18
1 Daidai wannan lokacin, almajiran suka zo wurin Yesu suka ce, ''Wanene mafi girma a mulkin sama?''
2 Sai Yesu ya kira karamin yaro gunsa, ya sa shi a tsakaninsu,
3 ya ce, ''Hakika ina gaya maku, idan baku juya kun zama kamar kananan yara ba, babu yadda zaku shiga mulkin sama.
4 Saboda haka, duk wanda ya kaskantar da kansa kamar karamin yaron nan, shi ne mafi girma a mulkin sama.
5 Duk wanda ya karbi karamin yaro a suna na, ya karbe ni.
6 Amma duk wanda ya sa daya daga cikin 'yan yaran nan da suka gaskanta da ni zunubi, gwamma a rataya dutsen nika a wuyansa a jefa shi cikin zurfin teku.
7 Kaiton duniya saboda lokacin tuntube! Lallai ne wadannan lokuta su zo, amma kaiton mutumin da ta wurinsa ne wadannan lokutan za su zo!
8 Idan hannunka ko kafarka ce za ta sa ka tuntube, ka yanke ta, ka yar daga gare ka. Zai fi maka kyau ka shiga rai da nakasa ko gurguntaka, da a jefa ka cikin madawwamiyar wuta tare da hannayenka ko kafafunka.
9 Idan idonka zai sa ka tuntube, ka kwakule shi, ka yar. Zai fi maka kyau ka shiga rai da ido daya, da a jefa ka cikin madawwamiyar wuta da idanu biyu.
10 Ku kula fa kada ku rena kananan nan. Domin koyaushe a sama, mala'ikunsu na duban fuskar Ubana da ke sama.
11 [Dan Mutum ya zo ya ceci abinda ya bata].
12 Menene tunaninku? Idan mutum na da tumaki dari, sa'annan daya ta bata, ashe ba zai bar tassa'in da tara a gefen tudu ya tafi neman wadda ta bata ba?
13 In ya same ta, hakika ina gaya maku, farin cikinsa na samun dayan nan da ta bace, zai fi na tassa'in da taran nan da basu bata ba.
14 Hakanan fa, ba nufin Ubanku dake sama ba ne da ya daga cikin wadannan kananan ya hallaka.
15 Idan dan'uwanka yayi maka laifi, fada masa tsakaninku, kai da shi kadai. Idan ya saurare ka, ka maido da dan'uwanka kenan.
16 Amma in ya ki ya saurare ka, ka je da 'yan'uwa biyu ko uku su zama shaidu, don ta wurin shaidu biyu ko uku ake tabbatar da kowacce kalma.
17 In kuma ya ki ya saurare su, ka kai lamarin ga ikklisiya. Idan ya ki ya saurari ikklisiya, ka maishe shi ba'al'umme da mai karbar haraji.
18 Hakika ina gaya maku, duk abin da kuka daure a duniya, a daure yake a sama. Abin da kuka kwance kuma, a kwance yake a sama.
19 Kuma ina gaya maku, idan mutum ku biyu zaku yarda akan duk abin da zaku roka, Ubana wanda ke a sama zai yi maku shi.
20 Wurin da mutum biyu ko uku suka taru a cikin sunana, zan kasance tare da su.''
21 Bitrus ya zo ya ce wa Yesu, ''Ubangiji, sau nawa ne dan'uwana zai yi mani laifi in gafarta masa? Har sai ya kai sau bakwai?''
22 Yesu ya amsa ya ce masa, ''Ban gaya maka sau bakwai ba, amma bakwai din ma har sau saba'in.
23 Saboda haka, za a kwatanta mulkin sama da wani sarki da yake so ya lisafta dukiyarsa dake a hannun barorinsa.
24 Da ya fara yin haka, sai aka kawo masa daya daga cikin barorinsa da yake binsa talanti dubu goma.
25 Amma tunda ba shi da abin biya, ubangidansa ya bada umurni a sayar da shi, tare da matarsa da 'ya'yansa da duk mallakarsa, domin a biya.
26 Sai baran ya fadi kasa, ya rusuna a gaban ubangidansa ya ce, “Maigida, kayi mani hakuri, zan biya duk abin da na karba.”
27 Don haka ubangidansa yayi juyayi, sai ya ce, ya yafe bashin, a saki baran.
28 Amma bayan an saki wannan baran, ya je ya sami wani baran kamar sa da yake bi bashin dinari dari. Ya cafke shi, ya shake shi a wuya, ya ce, 'Ka biya bashin da nake bin ka.'
29 Amma dan'uwansa bara ya roke shi ya ce, kayi mani hakuri, zan biya ka duk abinda na karba.'
30 Amma baran nan na farko ya ki. A maimakon haka, ya sa aka jefa dan'uwansa bara a kurkuku sai ya biya bashin nan.
31 Da sauran barori suka ga abin da ya faru, suka damu kwarai. Sai suka je suka fada wa ubangidansu yadda abin ya faru duka.
32 Sai ubangidansa ya kirawo shi, ya ce masa, ''Kai mugun bawa, na gafarta maka bashin nan duka, domin ka roke ni.
33 Ashe, bai kamata kaima ka nuna jinkai ga dan'uwanka bara kamar yadda na nuna maka jinkai ba?'
34 Ubangidansa yayi fushi, ya danka shi ga masu azabtarwa, har sai ya gama biyan dukan bashin da ake binsa.
35 Hakanan Ubana dake a sama zai yi maku, idan kowannenku bai gafarta wa dan'uwansa daga zuciya ba.''