20
Isra’ila ’yan tawaye
1 A shekara ta bakwai, a wata na biyar a rana ta goma, waɗansu dattawan Isra’ila suka zo don su nemi nufin Ubangiji, suka kuwa zauna a ƙasa a gabana.
2 Sai maganar Ubangiji ta zo mini cewa,
3 “Ɗan mutum, ka yi magana da dattawan Isra’ila ka ce musu, ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa kun zo ne ku nemi shawarata? Muddin ina raye, ba zan bari ku nemi shawarata ba, in ji Ubangiji Mai Iko Duka.’
4 “Za ka hukunta su? Za ka hukunta su, ɗan mutum? To, sai ka kalubalance su da ayyukan banƙyamar kakanninsu
5 ka ce musu, ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa a ranar da na zaɓi Isra’ila, na ɗaga hannuna, na rantse wa zuriyar gidan Yaƙub na kuma bayyana kaina gare su a Masar da hannun da na ɗaga na ce musu, “Ni ne Ubangiji Allahnku.”
6 A ranar na yi musu rantsuwa cewa zan fitar da su daga Masar zuwa ƙasar da na samo musu, ƙasa mai zub da madara da zuma, ƙasa mafi kyau cikin dukan ƙasashe.
7 Na kuma ce musu, “Kowannenku ya zubar da mugayen siffofin da kuka kafa idanunku a kai, kuma kada ku ƙazantar da kanku da gumakan Masar. Ni ne Ubangiji Allahnku.”
8 “ ‘Amma sai suka yi tawaye a kaina ba su kuwa saurare ni ba; ba su zubar da mugayen siffofin da suka kafa idanunsu a kai ba, balle su ƙi gumakan Masar. Saboda haka zan zubo hasalata a kansu in kuma aukar musu da fushina a Masar.
9 Amma saboda sunana na yi abin da zai kiyaye shi daga ƙazantuwa a idanun al’umman da suka zauna a ciki da kuma a idanun al’ummai da na bayyana kaina ga Isra’ilawa ta wurin fitar da su daga Masar.
10 Saboda haka na fisshe su daga Masar na kawo su cikin hamada.
11 Na ba su ƙa’idodina na kuma sanar musu da dokokina, gama mutumin da ya yi biyayya da su zai rayu ta wurinsu.
12 Na kuma ba su Asabbataina kamar alama tsakaninmu, domin su san cewa Ni Ubangiji ne yake tsarkake su.
13 “ ‘Duk da haka mutanen Isra’ila suka yi mini tawaye a cikin hamada. Ba su bi ƙa’idodina ba amma suka ki dokokina, ko da yake mutumin da ya yi biyayya da su zai rayu ta wurinsu, suka ɓata Asabbataina ƙwarai. Saboda haka na ce zan zuba hasalata a kansu in kuma hallaka su a hamada.
14 Amma saboda sunana na yi abin da zai kiyaye shi daga ƙazantuwa a idanun al’umman da a idonsu na fisshe su.
15 Na kuma ɗaga hannu na rantse musu a hamada cewa ba zan kawo su ƙasar da na ba su ba, ƙasa mai zub da madara da zuma, ƙasa mafi kyau cikin dukan ƙasashe,
16 domin sun ƙi dokokina ba su kuwa bi ƙa’idodina ba suka kuma ƙazantar da Asabbataina. Gama zukatansu sun fi so su bauta wa gumakansu.
17 Duk da haka na dube su ta tausayi ba zan hallaka su ko in kawo ƙarshensu a hamada ba.
18 Na faɗa wa ’ya’yansu a hamada, “Kada ku bi farillai kakanninku ko ku kiyaye dokokinsu ko ku ƙazantar da kanku da gumakansu.
19 Ni ne Ubangiji Allahnku; ku bi ƙa’idodina ku kuma kula ku kiyaye dokokina.
20 Ku kiyaye Asabbataina da tsarki, don su zama alama tsakaninmu. Ta haka za ku san cewa ni ne Ubangiji Allahnku.”
21 “ ‘Amma ’ya’yan suka yi mini tawaye. Ba su bi ƙa’idodina ba, ba su kula su kiyaye dokokina ba, ko da yake mutumin da ya kiyaye su zai rayu ta wurinsu, suka kuma ƙazantar da Asabbataina. Saboda haka na ce zan zuba hasalata a kansu in kuma aukar musu da fushina a hamada.
22 Amma na janye hannuna, kuma saboda sunana na yi abin da zai kiyaye shi daga ƙazantuwa a idanun al’umman da a idonsu na fisshe su.
23 Na kuma ɗaga hannu na rantse musu cewa zan watsar da su cikin al’ummai in kuma warwatsa su cikin ƙasashe,
24 domin ba su kiyaye dokokina ba amma suka ƙi ƙa’idodina suka kuma ƙazantar da Asabbataina, idanunsu suka yi sha’awar gumakan kakanninsu.
25 Na kuma ba da su ga farillan da ba su da kyau da dokokin da ba za su rayu ta wurinsu ba;
26 na bari suka ƙazantu ta wurin kyautai, hadayar kowane ɗan fari don in cika su da abin tsoro domin su san cewa ni ne Ubangiji.’
