2
Annabawan karya sun zo ga mutane, hakannan kuma malaman karya suma sun zo. A asirce za su zo maku da karkatacciyar koyarwa mai hallakarwa, su kuma yi musun sanin Ubangiji da ya fanshe su. Su na jawowa kansu hallaka da sauri. Da yawa za su bi gurbinsu, kuma ta wurinsu za a sabawa sahihiyar gaskiya. Ta wurin hadama za su ribace ku ta wurin maganganunsu na yaudara. Hallakarsu ba za ta yi jinkiri ba; hukuncinsu na nan tafe. Allah bai kebe mala'ikkun da suka yi zunubi ba. Maimakon haka ya tura su a cikin bakin duhun jahannama daure da sarkoki, har ya zuwa ranar shari'a. Hakan nan kuma bai kebe duniya ta zamanin da ba. Maimakon haka, ya kebe Nuhu, wanda yake wa'azin adalci, tare da mutane bakwai, lokacin da ya kawo ambaliyar ruwan Tsufana a fuskar duniyar marasa bin Allah. Sa'annan Allah ya kone biranen Sadoma da Gomrata da wuta ya maishe su toka, wannan ya zama misalin abin da zai faru da marasa ibada. Amma ga adalinnan Lutu, wanda ya zaku a ransa ta wurin miyagun halayen mutanen, Ubangiji kuwa ya cece shi. Ga wannan mutum mai adalci, wanda yayi zama a cikinsu kowace rana ransa na baci, domin abin da yake gani yake kuma ji. Saboda haka Allah ya san yadda zai ceci masu adalci daga gwaji, da yadda kuma zai kama masu rashin adalci da hukunci a ranar shari'a. 10 Wannan kuwa musamman gaskiya ce ga wadanda suka ci gaba da ayyuka na jiki suka kuma raina masu mulki. Suna da taurin kai da kuma yin ganin dama. Ba sa tsoron sabo ga wadanda aka daukaka. 11 Ko da shike mala'iku suna da karfi da iko fiye da su, amma basu kawo karar batanci a kansu a gaban Ubangiji ba. 12 Amma wadannan dabbobi marassa tunani an yi su ne musamman domin a kama a yanka. Suna sabawa abin da ba su sani ba. Zasu halaka. 13 Za su sami sakamakon mugun aikinsu. Suna tunanin yin nishadi da rana abin annashuwa ne. Su kan su tababbu ne. Suna jin dadin ayyukansu na yaudara yayin da suke liyafa tare da ku. 14 Suna da idanun sha'awace sha'awacen mata mazinata; ba sa koshi da aikata zunubi. Suna rinjayar wandanda ba su da tsayayyan hankali zuwa ga munanan ayyuka, kuma sun kafa zukatansu ga hadama, su 'ya'yan la'ana ne! 15 Sun bar bin hanyar gaskiya. Sun bijire kuma sun bi hanyar Bal'amu dan Be'or wanda yake kaunar ribar rashin adalci. 16 Amma ya karbi tsautawa domin zunubinsa. Jaki ma da baya magana ya tsauta wa haukan annabin da muryar dan adam. 17 Wadannan mutane suna kamar mabulbullai da babu ruwa. suna nan kamar gizagizai da iska ke korawa. Duhu mai tsanani yana jiransu. 18 Su masu babatu ne da girman kai. suna yadaurar mutane ta wurin sha'awowin jiki. Suna yaudarar mutane da suke kokarin su tsere daga wadanda suke rayuwa cikin kuskure. 19 Suna masu alkawarin yanci, amma su da kan su bayi ne ga zunubi. Domin mutum bawa ne ga duk abinda ya rinjaye shi. 20 Duk wanda ya kubuta daga shashanci na duniya ta wurin sanin Ubangiji da mai Ceto Yesu Almasihu, sa'annan ya koma cikin shashaci, yanayinsu na karshe ya zama da muni fiye da na farkon. 21 Da ma zai fi masu kada su san hanyar adalci da su san ta amma sa'annan su juya daga ka'ida mai tsarki wanda aka damka masu. 22 Wannan karin magana ya zama gaskiya a kan su: “Kare ya dawo yana lashe amansa. Aladen da akayi masa wanka ya koma cikin tabo.”