8
Kada ku manta da Ubangiji
1 Ku hankali, ku bi kowane umarnin da nake ba ku a yau, saboda ku rayu, ku ƙaru, ku kuma shiga, ku mallaki ƙasar da Ubangiji ya alkawarta da rantsuwa ga kakanninku.
2 Ku tuna yadda Ubangiji Allahnku ya bishe ku a dukan hanya, a cikin hamada waɗannan shekaru arba’in, don yă ƙasƙantar da ku, yă kuma gwada ku don yă san abin da yake a zuciyarku, ko za ku kiyaye umarnansa, ko babu.
3 Ya ƙasƙantar da ku, ya bar ku da yunwa, sa’an nan ya ciyar da ku da Manna, wadda ku, ko kakanninku, ba su sani ba, ta haka ne ya sa kuka sani cewa, ba da abinci kaɗai mutum zai rayu ba, amma ta wurin kowace kalmar da ta fito daga bakin Ubangiji.
4 Tufafinku ba su yayyage ba, ƙafafunku kuma ba su kumbura ba a waɗannan shekaru arba’in.
5 Sai ku sani fa a cikin zuciyarku cewa kamar yadda mutum kan horar da ɗansa, haka Ubangiji Allahnku ke horar da ku.
6 Ku kiyaye umarnan Ubangiji Allahnku, kuna tafiya cikin hanyoyinsa, kuna kuma girmama shi.
7 Gama Ubangiji Allahnku yana fitar da ku zuwa cikin ƙasa mai kyau, ƙasa mai rafuffuka da tafkunan ruwa, tare da maɓulɓulai masu gudu a kwari da tuddai;
8 ƙasa mai alkama da sha’ir, inabi da ɓaure, rumman, man zaitun da zuma;
9 ƙasa inda abinci ba zai yi ƙaranci ba, ba kuma za ku rasa kome ba; ƙasa ce inda ƙarfe ne duwatsunta, ana kuma haƙar tagulla a tuddanta.
10 Sa’ad da kuka ci, kuka ƙoshi, sai ku yabi Ubangiji Allahnku saboda ƙasa mai kyau da ya ba ku.
11 Ku yi hankali cewa ba ku manta da Ubangiji Allahnku, har ku kāsa kiyaye umarnansa, dokokinsa da ƙa’idodinsa da nake ba ku a wannan rana ba.
12 To, sa’ad da kuka ci, kuka ƙoshi, sa’ad da kuka gina gidaje masu kyau, kuka zauna,
13 sa’ad da kuma garkunanku na shanu da na tumaki suka ƙaru, azurfanku da zinariyarku kuma suka ƙaru, sa’an nan dukan abin da kuke da shi ya haɓaka,
14 to, sai ku lura, kada ku ɗaukaka kanku, har ku manta da Ubangiji Allahnku, wanda ya fitar da ku daga Masar, daga ƙasar bauta kuma.
15 Ya bishe ku cikin hamada mai fāɗi, mai bantsoro, wannan busasshiyar ƙasa wadda ba ta da ruwa, ga macizai masu dafi da kuma kunamai. Ya ba ku ruwa daga dutsen ƙanƙara.
16 Ya ba ku Manna don ku ci a cikin hamada, wani abin da kakanninku ba su taɓa sani ba, don yă ƙasƙantar yă kuma gwada ku, saboda yă yi muku alheri daga baya.
17 Wataƙila ku ce wa kanku, “Ikona da ƙarfin hannuwana ne suka ba ni da wannan arziki.”
18 Amma ku tuna da Ubangiji Allahnku, gama shi ne wanda yake ba ku azanci na yin arziki, ta haka kuwa ya tabbatar da alkawarinsa, wanda ya rantse wa kakanninku, kamar yadda yake a yau.
19 In kuka manta da Ubangiji Allahnku, kuka kuma bi waɗansu alloli, kuka yi musu sujada, kuka kuma rusuna musu, to, a yau ina gargaɗe ku cewa tabbatacce za a hallaka ku.
20 Kamar al’ummai da Ubangiji ya hallakar kafin ku, haka zai hallaka ku, domin ba ku yi biyayya da muryar Ubangiji Allahnku ba.