7
Korin al’ummai
(Fitowa 34.11-16)
1 Sa’ad da Ubangiji Allahnku ya kawo ku ƙasar da kuke shiga don ku mallaka, ya kuma kori al’ummai masu yawa a gabanku; wato, Hittiyawa, Girgashiyawa, Amoriyawa, Kan’aniyawa, Ferizziyawa, Hiwiyawa da Yebusiyawa, al’ummai bakwai masu girma da ƙarfi fiye da ku.
2 Sa’ad da kuma Ubangiji Allahnku ya ba da su gare ku, kuka kuma ci su da yaƙi, sai ku hallaka su ƙaƙaf. Kada ku yi yarjejjeniya da su, kada kuma ku nuna musu jinƙai.
3 Kada ku yi auratayya da su. Kada ku ba da ’ya’yanku mata wa ’ya’yansu maza, ko ku ɗauko ’ya’yansu mata wa ’ya’yanku maza.
4 Gama za su juye ’ya’yanku maza daga bina, su bauta waɗansu alloli, fushin Ubangiji kuma zai ƙuna a kanku da sauri, zai kuma hallaka ku.
5 Ga abin da za ku yi da su, za ku rurrushe bagadansu, ku ragargaza keɓaɓɓun duwatsunsu, ku farfashe ginshiƙan Asheransu, ku kuma ƙona gumakansu da wuta.
6 Gama ku mutane masu tsarki ne ga Ubangiji Allahnku. Ubangiji Allahnku ya zaɓe ku daga dukan mutane a fuskar duniya, don ku zama mutanensa, kayan gādonsa.
7 Ba don kun fi sauran al’ummai yawa ne ya sa Ubangiji ya ƙaunace ku, ya kuma zaɓe ku ba, gama ku ne mafi ƙanƙanta cikin dukan al’ummai.
8 Amma ya zama haka domin Ubangiji ya ƙaunace ku, ya kuma kiyaye rantsuwar da ya yi wa kakanninku da ya fitar da ku da hannu mai ƙarfi, ya kuma cece ku daga ƙasar bauta, daga ikon Fir’auna sarkin Masar.
9 Saboda haka, ku sani cewa Ubangiji Allahnku, shi ne Allah; shi Allah ne mai aminci, yana kiyaye alkawarinsa na ƙauna ga tsararraki dubu na waɗanda suke ƙaunarsa suke kuma kiyaye umarnansa.
10 Amma
waɗanda suke ƙinsa, a fili yakan sāka musu da hallaka;
ba zai yi jinkiri yin ramuwa a kan maƙiyinsa ba, zai yi ramuwar a fili.
11 Saboda haka, sai ku lura, ku bi umarnai, ƙa’idodi, da dokokin nan da nake ba ku a yau.
(Maimaitawar Shari’a 28.1-14; Firistoci 26.3-13)
12 In kuka mai da hankali ga waɗannan dokoki, kuka kuma yi hankali ga bin su, to, Ubangiji Allahnku zai kiyaye alkawarinsa na ƙauna gare ku, kamar yadda ya rantse wa kakanninku.
13 Zai ƙaunace ku, yă albarkace ku, yă kuma ƙara yawanku. Zai albarkaci ’ya’yanku, amfanin gonarku; hatsinku, sabon ruwan inabinku da kuma mai, ƙanana shanunku, da ’yan tumaki na tumakinku, a ƙasar da ya rantse wa kakanninku cewa zai ba ku.
14 Za a albarkace ku fiye da waɗansu mutane; babu wani cikin maza ko matanku da zai kasance babu haihuwa, ba kuwa wata dabbarku da za tă kasance babu haihuwa.
15 Ubangiji zai kiyaye ku daga kowace cuta. Ba zai wahalshe ku da mugayen cututtukan da kuka sani a Masar ba, amma zai aukar wa dukan maƙiyanku.
16 Dole ku hallaka dukan mutanen da Ubangiji Allahnku ya bashe su gare ku. Kada ku ji tausayinsu, kada kuma ku bauta wa allolinsu, gama wannan zai zama tarko gare ku.
17 Wataƙila ku ce wa kanku, “Waɗannan al’ummai sun fi mu ƙarfi. Yaya za mu kore su?”
18 Amma kada ku ji tsoronsu; ku tuna da kyau abin da Ubangiji Allahnku ya yi wa Fir’auna da kuma dukan Masar.
19 Kun ga da idanunku, manyan gwaje-gwaje, alamu masu banmamaki da al’ajabai, hannu mai ƙarfi da kuma mai ikon da Ubangiji Allahnku ya fitar da ku. Ubangiji Allahnku zai yi haka ga dukan mutanen da yanzu kuke tsoro.
20 Ban da haka ma, Ubangiji Allahnku zai aika da rina a cikinsu, har sai sun hallaka sauran mutanen da suka ragu, waɗanda suka ɓuya daga gare ku.
21 Kada ku tsorata saboda su, gama Ubangiji Allahnku, wanda yake a cikinku, Allah ne mai girma da kuma mai banrazana.
22 Da kaɗan da kaɗan Ubangiji Allahnku zai kore waɗannan al’ummai a gabanku. Ba a bari ku hallaka su duka gaba ɗaya ba, in ba haka namun jeji za su yaɗu kewaye da ku.
23 Amma Ubangiji Allahnku zai ba da su gare ku, yana jefa su cikin rikicewa mai girma, har sai an hallaka su.
24 Zai ba da sarakunsu a hannunku, za ku kuwa shafe sunayensu daga duniya. Babu wani da zai yi tsayayya da ku, za ku hallaka su.
25 Ku ƙone siffar allolinsu da wuta. Kada ku yi ƙyashin azurfa ko zinariyar da aka rufe allolin da ita, Kada ku kwashe su, don kada su zamar muku tarko, gama abin ƙyama ne ga Ubangiji Allahnku.
26 Kada ku kawo abin ƙyama cikin gidajenku, domin kada ku zama kamar su. Gaba ɗaya ku yi ƙyamarsu, ku ƙi su, gama an ware su, sun zama domin a hallaka.