27
1 Da gari ya waye, duk manyan firistoci da dattawan jama'a suka shirya yadda zasu kulla makirci domin su kashe shi.
2 Suka daure shi, suka mika shi ga gwamna Bilatus.
3 Sa'adda Yahuza, wanda ya bashe shi, ya ga an zartarwa Yesu hukuncin kisa, ya nemi tuba ya kuma mayar da azurfar talatin ga manyan firistocin da dattawan,
4 yace, “Na yi zunubi ta wurin cin amanar mara laifi.” Amma sukace, “Ina ruwan mu? Ka ji da shi da kanka?”
5 Sai ya jefar da kwandalolin azurfar a kasa cikin haikalin ya kuma bar su, ya tafi ya rataye kansa.
6 Sai babban firist ya dauki kwandalolin azurfar ya ce, “Ba daidai bane bisa ga shari'a musa wannan cikin ma'aji, saboda kudin jini ne.”
7 Sai suka tattauna al'amarin a tsakanin su, kudin kuma suka sayi filin maginin tukwane domin makabatar baki.
8 Dalilin wannan ne ake kiran wurin, “Filin jini” har yau.
9 Sai abin da aka fada ta bakin annabi Irmiya ya cika, cewa, “Suka dauki tsabar azurfa talatin na farashin da mutanen Isra'ila suka sa a kansa,
10 suka bayar domin sayen filin mai tukwane, kamar yadda Ubangiji ya umarce ni.”
11 Sai Yesu ya tsaya a gaban gwamna, gwamna ya kuma tambaye shi, “Kai sarkin Yahudawa ne?” Yesu ya amsa, “Haka ka fada.”
12 Amma da manyan firistocin da dattawan suka zarge shi, bai ce komai ba.
13 Sai Bilatus yace masa, “Baka ji dukan zarge-zargen da ake yi maka ba?”
14 Amma bai ce masa ko kalma guda ba, sai gwamna yayi matukar mamaki.
15 To lokacin bikin idi, al'adar gwamna ne ya saki mutum guda wanda jama'a suka zaba.
16 A wannan lokacin suna da wani sanannen dan kurkuku mai suna Barabbas.
17 To da suka tattaru, sai Bilatus yace masu, “Wa kuke so a sakar maku? Barabbas, ko Yesu wanda ake kira Almasihu?”
18 Saboda ya san sun kawo shi ne domin kishi.
19 Da yake zaune a kujerar shari'a, matarsa ta aika masa cewa, “Ka fita sha'anin mutumin nan marar laifi. Saboda na sha wahala sosai a yau cikin mafarki saboda shi.”
20 A lokacin nan manyan firistoci da dattawa suka rinjayi ra'ayin jama'a suce a sakar masu da Barabbas, a kashe Yesu.
21 Sai gwamna ya tambayesu, “Wa kuke so a sakar maku?” Sukace, “Barabbas.”
22 Bilatus yace masu, “Me zan yi da Yesu wanda ake kira Almasihu?” Sai duka suka amsa, “A gicciye shi.”
23 Sai yace, “Don me, wane laifi ya aikata?” Amma suka amsa da babbar murya, “A gicciye shi”
24 Amma da Bilatus ya ga ba zai iya komai ba don hargitsi zai iya barkewa, ya dauki ruwa ya wanke hannuwansa a gaban jama'a, yace, “Ba ni da laifi ga jinin mutumin nan marar laifi. Ku yi abin da kuka ga dama.”
25 Duka mutanen sukace, “Bari jininsa ya kasance a kan mu da 'ya'yan mu.”
26 Sai ya sakar masu da Barabbas amma yayi wa Yesu bulala ya mika shi garesu domin su gicciye shi.
27 Sai sojojin gwamna suka dauki Yesu zuwa farfajiya suka kuma tara dukan rundunar sojoji.
28 Suka yi masa tumbur sa'annan suka sa masa jar alkyabba.
29 Sai suka yi masa rawanin kaya suka sa a kansa, suka kuma bashi sanda a hannunsa na dama. Suka rusuna a gabansa suna masa ba'a, suna cewa, “Ranka ya dade, Sarkin Yahudawa!”
30 Suka kuma tofa masa yawu, suka kwace sandar suka buga masa a ka.
31 Bayan sun gama masa ba'a, suka cire masa alkyabbar suka sa masa kayansa, suka jagorance shi zuwa wurin da za a gicciye shi.
32 Da suka fito waje, sai suka iske wani Bakurame mai suna Saminu, wanda suka tilasta ya tafi tare dasu domin ya dauki gicciyen.
