suka sayi kayanki da ’yan raguna, da raguna, da awaki.
22 “ ‘’Yan kasuwan Sheba da Ra’ama sun yi ciniki da ke; suka sayi kayanki da kayan yaji mafi kyau iri-iri, da duwatsu masu daraja iri-iri, da zinariya.
23 “ ‘Haran, Kanne da Eden da kuma ’yan kasuwan Sheba, Assuriya da Kilmad sun yi ciniki da ke.
24 A kasuwarki sun yi ciniki da ke suka sayar miki tufafi masu tsada, da na shuɗi, da masu ado, da dardumai masu ƙyalƙyali da kirtani, da igiyoyi waɗanda aka tuƙa da kyau.
25 “ ‘Jiragen ruwan Tarshish sun zama
masu jigilar kayanki.
Kin cika da kaya masu nauyi
a tsakiyar teku.
26 Matuƙan jiragenki sun kai ki
can cikin manyan tekuna.
Amma iskar gabas za tă farfasa ki kucu-kucu
a tsakiyar teku.
27 Dukiyarki, cinikinki da kayan kasuwarki,
ma’aikatanki na jirgi, matuƙan jiragenki da masu tattoshe mahaɗan katakan jiragenki,
’yan kasuwarki da dukan sojojinki,
da kuma kowa da yake cikin jirgi
zai nutsa a tsakiyar teku
a ranar da jirginki zai nutse.
28 Ƙasashen bakin teku za su girgiza
sa’ad da matuƙan jirginki suka yi kuka.
29 Dukan waɗanda suke riƙe da matuƙi
za su ƙyale jiragensu;
ma’aikatan jirage da dukan matuƙan jirage
za su tsaya a bakin teku.
30 Za su tā da muryarsu
su yi kuka mai zafi a kanki;
za su yayyafa ƙura a kawunansu,
su yi ta birgima a cikin toka.
31 Za su aske kawunansu saboda ke
za su kuma sa tufafin makoki.
Za su yi kuka dominki su yi ɓacin rai
da kuma kuka mai zafi.
32 Yayinda suke kuka a kanki kuwa,
za su yi makoki dominki suna cewa,
“Wa ya taɓa yin shiru kamar Taya,
kewaye da teku?”
33 Sa’ad da kayan cinikinki suka tafi ƙasashen hayi,
kin gamsar da al’ummai masu yawa;
da dukiyarki masu yawa da kuma kayan cinikinki
kin azurtar da sarakunan duniya.
34 Yanzu teku ta farfashe ki
cikin zurfafan ruwaye;
kayan cinikinki da dukan kamfaninki
sun nutse tare da ke.
35 Dukan mazaunan bakin teku
sun giggice saboda masifarki;
sarakunansu sun tsorata ƙwarai
fuskokinsu kuwa sun yamutse don tsoro.
36 ’Yan kasuwa a cikin al’ummai suna yin miki tsaki;
kin zo ga mummunar ƙarshe
ba za ki ƙara kasancewa ba har abada.’ ”