12
1 Ina rokon ku 'yan'uwa, saboda yawan jinkan nan na Allah, da ku mika jikunanku hadaya mai rai, mai tsarki kuma abar karba ga Allah. wannan itace hidimarku ta zahiri.
2 Kada ku kamantu da wannan duniya, amma ku sami canzawa ta wurin sabunta tunaninku, kuyi haka don ku san abin da ke nagari, karbabbe, kuma cikakken nufin Allah.
3 Don ina cewa, saboda alherin da aka bani, ka da waninku ya daukaka kansa fiye da inda Allah ya ajiye shi; a maimakon haka ku kasance da hikima, gwargwadon yadda Allah yaba kowa bangaskiya.
4 Domin muna da gababuwa da yawa a jiki daya, amma ba dukansu ne ke yin aiki iri daya ba.
5 haka yake a garemu, kamar yadda muke da yawa haka cikin jikin Almasihu, dukkanmu gabobin juna ne.
6 Muna da baye-baye dabam-dabam bisa ga alherin da aka bayar a gare mu. Idan baiwar wani anabci ne, yayi shi bisa ga iyakar bangaskiyarsa.
7 In wani yana da baiwar hidima, sai yayi hidimarsa. Idan baiwar wani koyarwa ce, yayi koyarwa.
8 Idan baiwar wani karfafawa ce, yayi ta karfafawa; Idan baiwar wani bayarwa ce, yayi ta da hannu sake; Idan baiwar wani shugabanci ne, yayi shi da kula; Idan baiwar wani nuna jinkai ne, yayi shi da sakakkiyar zuciya.
9 Ku nuna kauna ba tare da riya ba. Ku Ki duk abin da ke mugu ku aikata abin da ke nagari.
10 Akan kaunar 'yan'uwa kuma, ku kaunaci juna yadda ya kamata; akan ban girma kuma, ku ba juna girma.
11 Akan himma kuma, kada ku yi sanyi; akan ruhu kuma, ku sa kwazo; Game da Ubangiji kuma, ku yi masa hidima.
12 Akan gabagadi kuma, ku yi shi da farin ciki; akan tashin hankali kuma, ku cika da hakuri; akan adu'a kuma, ku nace.
13 Ku zama masu biyan bukatar tsarkaka, ku zama masu karbar baki a gidajenku.
14 Ku albarkaci masu tsananta maku, kada ku la'anta kowa.
15 Ku yi farinciki tare da masu farinciki; Ku yi hawaye tare da masu hawaye.
16 Tunanin ku ya zama daya. Kada tunaninku ya zama na fahariya, amma ku yi abokantaka da matalauta. Kada wani a cikin ku ya kasance da tunanin yafi kowa.
17 Kada ku rama mugunta da mugunta. Ku yi ayukan nagarta a gaban kowa.
18 Ku yi duk abin da za ku iya yi domin ku yi zaman salama tare da kowa.
19 'Yan'uwa, kada ku yi ramako, ku bar Allah ya rama maku. A rubuce yake, '' 'Ramako nawa ne; zan saka wa kowa,' in ji Ubangiji.''
20 ''Amma idan makiyin ka na jin yunwa, ba shi abinci ya ci. Idan yana jin kishin ruwa, ba shi ruwan sha. Idan kun yi haka, garwashin wuta ne za ku saka akan duk makiyi.''
21 Kada mugunta ta rinjaye ku, amma ku rinjayi mugunta ta wurin yin aikin nagarta.