27 “Saboda haka, ɗan mutum, ka yi magana da mutanen Isra’ila ka faɗa musu cewa, ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa a wannan kuma kakanninku suka saɓe ni ta wurin yashe ni.
28 Sa’ad da na kawo su cikin ƙasar da na rantse zan ba su suka kuma ga tudu mai tsawo ko itace mai ganye, a can suka miƙa hadayunsu, suka yi sadakokin da suka tsokane ni na yi fushi, suka miƙa turaren ƙanshinsu suka kuma zuba sadakokinsu na sha.
29 Sai na ce musu, Wane ɗakin tsafi kuke tafiya?’ ” (Ana ce da shi Bama har wa yau.)
Hukunci da Maidowa
30 “Domin haka ka faɗa wa gidan Isra’ila, ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa za ku ƙazantar da kanku yadda kakanninku suka yi ne ku yi sha’awar mugayen siffofinsu?
31 Sa’ad da kuka miƙa kyautai naku, hadayar ’ya’yanku maza a wuta, kuna cin gaba da ƙazantar da kanku da duka gumakanku har wa yau. Zan bari ku nemi shawarata, ya gidan Isra’ila? Muddin ina raye, in ji Ubangiji Mai Iko Duka, ba zan bari ku nemi shawarata ba.
32 “ ‘Kukan ce, “Kuna so ku zama kamar sauran al’ummai, kamar sauran mutanen duniya, waɗanda suke bauta wa itace da dutse.” Amma abin da kuke tunani ba zai taɓa faruwa ba.
33 Muddin ina raye, in ji Ubangiji Mai Iko Duka, zan yi mulki a kanku da hannu mai iko da kuma hannu mai ƙarfi da kuma fushi.
34 Zan fitar da ku daga al’ummai in tattara ku daga ƙasashe inda aka warwatsa ku, da hannu mai iko da kuma hannu mai ƙarfi da kuma fushi.
35 Zan kawo ku cikin hamadar al’ummai a can kuwa, fuska da fuska, zan hukunta ku.
36 Yadda na hukunta kakanninku a hamadar ƙasar Masar, haka zan hukunta ku, in ji Ubangiji Mai Iko Duka.
37 Zan lura da ku yayinda kuke wucewa ƙarƙashin sanda, zan kuma kawo ku cikin daurin alkawari.
38 Zan fitar da waɗanda suke mini tayarwa da kuma ’yan tawaye. Ko da yake zan fitar da su daga ƙasar da suke zama, duk da haka ba za su shiga ƙasar Isra’ila ba. Sa’an nan za ku san cewa ni ne Ubangiji.
39 “ ‘Game da ku, ya gidan Isra’ila, ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa ku tafi ku bauta wa gumakanku, kowannenku! Amma daga baya tabbatacce za ku saurare ni ba kuwa za ku ƙara ɓata sunana mai tsarki da hadayunku da gumakanku ba.
40 Gama a kan dutsena mai tsarki, dutse mai tsayi na Isra’ila, in ji Ubangiji Mai Iko Duka, a can a ƙasar gidan Isra’ila gaba ɗaya za su bauta mini, a can kuwa zan karɓe su. A can zan bukaci hadayunku da sadake sadakenku mafi kyau, tare da dukan tsarkakan hadayunku.
41 Zan karɓe ku kamar turare mai ƙanshi sa’ad da na fitar da ku daga al’ummai na kuma tattara ku daga ƙasashe inda aka warwatsa ku, zan kuma nuna kaina mai tsarki a cikinku a idon al’ummai.
42 Sa’an nan za ku san cewa ni ne Ubangiji sa’ad da na kawo ku cikin ƙasar Isra’ila, ƙasar da na ɗaga hannu na rantse zan ba wa kakanninku.
43 A can za ku tuna da halinku da kuma dukan ayyukanku waɗanda kuka ɓata kanku da su, za ku kuwa ji ƙyamar kanku saboda mugayen abubuwan da kuka aikata.
44 Za ku san cewa ni ne Ubangiji, sa’ad da na yi muku haka saboda sunana ba bisa ga mugayen hanyoyinku da ayyukanku marasa kyau ba, ya gidan Isra’ila, in ji Ubangiji Mai Iko Duka.’ ”
Annabci a kan kudu
45 Maganar Ubangiji ta zo mini cewa,
46 “Ɗan mutum, ka kafa fuskarka wajen kudu; ka yi wa’azi a kan kudu ka kuma yi annabci a kan kurmin ƙasar kudu.
47 Ka faɗa wa kurmin kudanci, ‘Ji maganar Ubangiji. Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa ina gab da sa maka wuta, za tă kuwa cinye dukan itatuwanki sarai, da ɗanye da busasshe. Ba za a kashe wutar da take ci ba, kuma kowace fuska a kudu zuwa arewa za tă ƙone.
48 Kowa zai san cewa Ni Ubangiji ne ya ƙuna ta; ba za a kashe ta ba.’ ”
49 Sai na ce, “Kash, Ubangiji Mai Iko Duka! Suna zance a kaina cewa, ‘Ba misalai kawai yake yi ba?’ ”