33 Suka iso wani wuri da ake kira Golgotta, wanda ke nufin,”Wurin kwalluwa.”
34 Suka bashi ruwan inabi da aka gauraya da wani abu mai daci. Amma da ya 'dan-'dana shi sai ya ki sha.
35 Bayan da suka gicciye shi, suka kada kuri'a a kan rigarsa.
36 Suka kuma zauna suna kallonsa.
37 A sama da kansa suka sa abinda ake tuhumarsa da ita a rubuce, “Wannan shine sarkin Yahudawa.”
38 An gicciye shi da 'yanfashi guda biyu, daya ta damansa dayan kuma ta hagunsa.
39 Wadanda suke wucewa suna zaginsa, suna girgiza kai,
40 suna kuma cewa, “Kai da kace zaka rushe haikali ka kuma gina shi a kwana uku, ka ceci kanka mana! In dai kai Dan Allah ne, ka sauko daga gicciyen!”
41 Ta haka ma manyan firistocin suka rika yi masa ba'a, tare da marubuta da shugabannin, suna cewa,
42 “Ya ceci wasu amma ya kasa ceton kansa. Shi ne sarkin Isra'ila. Ya sauko mana daga kan gicciyen, sai mu ba da gaskiya gareshi.
43 Tun da ya yarda da Allah. Bari Allahn ya cece shi mana, saboda yace, “Ni dan Allah ne.”
44 Hakan nan ma 'yanfashin guda biyu da aka gicciye su tare suka zage shi.
45 To tun da tsakar rana sai duhu ya rufe kasar gaba daya har karfe uku na yamma.
46 Wajen karfe uku, Yesu ya tada murya mai karfi yace, “Eli, Eli lama sabaktani?” wanda ke nufin, “Allahna, Allahna, don me ka yashe ni?”
47 Da wadanda suke tsaye kusa suka ji haka, sai sukace, “Yana kiran Iliya.”
48 Nan take wani ya ruga da gudu ya dauki soso ya tsoma cikin ruwan inabi mai tsami ya soka kan sandar kara ya mika masa ya sha.
49 Sai sauran sukace, “Rabu da shi mu gani ko Iliya zai zo ya cece shi.”
50 Sai Yesu ya ta da murya mai karfi yayi kuka sai ya saki ruhunsa.
51 Sai labullen haikali ya yage gida biyu daga sama zuwa kasa. Kasa kuma ta girgiza, duwatsu suka farfashe.
52 Kaburbura suka bude, tsarkaka kuwa wadanda suke barci da yawa suka tashi.
53 Suka fito daga kaburbura bayan tashinsa, suka shiga birni mai tsarki suka bayyana ga mutane da yawa.
54 Da hafsan sojan da wadanda suke kallon Yesu suka ga girgizar kasar da abinda ya faru, suka ji tsoro kwarai sukace, “Hakika wannan Dan Allah ne”
55 Mata dayawa da suka bi Yesu daga Galili domin su lura da shi suka tsaya suna kallo daga nesa.
56 A cikin su akwai Maryamu Magadaliya, Maryamu uwar Yesu da Yusufu, da uwar 'ya'yan Zabadi.
57 Da yamma sai wani attajiri mutumin Armatiya ya zo, mai suna Yusufu wanda shi ma almajirin Yesu ne.
58 Ya je wurin Bilatus ya roka a bashi jikin Yesu. Sai Bilatus ya umarta a bashi.
59 Yusufu ya dauki jikin, ya rufe shi da likafani mai tsabta,
60 sai ya sa shi a cikin sabon kabarinsa da ya sassaka cikin dutse. Sai ya mirgina babban dutse a bakin kofar kabarin ya tafi.
61 Maryamu Magadaliya da dayan Maryamun suna nan zaune akasin kabarin.
62 Washegari, wato bayan ranar Shiri, Sai manyan firistoci da Farisawa suka taru tare da Bilatus.
63 Sukace, “Mai gida, mun tuna lokacin da mayaudarin nan yake da rai, yace, “Bayan kwana uku zan tashi.”
64 Saboda haka, ka bada umarni a tsare kabarin na kwana uku. In ba haka ba almajiransa zasu zo su sace shi, kuma su ce wa mutane, “Ya tashi daga mattatu.” Kuma yaudarar karshe zata fi ta farko muni.”
65 Bilatus yace masu, “Ku dauki masu tsaro. Kuyi tsaro iyakar karfin ku.”
66 Sai suka tafi suka tsare kabarin, suka hatimce dutsen, suka sa masu tsaro.