13
Kamin bukin idin ketarewa, sa'adda Yesu ya san lokaci ya yi da zai tashi daga wannan duniya zuwa wurin Uba, da yake ya kaunaci nasa wadanda ke duniya- ya kaunace su har karshe. Iblis ya rigaya ya sa a zuciyar Yahuza Iskariyoti dan Saminu, ya bashe da Yesu. Ya san cewa Uba ya bada kome a hannunsa, kuma ya zo daga wurin Allah, kuma zai koma wurin Allah. Ya tashi daga cin abincin, ya tube tufafinsa, ya dauki tawul ya lullube kansa da shi. Sa'an nan ya zuba ruwa a bangaji, ya fara wanke kafafun almajiran, yana shafe su da tawul din da ya lullube jikinsa da shi. Ya zo wurin Bitrus Saminu, sai Bitrus ya ce masa,”Ubangiji, za ka wanke mani kafa?” Yesu ya amsa ya ce, “Abin da nake yi ba za ka fahimce shi yanzu ba, amma daga baya za ka fahimta.” Bitrus ya ce masa, “Ba za ka taba wanke mani kafa ba.” Yesu ya amsa masa ya ce, “In ban wanke maka ba, ba ka da rabo da ni”. Bitrus ya ce masa, “Ubangiji, ba kafafuna kadai za ka wanke ba, amma da hannayena da kaina.” 10 Yesu ya ce masa, “Duk wanda ya yi wanka ba ya da bukata, sai dai a wanke kafafunsa, amma shi tsarkakakke ne baidaya; ku tsarkakakku ne, amma ba dukanku ba.” 11 (Don Yesu ya san wanda zai bashe shi, shiyasa ya ce, “Ba dukanku ne ke da tsarki ba.”) 12 Bayan Yesu ya wanke masu kafafu, ya dauki tufafinsa ya zauna kuma, ya ce masu, “Kun san abin da na yi muku? 13 kuna kirana, 'Malam, da Ubangiji,' kun fadi daidai, don haka Nake. 14 Idan ni Ubangiji da kuma mallam, na wanke maku kafafu, ya kamata kuma ku wanke wa junan ku kafafu. 15 Gama na baku misali, saboda ku yi yadda na yi maku. 16 Lalle hakika ina gaya muku, bawa ba ya fi mai gidansa girma ba; dan aike kuma ba ya fi wanda ya aiko shi girma ba. 17 Idan kun san wadannan abubuwa, ku masu albarka ne idan kun aikata su. 18 Ba ina magana akan dukanku ba; Na san wadanda na zaba. Amma domin Nassi ya cika: 'Shi Wanda ya ci gurasata, ya tayar mani'. 19 Ina fada maku wannan yanzu tun kafin haka ta faru domin sa'adda ta faru, ku gaskata Ni ne. 20 Hakika, hakika, Ina gaya maku, wanda ya karbi wanda na aiko, Ni ya karba, wanda kuma ya karbe ni, ya karbi wanda ya aiko ni. 21 Bayan Yesu ya fadi haka, ya damu a ruhu, ya yi shaida ya ce, “Lalle hakika, ina gaya muku cewa daya daga cikinku zai bashe ni.” 22 Almajiran suka kalli juna, suna juyayin ko akan wa yake magana. 23 Daya daga cikin almajiransa, wanda Yesu yake kauna, yana a teburi, jingine a kirjin Yesu. 24 Siman Bitrus ya ce wa almajirin, “ka fada mana ko akan wa ya ke magana.” 25 Sai ya sake jingina a kirjin Yesu, ya ce masa, “Ubangiji, wanene?” 26 Sannan Yesu ya amsa, “Shine wanda zan tsoma gutsuren gurasa in ba shi.” Sannan bayan ya tsoma gurasar, sai ya ba Yahuza Dan Siman Iskariyoti. 27 To bayan gurasar, sai shaidan ya shige shi, sai Yesu ya ce masa, “ Abinda kake yi, ka yi shi da sauri.” 28 Babu wani a teburin da ya san dalilin dayasa ya fada masa wannan. 29 Wadansu sun yi tsamanin cewa, tun da Yahuza ne ke rike da jakkar kudi, Yesu ya ce masa, “Ka sayi abinda muke bukata don idin”, ko kuma ya bada wani abu domin gajiyayyu. 30 Bayan Yahuza ya karbi gurasar, sai ya fita nan da nan. Da daddare ne kuwa. 31 Bayan Yahuza ya tafi, Yesu ya ce, “Yanzu an daukaka Dan mutum, kuma an daukaka Allah a cikinsa. 32 Allah zai daukaka shi a cikin kansa, kuma zai daukaka shi nan da nan. 33 'Ya'ya kanana, ina tare da ku na wani gajeren lokaci. Zaku neme ni, kuma kamar yadda na fadawa Yahudawa, 'in da zan tafi ba za ku iya zuwa ba.' Yanzu kuma na fada maku wannan. 34 Ina baku sabuwar doka, ku kaunaci juna; kamar yadda na kaunace ku, haka kuma ku kaunaci juna. 35 Ta haka kowa zai san ku almajiraina ne, idan kuna kaunar juna.” 36 Siman Bitrus ya ce masa, “Ubangiji, ina za ka?” Yesu ya amsa ya ce, “Inda za ni, ba zaka iya bi na ba yanzu, amma zaka bini daga baya.” 37 Bitrus ya ce masa, “Ubangiji, don me ba zan iya binka a yanzu ba? Zan bada raina domin ka.” 38 Yesu ya amsa ya ce, “ Za ka bada ranka domina? Lalle hakika, ina gaya maka, kafin zakara ya yi cara zaka yi musu na sau uku.”