4
Saboda haka, tunda yake Almasihu ya sha wuya a jiki, muma mu sha damara da wannan ra'ayi. Duk wanda ya sha wuya a jiki ya daina aikata zunubi. Wannan mutum kuma baya kara zaman biye wa muguwar sha'awar mutumtaka, amma sai dai nufin Allah dukkan sauran kwanakinsa a duniya. Gama lokaci ya wuce da zamu yi abin da al'ummai suke son yi, wato fajirci, mugayen sha'awace-sha'awace, da buguwa da shashanci da shaye-shaye da bautar gumaku da abubuwan kyama. Suna tunanin bakon abu ku ke yi da ba kwa hada kai tare da su yanzu a yin wadannan abubuwa, sai suna zarginku. Za su bada lissafi ga wanda yake a shirye ya shari'anta masu rai da matattu. Shi yasa aka yi wa matattu wa'azin bishara, cewa ko da shike anyi masu shari'a cikin jikunan mutane, su rayu bisa ga Allah a ruhu. Karshen dukkan abubuwa yana gabatowa. Saboda haka, ku zama natsatsu, ku natsu cikin tunaninku domin yin addu'oi. Gaba da kome, ku himmatu wajen kaunar juna, domin kauna bata neman tona zunuban wadansu. Ku yi wa juna bakunta da abubuwa nagari ba tare da gunaguni ba. 10 Yadda kowanne dayanku ya sami baiwa, kuyi amfani da su domin ku kyautata wa juna, kamar masu rikon amanar bayebaye na Allah, wanda ya ba mu hannu sake. 11 Idan wani yana yin wa'azi, ya zamana fadar Allah ya ke fadi, idan wani yana hidima, ya yi da karfin da Allah ya ba shi, domin cikin dukkan abubuwa a daukaka Allah ta wurin Yesu Almasihu. Daukaka da iko nasa ne har abada abadin. Amin. 12 Ya kaunatattu, kada ku zaci cewa matsananciyar wahalar da ta zo ta gwada ku bakon abu ne, ko kuma wani bakon abu ne yake faruwa a gareku. 13 Amma muddin kuna tarayya da Almasihu cikin wahalarsa, ku yi murna, domin kuyi farin ciki da murna sa'adda za a bayyana daukakarsa. 14 Idan ana zargin ku sabili da sunan Almasihu, ku masu albarka ne, domin Ruhun daukaka da Ruhun Allah ya tabbata a kanku. 15 Amma kada kowannen ku ya sha wahala sabo da horon shi mai kisan kai ne, ko barawo, ko mamugunci, ko mai shisshigi. 16 Amma in wani yana shan wahala sabili da shi na Almasihu ne, kada ya ji kunya, amma ya daukaka Allah a wannan sunan. 17 Domin lokaci ya yi da shari'a za ta fara daga gidan iyalin Allah. Idan kuwa za a fara da mu, menene karshen wadanda suka ki biyayya da bisharar Allah? 18 Idan mutum, “mai adalci ya tsira da kyar, to, me zai faru da marar bin Allah da mai zunubi kuma?” 19 Sabo da haka bari wadanda suke shan wuya bisa ga nufin Allah, su mika rayukansu ga amintaccen Mahalicci suna kuma yin ayyuka nagari.