6
Bari duk wadanda ke bayi a karkashin karkiya su ga iyayengijinsu sun cancanci dukan daraja. Su yi haka domin kada a sabawa sunan Allah da koyarwarsa. Bayin da suke da iyayengiji da ke masu ba da gaskiya kada su rena su saboda su 'yan'uwa ne. A maimakon haka, su yi masu hidima da kwazo. Gama iyayengijin da suke cin ribar aikinsu masu bi ne, kaunattatu kuma. Ka koyar ka kuma bayyana wadannan abubuwa. Idan ya kasance wani na koyar da wani abu dabam bai kuma yarda da amintaciyar koyarwa ba, wato maganar Ubangijinmu Yesu Almasihu. Alal misali ba su amince da koyarwa da ke kai ga Allahntaka ba. Wannan mutum mai girman kai ne, kuma bai san komai ba. A maimakon haka, yana da matukar jayayya da gardama game da kalmomi. Wadannan kalmomi na kawo kishi, da husuma, da zage-zage, da miyagun zace-zace, da yawan rashin jituwa tsakanin mutane masu rubabbun hankula. Sun bijire wa gaskiya. Suna tunani cewa ibada hanya ce ta yin arziki.” Ka zame daga wadannan abubuwa. Yanzu bin Allah tare da dangana babbar riba ce. Gama ba mu kawo komai a duniya ba, ba zamu iya fita cikinta da komai ba. A maimakon haka, mu dangana da abinci da kuma sutura. To wadanda ke son zama mawadata su kan fada cikin jaraba, cikin tarko. Suna fadawa cikin abubuwan wauta da sha'awoyi masu illa da kowanne abu da ke sa mutane su dulmaya cikin lallacewa da hallaka. 10 Gama son kudi shine tushen kowacce irin mugunta. Wadansu mutane garin neman kudi sun kauce daga bangaskiya, sun kuma jawowa kansu bakin ciki mai yawa. 11 Amma kai, mutumin Allah, ka guji wadannan abubuwa, ka bi adalci, ibada, aminci, kauna, jimiri, da tawali'u. 12 Ka yi fama, fama mai kyau na bangaskiya. Ka kama rai madawami da aka kira ka gare shi. A kan wannan ne ka ba da shaida a gaban shaidu masu yawa game da abin da ke da kyau. 13 Ina ba ka wannan umarni a gaban Allah wanda ke rayar da dukan abubuwa, da gaban Almasihu Yesu, wanda ya fadi abin da ke gaskiya ga Bilatus Babunti. 14 Ka bi doka daidai, babu abin zargi har bayanuwar Ubangijinmu Yesu Almasihu. 15 Allah zai nuna bayyanuwarsa a daidai lokaci- Allah, mai albarka, Makadaicin iko, Sarkin da ke sarauta, Ubangiji mai mulki. 16 Shine kadai marar mutuwa, mai zama cikin hasken da ba ya kusantuwa. Ba wanda ke ganinsa, ko ya iya hango shi. Girma ya tabbata a gare shi da kuma madawwamin iko. Amin. 17 Ka gaya wa masu dukiya a cikin wannan duniya kada su daga kai, kada su sa bege ga arziki mara dawwama. Maimamakon haka, su sa begensu ga Allah wanda ke ba mu wadatar gaske domin jin dadin mu. 18 Gaya masu su yi nagarta su arzurta a ayyuka nagari, su zama masu bayarwa hannu sake. 19 Ta haka za su ajiye wa kansu harsashi mai kyau kan abin da ke zuwa domin su amshi rayuwa ta kwarai. 20 Timoti, ka kare abin da aka ba ka. Ka nisanci maganar wauta da gardamomin da ke sabawa juna wanda ake kira ilimi a karyace. 21 Wadansu mutane suna shelar wadannan abubuwa, don haka sun kauce wa bangaskiyar. Bari alheri ya kasance tare da kai.