2
Saboda haka sai ku tube dukkan keta, rikici, da riya, kishi, da dukkan mugun zance. Kammar jarirai, sababbin haihuwa, ku yi marmarin madara mai ruhaniya wadda take sahihiya, domin ta wurinta kuyi girma zuwa ceto, idan kun dandana Ubangiji mai-alheri ne. Kuzo gareshi rayayyen dutse wanda mutane suka ki, amma zababbe ne mai-daraja wurin Allah. Ku kuma kamar rayayyun duwatsu ana gina ku gida mai ruhaniya, domin ku zama tsarka-kan fristoci, domin ku mika hadayu masu ruhaniya abin karba ga Allah ta wurin Yesu Almasihu. Gama nassi ya ce, “Ga shi na sanya dutse na kan kusurwa, zababe, mai daraja a cikin Sihiyona. Duk wanda ya bada gaskiya gareshi ba zaya kunyata ba.” Daraja a gareku take ku da kun bada gaskiya. Amma, ga wadanda suka ki bada gaskiya, “Dutsen da magina suka ki shine aka mai she shi kan kusurwa”. kuma, “Dutsen sa tuntube da fa na sa tuntube. “Sun yi tuntube, da shike sun ki biyayya da maganar, an kuwa kaddara su ga wannan. Amma ku zababben jinsi ne, kungiyar fristoci ba-sarauci, al'umma mai-tsarki, jama'ar mallakar Allah, domin ku sanar da mafifitan al'amuran wanda ya kiraye ku daga chikin duhu zuwa cikin haskensa mai'ban al'ajibi. 10 Ku da ba jama'a ba ne a da, amma yanzu jama'ar Allah ne. Da baku sami jinkai ba, amma yanzu kun sami jinkai. 11 Kaunatattu, ina rokon ku misalin baki da masu-tafiya kuma, ku guje wa sha'awoyin jiki wadanda ke yaki da rai. 12 Ku kasance da kyakkyawan hali a cikin al'ummai, domin, sa'adda suke kushen ku kamar masu aikata mugunta, sai su lura da nagargarun ayyukanku su kuma daukaka Allah a ranar zuwansa. 13 Kuyi biyayya ga kowacce hukuma ta mutane sabili da Ubangiji, ko ga sarki domin shi ne shugaba. 14 Ko kuwa ga masu mulki aikakkunsa ne domin su hori masu aikata mugunta da yabawa masu aikata nagarta. 15 Gama wannan nufin Allah ne, ta wurin aikin kirki ku, kwabi jahilcin mutane marassa hikima. 16 Kamar 'yan'tattu kada ku mori 'yan'cinku kamar mayafin mugunta, amma ku zama kamar bayin Allah. 17 Ku girmama dukkan mutane. Ku kaunaci 'yan'uwa, kuji tsoron Allah. Ku girmama sarki. 18 Ku barori, kuyi biyayya ga iyayen gidanku da dukkan bangirma, ba ga nagargaru da masu saukin kai ba, amma har ga miskilai. 19 Gama abin yaba wa ne idan sabili da lamiri zuwa ga Allah in wani ya jimre da shan zalunci. 20 Gama wacce riba ke nan idan kun yi zunubi ana horonku kuna jimrewa da hukuncin? amma idan kunyi aikin kirki kuka sha wuya a kansa kuka yi hakuri, wannan abin karba ne wurin Allah. 21 Gama akan haka aka kiraye ku, gama Almasihu ma yasha azaba saboda ku, ya bar maku gurbi kubi sawunsa. 22 Bai taba yin zunubi ba, ba'a taba jin yaudara a bakinsa ba. 23 Da'a ka zage shi bai mai da zagi ba. Da ya sha azaba, bai yi kashedi ba, amma ya mika kansa ga wanda yake yin shari'ar adalci. 24 Shi da kansa ya dauki zunubanmu a cikin jiki nasa ya kai su bisa itace, domin kada a iske mu cikin zunubi, amma muyi rayuwa ga adalci. Ta wurin raunukansa ne kuka warke. 25 Dukkanku da kun bata kuna yawo kamar batattun tumaki, amma yanzu kun dawo wurin makiyayi da mai tsaron rayukanku.