26
Annabci a kan Taya
1 A shekara ta goma sha ɗaya, a rana ta fari ga wata, maganar Ubangiji ta zo mini cewa,
2 “Ɗan mutum, domin Taya ta yi magana a kan Urushalima ta ce, ‘Yauwa! Ƙofar zuwa al’ummai ta karye, an kuma buɗe mini ƙofofinta; yanzu da take kufai zan wadace,’
3 saboda haka ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa ina gāba da ke, ya Taya, zan kuwa kawo al’ummai masu yawa su yi gāba da ke, kamar yadda teku takan kawo raƙuman ruwa.
4 Za su hallaka katangar Taya su kuma rurrushe hasumiyoyinta; zan kankare tarkacenta, in maishe ta fā.
5 Za tă zama wurin shanya abin kamun kifi a tsakiyar teku, gama na faɗa, in ji Ubangiji Mai Iko Duka. Za tă zama ganima ga sauran al’ummai,
6 za a kashe mazaunan filin ƙasar da takobi. Ta haka za su san cewa ni ne Ubangiji.
7 “Gama ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa daga arewa zan kawo wa Taya Nebukadnezzar sarkin Babilon, sarkin sarakuna, tare da dawakai da kekunan yaƙi, da mahayan dawakai da babbar rundunar soja.
8 Zai kashe mazaunan filin ƙasar da takobi; zai yi miki ƙawanya, ya gina miki mahaurai, sa’an nan ya rufe ki da garkuwoyi.
9 Zai rushe katangarki da dundurusai, ya rurrushe hasumiyoyinki da makamai.
10 Dawakansa za su yi yawa har su rufe ke da ƙura. Katanga za su girgiza saboda motsin dawakan yaƙi, kekunan doki da keken yaƙin sa’ad da suka shiga birnin da aka rushe katangar.
11 Kofatan dawakansa za su tattake dukan titunanki; zai kashe mutanenki da takobi, ginshiƙanki masu ƙarfi kuma za su fāɗi a ƙasa.
12 Za su washe dukiyarki, kayan cinikinki kuma su zama ganima; za su rurrushe katangarki su ragargaza gidajenki masu kyau su kuma zubar da duwatsunki, katakanki da kuma tarkacenki a cikin teku.
13 Zan kawo ƙarshen waƙoƙinki masu surutu, ba kuwa za a ƙara jin kaɗe-kaɗen garayunki ba.
14 Zan maishe ki fā, za ki kuma zama wurin shanya abin kamun kifi. Ba za a sāke gina ki ba, gama Ni Ubangiji na faɗa, in ji Ubangiji Mai Iko Duka.
15 “Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa wa Taya. Ƙasashen da suke a bakin teku ba za su girgiza saboda ƙarar fāɗuwarki, sa’ad da nishin waɗanda aka yi wa rauni da kashe-kashen da aka yi a cikinki suka faru ba?
16 Sa’an nan sarakunan bakin teku za su sauka daga gadajen sarautarsu, su tuɓe rigunansu, da rigunansu waɗanda aka yi wa ado. Za su zauna a ƙasa suna rawar jiki a kowane lokaci suna razana saboda abin da ya same ki.
17 Sa’an nan za su yi makoki game da ke su ce,
“ ‘Yaya kika hallaka haka nan, ya birnin da ta yi suna,
cike da mutanen teku!
Ke da kika zama mai ƙarfi cikin tekuna,
ke da mazauna cikinki;
kin sa tsoronki
a kan dukan waɗanda suka zauna a can.
18 Yanzu tsibirai suna rawar jiki
a ranar fāɗuwarki;
tsibirai a cikin teku
sun tsorata a ɓacewarki.’
19 “Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa sa’ad da na maishe ki kufai, kamar sauran biranen da ba a ƙara zama a ciki, sa’ad da kuma na kawo zurfafan teku a kanki da yawan ruwansa suka rufe ki,
20 a sa’an nan zan sauko da ke ƙasa tare da waɗanda suke gangarawa zuwa rami, zuwa wurin mutanen dā. Zan sa ki zauna ƙarƙashin ƙasa, kamar a kufai na tun dā, tare da waɗanda suke gangarawa zuwa rami, ba kuwa za ki ƙara dawowa ba ko ki ɗauki matsayinki a ƙasar masu rai.
21 Zan sa ki yi mummunan ƙarshe kuma ba za ki ƙara kasancewa ba. Za a neme ki, amma ba za a ƙara same ki ba, in ji Ubangiji Mai Iko Duka.”