25
1 Sa'annan mulkin sama zai zama kamar budurwai goma da suka dauki fitilunsu domin su taryi ango.
2 Biyar daga cikin su masu hikima ne biyar kuma wawaye.
3 Sa'adda wawayen budurwai suka dauki fitilunsu, ba su dauki karin mai ba.
4 Amma budurwai masu hikimar suka dauki gorar mai tare da fitilunsu.
5 To da angon ya makara, dukkan su sai suka fara gyangyadi sai barci ya dauke su.
6 Amma da tsakkar dare sai aka yi shela, 'Ga ango ya iso! Ku fito taryensa.
7 Sai dukka budurwan nan suka tashi suka gyaggyara fitilunsu.
8 Wawayen su ka ce da masu hikimar, 'Ku sammana kadan daga manku gama fitilunmu su na mutuwa.'
9 “Amma masu hikimar suka ce 'Tun da man ba zai ishe mu tare da ku ba, sai ku je gun ma su sayarwa ku sayo wa kanku.
10 Sa'adda suka tafi sayan man, sai angon ya shigo, kuma wadanda suke a shirye su ka shiga tare da shi bukin auren, sai aka rufe kofar.
11 Bayan dan lokaci kadan sauran budurwan suka dawo suna cewa, 'Mai gida, mai gida, bude mana kofar.'
12 Amma ya amsa ya ce, 'A gaskiya ina gaya maku, ni ban san ku ba.'
13 Don haka sai ku lura, don baku san rana ko sa'a ba.
14 Domin yana kama da wani mutum da zai tafi wata kasa. Ya kira barorinsa ya ba su dukiyar sa.
15 Ga wani ya ba shi talanti biyar, ga wani ya ba shi biyu, ga wani kuma ya ba shi talanti daya. kowa an bashi gwargwadon iyawarsa, sai wannan mutum ya yi tafiyar sa
16 nan da nan sai wanda ya karbi talanti biyar ya sa nasa a jari, ya sami ribar wasu talanti biyar.
17 Haka ma wanda ya karbi talanti biyu ya sami ribar wasu biyu.
18 Amma bawan da ya karbi talanti dayan ya yi tafiyar sa, ya haka rami, ya binne kudin mai gidansa.
19 To bayan tsawon lokaci sai ubangidan barorin nan ya dawo, domin yayi lissafin kudinsu.
20 Bawan da ya karbi talanti biyar, ya kawo nasa da ribar wasu biyar. Yace, 'Maigida, ka bani talanti biyar, gashi na samo ribar karin talanti biyar.'
21 Maigidansa yace masa, 'Madalla, bawa na gari mai aminci! Ka yi aminci akan abu kadan. Zan sa ka akan abubuwa masu yawa. Ka shiga cikin farincikin maigidanka.'
22 Bawan da ya karbi talanti biyun, ya zo yace, 'Maigida, ka ba ni talanti biyu. Gashi kuwa na sami karin ribar wasu biyun.'
23 Ubangidansa yace masa, 'Madalla, kai bawa na gari mai aminci! Ka yi aminci akan abubuwa kadan. Zan saka akan abubuwa masu yawa. Ka shiga cikin farincikin maigidanka.'
24 Sai bawan da ya karbi talanti daya ya zo yace, 'Maigida, na san kai mai tsanani ne. Kana girbi inda baka yi shuka ba, kuma kana tattarawa inda ba ka watsa ba.
25 Na ji tsoro, don haka sai na je na boye talantinka a rami. Duba, ga abinda yake naka.'
26 Amma ubangidansa ya amsa yace, kai mugu malalacin bawa, ka san cewa ni mai girbi ne inda ban shuka ba kuma ina tattarawa inda ban zuba ba.
27 To da ba sai ka kai kudina a banki ba, da bayan na dawo da sai in karbi abina da riba.
28 Saboda haka ku kwace talantin daga gare shi ku baiwa mai talanti goman nan.
29 Gama ga wanda yake da shi za'a kara masa har ma a yalwace za'a kara bashi. Amma ga wanda bashi da komai abinda ke nasa ma za'a kwace.
30 Ku jefa wannan mugun bawan marar amfani, cikin duhu mai zurfi, inda ake kuka da cizon hakora.'
31 Sa'adda Dan mutum zai zo cikin daukakarsa da dukan Mala'iku tare da shi, sa'annan zai zauna kursiyinsa na daukaka.
32 A gabansa za'a tattara dukkan al'ummai, zai rarraba mutanen daya'daya, kamar yadda makiyayi yake rarraba tumaki daga awaki.
33 Zai sa tumakin a hannunsa na dama, amma awakin a hannunsa na hagu.
34 Sa'annan sarkin zai ce wa na hannun damarsa, 'Ku zo ku da Ubana ya albarkata, ku gaji mulkin da aka shirya maku kafin a kafa duniya.
35 Gama na ji yunwa kuka bani abinci; Na ji kishi kuka bani ruwa; Na yi bakunci kun bani masauki;
36 Na yi huntanci kuka tufasar dani; Na yi ciwo kuka kula dani; Ina kurkuku kuka ziyarceni.'
37 Sa'annan masu adalcin za su amsa su ce, 'Ubangiji, yaushe muka ganka kana jin yunwa muka baka abinci? Ko kana jin kishi muka baka ruwan sha?
38 Kuma yaushe muka ganka kana bakunci har muka baka masauki? Ko kuma kana huntanci da muka tufatar da kai?
39 Yaushe kuma muka ganka kana ciwo ko a kurkuku har muka ziyarce ka?'
40 Sa'annan Sarkin zai amsa masu yace, 'Hakika Ina gaya maku, duk abinda kuka yi wa daya mafi kakanta daga cikin 'yan'uwana a nan ni kuka yi wa.'
41 Sa'annan zai cewa wadanda suke hannunsa na hagu, 'Ku rabu da ni, ku la'anannu, ku tafi cikin wutar jahannama da aka shirya wa Shaidan da aljannunsa,
42 domin ina jin yunwa baku bani abinci ba; ina jin kishi ba ku bani ruwa ba;
43 Ina bakunci amma baku bani masauki ba; ina huntanci, baku tufasar da ni ba; ina ciwo kuma ina kurkuku, baku kula da ni ba.'
44 Sa'annan suma zasu amsa su ce, 'Ubangiji, yaushe muka ganka kana jin yunwa, ko kishin ruwa, ko kana bakunci, ko kana huntanci, ko ciwo, kuma a kurkuku, da bamu yi maka hidima ba?'
45 Sa'annan zai amsa ya ce masu, 'Ina gaya maku hakika abin da baku iya yiwa mafi karanta daga cikin wadannan ba, ba ku yi mani ba.'
46 Wadannan kuwa zasu tafi cikin madawwamiyar azaba amma adalai zuwa rai madawwami.”