18
1 Ya kuma ba su wani misali cewa ya kamata kullum su yi addu'a kada kuma su karaya,
2 yace, “A wani gari an yi wani alkali mara tsoron Allah, kuma baya ganin darajan mutane.
3 Akwai wata mace gwauruwa a wannan garin, wadda ta rika zuwa wurinsa, tana ce masa, 'Ka taimake ni yanda zan sami adalci a kan abokin gaba na.'
4 An dade bai so ya taimaka mata, amma daga baya sai ya ce a ransa, 'ko da yake ba na tsoron Allah, ba na kuma darajanta mutane,
5 duk da haka saboda gwauruwar nan ta dame ni, zan taimake ta domin ta sami adalci, yadda ba za ta gajiyar da ni da zuwanta wurina ba.'”
6 Sai Ubangiji ya ce, “Ku ji fa abin da alkalin nan marar gaskiya ya fada.
7 A yanzu Allah ba zai biya wa zababbunsa da suke yi masa kuka dare da rana hakkinsu ba? Zai yi jinkiri a wajen taimakonsu ne?
8 Ina gaya maku, zai biya masu hakkin su da wuri. Amma sa'adda Dan Mutum ya zo, zai tarar da bangaskiya a duniya?”
9 Ya sake ba da misalin nan ga wadansu masu amincewa da kansu, wai su masu adalci ne, har suna raina sauran mutane,
10 “Wadansu mutane biyu suka shiga haikali domin yin addu'a - daya Bafarise, dayan kuma mai karbar haraji ne.
11 Sai Bafarisen ya mike, ya yi addu'a a kan wadannan abubuwa game da kansa, 'Allah, na gode maka, da cewa ni ba kamar sauran mutane dake mazambata ba, ko marasa adalci, ko mazinata, ko kamar wannan mai karbar harajin.
12 Duk mako ina azumi sau biyu. Nakan bayar da zakkar dukan abin da na samu.'
13 Amma mai karbar harajin kuwa yana tsaye daga can nesa, bai yarda ya daga kai sama ba, sai dai yana bugun kirjin sa, yana cewa, 'Allah, ka yi mini jinkai, ni mai zunubi.'
14 Ina gaya maku, wannan mutum ya koma gidansa baratacce, ba kamar dayan ba, domin dukan wanda ya daukaka kansa, za a kaskantar da shi, amma duk wanda kaskantar da kansa kuwa daukaka shi za a yi.”
15 Sai mutanen suka kawo masa jariransu, domin ya taba su, da almajiransa suka ga haka, sai suka kwabe su.
16 Amma Yesu ya kira su wurinsa, ya ce, “Ku bar yara kanana su zo wurina, kada ku hana su. Ai mulkin Allah na irin su ne.
17 Gaskiya ina gaya maku, duk wanda bai karbi mulkin Allah kamar karamin yaro ba, lallai ba zai shige shi ba.”
18 Wani shugaban jama'a ya tambaye shi ya ce “Malam managarci, me zan yi in gaji rai Madawwami?”
19 Yesu ya ce masa, “Don me ka kira ni managarci? Babu wani managarci sai Allah kadai.
20 Ka dai san dokokin - kada ka yi zina, kada ka yi kisankai, kada ka yi sata, kada ka yi shaidar karya, ka girmama mahaifinka da mahaifiyarka.”
21 Sai shugaban ya ce, “Dukan wadannan abubuwa na kiyaye su tun a kuruciya ta.”
22 Da Yesu ya ji haka, ya ce masa, “Abu daya ne kadai ya rage maka. Dole ne ka sayar da dukan mallakarka, ka rarraba wa gajiyayyu, za ka kuma sami wadata a sama - sa'annan ka zo ka biyoni.”
23 Amma da mai arzikin ya ji wadannan abubuwa, sai yayi bakin ciki kwarai, don shi mai arziki ne sosai.
24 Yesu kuwa, da ya ga ransa ya baci, sai ya ce, “Yana da wuya masu dukiya su shiga mulkin Allah!
25 Zai zama da sauki rakumi ya shiga kafar allura, da mai arziki ya shiga mulkin Allah.”
26 Wadanda suka ji wannan magana suka ce, “Idan hakane wa zai sami ceto kenan?”
27 Yesu ya amsa, “Abin da ya fi karfin mutum, mai yiwuwa ne a gun Allah.”
28 Sai Bitrus ya ce, “To, ga shi mun bar mallakarmu, mun bi ka.”
29 Yesu ya ce masu, “Hakika, ina gaya maku, ba wanda zai bar gida, ko matarsa, ko 'yan'uwansa, ko iyayensa, ko kuma 'ya'yansa, saboda mulkin Allah,
30 sa'annan ya kasa samun ninkin ba ninkin a duniyan nan, da rai na har abada a duniya mai zuwa.”
31 Bayan da ya tara su goma sha biyun nan, ya ce masu, “Ga shi, muna tafiya zuwa Urushalima, duk abubuwan da aka rubuta game da Dan Mutum ta hannun annabawa zasu tabbata.
32 Gama za a bashe shi ga al'ummai, a yi masa ba'a, a wulakanta shi, a kuma tofa masa miyau.
33 Za su yi masa bulala, su kashe shi, a rana ta uku kuma zai tashi.”
34 Amma ba su fahimci ko daya daga cikin wadannan abubuwa ba, domin zancen nan a boye yake daga garesu, ba su ma gane abin da aka fada ba.
35 Da ya kusato Yariko, ga wani makaho zaune a gefen hanya, yana bara,
36 da ya ji taro na wucewa, sai ya tambaya ko menene.
37 Suka ce masa Yesu Banazarat ne yake wucewa.
38 Sai makahon ya ta da murya mai karfi, ya ce, “Yesu, Dan Dauda, ka yi mani jinkai.”
39 Sai wadanda suke gaba suka kwabe shi, suna gaya masa ya yi shiru. Amma ya kara daga murya kwarai da gaske, yana cewa, “Dan Dauda, ka yi mani jinkai.”
40 Sai Yesu ya tsaya, ya umarta a kawo shi wurinsa. Da makahon ya zo kusa, sai Yesu ya tambaye shi,
41 “Me kake so in yi maka?” Ya ce, “Ubangiji, ina so in samu gani.”
42 Yesu ya ce masa, “Karbi ganin gari, bangaskiyarka ta warkar da kai.”
43 Nan take ya samu gani, ya bi Yesu, yana daukaka Allah. Ganin haka, sai duk jama'a suka yabi Allah.