4
Ina bada wannan umarni a gaban Allah da Yesu Almasihu, wanda zai yi wa rayayyu da matattu shari'a, kuma saboda bayyanuwarsa da mulkinsa: Ka yi wa'azin Kalma. Ka himmantu a kai ko da zarafi ko ba zarafi. Ka tsautar, ka kwabar, ka gargadar, da dukan hakuri da koyarwa. Gama lokaci na zuwa wanda mutane ba za su jure wa koyarwar kirki ba. Maimakon haka, zasu tattara wa kansu malamai bisa ga sha'awowin zuciyarsu. Za su rika fada masu abin da kunnuwansu ke so. Za su juya kunnuwansu daga koyarwar gaskiya, za su koma wa tatsunniyoyi na banza. Amma kai, sai ka natsu a cikin dukan abubuwa. Ka jure wa wahala; ka yi aikin mai bishara, ka cika hidimarka. Gama ana-tsiyaye ni. Lokacin yin kaurata yayi. Na yi tsere na gaskiya; na kuma kammala tseren; na rike bangaskiya. An adana mani rawani na adalci, wanda Ubangiji, alkali mai adalci, zai ba ni a ranan nan. Ba ni kadai ba, amma kuma ga dukkan wadanda suke kaunar zuwansa. Ka yi iyakacin kokarinka ka zo wurina da sauri. 10 Domin Dimas ya yashe ni. Ya kaunaci wannan duniyar, ya tafi Tassalonika, Kariskis ya tafi Galatiya, Titus kuma ya tafi Dalmatiya. 11 Luka ne kadai yake tare da ni. Ka nemo Markus ka zo tare da shi domin yana da amfani a gareni a cikin aikin. 12 Na aiki Tikikus zuwa Afisus. 13 Ka kawo mani mayafin da na bari a Taruwasa wurin Karbus, idan za ka zo ka taho da shi, duk da littatafan nan, musanman takardun nan. 14 Iskandari makerin dalma ya kulla mani makirci ba kadan ba. Ubangiji zai biya shi gwargwadon ayyukansa. 15 Kai ma ka yi hankali da shi, domin yana tsayyaya da maganganunmu sosai. 16 Da farkon kariyar kaina, babu wanda ya goyi bayana. Maimakon haka kowa ya guje ni. Bana so dai a lissafta wannan a kansu. 17 Amma Ubangiji ya kasance tare da ni, ya kuma karfafa ni, yadda ta wurina, shelar ta sami cika da kyau, domin dukan al'ummai su ji. An kwato ni daga bakin zaki. 18 Allah zai kubutar ni daga dukan ayyukan mugunta, ya kuma cece ni domin mulkinsa na sama. Daukaka ta tabatta a gareshi har abada abadin. Amin. 19 Ka gayar da Briskilla, da Akila, da gidan Onisifurus. 20 Arastus ya nan zaune a Korinti, amma na bar Turufimus ya na zazzabi a Militus. 21 Ka yi iyakar kokarinka, ka zo kamin hunturu. Yubulus yana gayar da kai, haka ma Budis da Linus da Kalafidiya da dukan 'yan'uwa. 22 Bari Ubangiji ya kasance tare da ruhunka. Bari Alheri ya kasance da kai.