18
1 Bayan Yesu ya fadi wadannan maganganu, ya fita shi da almajiransa zuwa daya barayin kwarin Kidiron, inda wani lambu ya ke, ya kuma shiga da almajiransa.
2 Yahuza ma wanda zai bashe shi ya san wurin, domin Yesu ya saba zuwa wurin da almajiransa.
3 Yahuza kuwa, bayan ya dauko kungiyar soja daga manyan firistoci, da Farisawa, da 'yan majalisa, suka zo wurin, rike da fitilu, da cociloli, da makamai.
4 Sai Yesu, da ya san duk abinda ke faruwa da shi, yayiwo gaba, yace masu, ''Wa kuke nema''
5 Suka amsa masa su ka ce, ''Yesu Banazare'' Yesu yace masu, Ni ne'' Yahuza kuma, wanda ya bashe shi, yana tsaye tare da sojojin.
6 Sa'adda ya ce masu, ''Ni ne'', suka koma da baya, suka fadi a kasa.
7 Ya sake tambayarsu kuma, ''Wa ku ke nema?'' su ka ce, ''Yesu Banazare.''
8 Yesu ya amsa, ''Ai, na gaya maku cewa, Ni ne. In kuwa ni ku ke nema, ku bar wadannan su tafi abinsu;''
9 Wannan kuwa domin maganar daya fada ta cika, ''Daga cikin wadanda ka ba ni, ko daya bai bace mani ba.''
10 Saminu Bitrus kuwa, da ya ke yana da takobi, ya zaro ya kai wa bawan babban firist sara, ya dauke masa kunnensa na dama, sunan bawan Malkus ne.
11 Yesu ya ce wa Bitrus, ''Mai da takobin ka kubenta. Ba zan sha kokon da Uba ya ba ni ba.'?
12 Sai sojojin da hafsan, da 'yan majalisar Yahudawa, suka kama Yesu, suka daure shi.
13 Da fari suka tafi da shi wurin Hanana, don shi surukin Kayafa ne, wanda ya ke shi ne babban firist a shekaran nan.
14 Kayafa kuma shi ne ya ba Yahudawa shawara, cewa ya fiye masu mutum daya ya mutu domin mutane.
15 Saminu bitrus ya bi bayan Yesu, haka kuma wani almajirin yayi. Almajirin nan kuwa sananne ne ga babban firist, sai ya shiga har farfajiyar babban firist din tara da Yesu;
16 Amma bitrus kuwa ya tsaya a bakin kofa daga waje. Sai daya almajirin da ya ke sananne ga babban firist ya fita, yayi magana da macen da ta ke tsaron kofar, sa'an nan ya shigo da Bitrus.
17 Sai yarinyar mai tsaron kofar ta ce wa Bitrus, ''kai ma ba kana cikin almajiran mutumin nan ba?'' Yace ''bani ba.''
18 To, barorin da dogaran Haikali suna tsaye a wurin, sun kuwa hura wutar gawayi, suna jin dumi, gama ana sanyi. Bitrus ma yana tsaye tare da su yana jin dumin.
19 babban firist ya tambayi Yesu game da almajiransa da koyarwarsa kuma.
20 Yesu ya amsa masa, Ai, na yi wa duniya magana a bayyane. Na kuma sha koyarwa a majami'u da Haikali in da Yahudawa duka sukan taru. Ban fadi komai a boye ba.
21 Don me kake tambaya ta? Ka tambayi wadanda suka saurare ni a kan abinda na fada, ai, sun san abinda na fada.
22 Sa'adda Yesu ya fadi wannan, wani daga cikin 'yan majalisar da ke tsaye a wurin ya nushi Yesu, yace, ''Kana amsa wa babban firist haka.''
23 Yesu ya amsa masa yace, ''Idan na fadi mugun abu to, ka bada shaida kan hakan. In kuwa dai dai na fada, to, dan me za ka nushe ni?''
24 Sai Hanana ya aika daYesu a daure wurin Kayafa, babban firist.
25 To Saminu Bitrus yana tsaye yana jin dumin. Mutanen kuwa suka ce masa, ''Anya kai ma ba cikin almajiransa ka ke ba?'' Sai yayi musu yace, ''A'a, ba na ciki.''
26 Sai wani daga cikin bayin babban firist, wato dan'uwan wanda Bitrus ya fillewa kunne, yace, ''Ashe, ban gan ka tare da shi a lambun ba?
27 Bitrus ya sake yin musu, nan da nan kuwa zakara yayi cara.
28 Daga wurin Kayafa kuma suka kai Yesu fadar Gwamna. Da asuba ne kuwa, su kansu ba su shiga fadar Gwamnan ba, wai don kada su kazantu su kasa cin jibin Ketarewa.
29 Sai bilatus fa ya fita zuwa wurinsu, yace, 'Wane zargi ku ke kawowa akan mutumin nan?'
30 ''Sai suka amsa suka ce, ''idan da mutumin nan bai yi mugun abu ba, me zai sa mu yi kararsa a wurin ka''
31 bilatus yace masu, ''Ku tafi da shi da kan ku mana, ku hukunta shi bisa ga shari'arku!'' Sai Yahudawa su kace masa, ''Ai, ba mu da ikon zartar da hukuncin kisa akan kowa.''
32 Sun fadi Wannan ne don a cika maganar da Yesu yayi, wadda ta kwatanta irin mutuwar da zai yi.
33 Sai bilatus ya sake shiga cikin fadar Gwamnan, ya kira Yesu ya ce masa, ''kai sarkin Yahudawa ne?''
34 Yesu ya amsa, '' wannan fadarka ce, ko kuwa wadansu ne suka ce da ni haka a wurinka?''
35 Bilatus ya amsa “Ni ba Bayahude bane, ko kuwa?'' Ai, jama'arka ne da manyan firistoci suka bashe ka gareni. ''Me ka yi?''
36 Yesu ya amsa, ''Mulkina ba na duniya nan ba ne. Da mulkina na duniyan nan ne da barorina za su yi yaki kada a bashe ni ga Yahudawa. To, mulkina ba daga nan ya ke ba.''
37 Sai Bilatus yace masa, ''Wato ashe, sarki ne kai?'' Yesu ya amsa, ''Yadda ka fada, ni sarki ne. Domin wannan dalili aka haife ni, domin kuma wannan dalili na zo cikin duniya, don in bada shaida game da gaskiya. Kowane mai kaunar gaskiya kuma yakan saurari muryata.''
38 Bilatus yace masa, ''Menene gaskiya?'' Bayan da ya fadi haka, ya sake fitowa wurin Yahudawa, yace masu, ''Ni kam, ban sami mutumin nan da wani laifi ba.
39 Amma dai kuna da wata al'ada, in Idin Ketarewa ya yi, na kan sakar maku mutum daya. To, kuna so in sakar maku sarkin Yahudawa?''
40 Sai suka sake daukar kururuwa suna cewa, ''A; a, ba wannan mutum ba, sai dai Barabbas.'' Barabbas din nan kuwa dan fashi ne.