21
Babilon, takobin hukuncin Allah
1 Maganar Ubangiji ta zo mini cewa,
2 “Ɗan mutum, ka kafa fuskarka gāba da Urushalima ka kuma yi wa’azi a kan wuri mai tsarki. Ka yi annabci gāba da ƙasar Isra’ila
3 ka faɗa mata, ‘Ga abin da Ubangiji ya ce ina gāba da ke. Zan ja takobina daga kubensa in karkashe adalai da mugaye daga cikinki.
4 Domin zan karkashe adalai da kuma mugaye, ba zan rufe takobina a kan kowa daga kudu zuwa arewa ba.
5 Sa’an nan duka mutane za su san cewa Ni Ubangiji na ja takobina daga kubensa; ba zai sāke koma kuma ba.’
6 “Saboda ka yi nishi, ɗan mutum! Yi nishi a gabansu da ajiyar zuciya da ɓacin rai.
7 Kuma sa’ad da suka tambaye ka, ‘Me ya sa kake nishi?’ Sai ka ce musu, ‘Domin labarun da suke fitowa. Kowace zuciya za tă narke kowane hannu kuma ya gurgunta; kowane ruhu zai sume kowane gwiwa kuma ta rasa ƙarfi kamar ruwa.’ Yana zuwa! Tabbatacce zai faru, in ji Ubangiji Mai Iko Duka.”
8 Maganar Ubangiji ta zo mini cewa,
9 “Ɗan mutum, yi annabci ka ce, ‘Ga abin da Ubangiji ya faɗa,
“ ‘Takobi, takobi,
wasasshe da kuma gogagge,
10 wasasshe don kisa,
gogagge har yana walwal kamar walƙiya!
“ ‘Kada ku yi farin ciki, hukunci yana zuwa, domin kowa ya ƙi jin abin da na yi gargaɗi a kai.
11 “ ‘An ba da wannan takobi don a goge,
don a kama da hannu;
an washe shi aka kuma goge,
shiryayye don a yi kisa da shi.
12 Ka yi kuka ka yi makoki, ɗan mutum,
gama yana gāba da dukan sarakunan Isra’ila.
An jefa su ga takobi
tare da jama’ata.
Saboda haka ku buga ƙirjinku.
13 “ ‘Gwaji tabbatacce zai zo. Kuma a ce sandan Yahuda, wanda takobi ya ƙi, ya ci gaba? In ji Ubangiji Mai Iko Duka.’
14 “Saboda haka fa, ɗan mutum ka yi annabci
ka kuma tafa hannuwanka.
Bari takobi ya yi sara sau biyu,
har sau uku ma.
Takobin kisa ne,
takobi ne don kisa mai girma,
zai kewaye su a kowane gefe.
15 Domin zukata su narke
da yawa kuma su fāɗi,
na tsai da takobin kisa
a dukan ƙofofinsu.
Kash! A sa ya haska kamar walƙiya,
ana riƙe da shi don kisa.
16 Ya takobi, yi sara zuwa dama
ka yi kuma zuwa hagu,
duk inda aka juya ka.
17 Zan tafa hannuwana,
fushina kuwa zai sauka.
Ni Ubangiji na faɗa.”
18 Sai maganar Ubangiji ta zo mini cewa,
19 “Ɗan mutum, ka nuna hanyoyi biyu inda takobin sarkin Babilon zai bi, duka biyun su fara daga ƙasa guda. Ka kafa shaida inda hanyar za tă rabu zuwa cikin birni.
20 Ka nuna hanya guda wadda takobi zai fāɗo wa Rabba ta Ammonawa ɗayan kuma da zai fāɗo a kan Yahuda da kuma Urushalima mai katanga.
21 Gama sarkin Babilon zai tsaya a mararrabar hanya, a inda hanyar ta rabu biyu, don yă yi duba. Zai jefa ƙuri’a da kibiyoyinsa, zai nemi shawarar gumakansa, zai bincike hanta.
22 A hannunsa na dama ƙuri’a don Urushalima za tă fito, inda zai kafa dundurusai, ya ba da umarni kisa, a yi kururuwar yaƙi, a kafa dundurusai a kan ƙofofi, a gina mahaurai a kuma yi ƙawanya.
23 Zai zama kamar duban ƙarya ne ga waɗanda suka yi rantsuwar yin masa biyayya, amma zai tunashe su game da laifinsu ya kuma kama su.
24 “Saboda haka ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa, ‘Domin ku mutanen nan kun tuna da laifinku ta wurin tawaye, kun kuma bayyana zunubanku cikin dukan abin da kuke yi, domin kun yi haka, za a kama ku.
25 “ ‘Ya kai ƙazantaccen mugu, yerima Isra’ila, wanda kwanansa ta zo, wanda lokacin hukuncinsa ya cika fal,
26 ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa ka kunce rawanin, ka ɗauke rawanin nan. Ba zai zama kamar yadda yake ba. Za a ɗaukaka ƙasƙantacce, amma a ƙasƙantar da mai girma.
27 Hallaka! Hallaka! Zan hallaka shi! Ba za a maido da shi ba sai ya ga ainihin mai shi; gare shi zan bayar da shi.’
28 “Kai kuma, ɗan mutum, ka yi annabci ka ce, ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa game da Ammonawa da kuma zarginsu.
“ ‘Takobi, takobi,
an ja don kisa,
an goge don cinyewa
yana haske kamar walƙiya!
29 Duk da wahayin ƙarya game da kai,
duban ƙarya game da kai,
za a sa shi a wuyan
mugaye waɗanda za a kashe,
waɗanda kwanansu ta zo,
waɗanda lokacin hukuncinsu ya cika fal.
30 “ ‘Ka mai da takobi a kubensa.
A inda aka halicce ka,
a ƙasar kakanninka,
zan hukunta ka.
31 Zan zub da hasalata a kanka
in hura maka wutar fushina;
Zan ba da kai a hannun mugayen mutanen
da suka gwanince a hallakarwa.
32 Za ka zama itacen wuta,
za a zub da jininka a ƙasarka,
ba za a ƙara tuna da kai ba;
gama Ni Ubangiji na faɗa.’ ”