10
“Hakika, Hakika, ina ce maku, wanda bai shiga ta kofa zuwa garken tumaki ba, amma ya haura ta wata hanya, wannan mutum barawo ne da dan fashi. Wanda ya shiga ta kofa shine makiyayin tumakin. Mai gadin kofar zai bude masa. Tumakin suna jin muryarsa, ya na kuma kiran tumakinsa da sunayensu, ya kuma kai su waje. Bayanda ya kawo su duka a waje, yana tafiya a gabansu, sai tumakin su bi shi, domin sun san muryarsa. Ba za su bi bako ba amma sai dai su guje shi, domin basu san muryar baki ba.” Yesu ya yi masu magana da wannan misali, amma basu gane wadannan abubuwa da yake gaya masu ba. Sai Yesu ya ce masu kuma, “Hakika, Hakika, Ina ce maku, Ni ne kofar tumaki. Dukan wadanda suka zo kamin ni barayi ne da yan fashi, amma tumakin ba su ji su ba. Ni ne kofa, In kowa ya shiga ta wurina, zai sami ceto, zai shiga ya fita ya kuma sami wurin kiwo. 10 Barawo ba ya zuwa sai don ya yi sata, ya kashe, ya kuma hallakar. Na zo ne domin su sami rai su kuma same shi a yalwace. 11 Ni ne makiyayi mai kyau. Makiyayi mai kyau yana bada ransa domin tumakinsa. 12 Wanda yake dan sako kuma, ba makiyayi ba, wanda ba shine mai tumakin ba, in ya ga kyarkeci na zuwa sai ya saki tumakin ya gudu. Sai kyarkecin ya dauke su ya kuma warwatsa su. 13 Ya gudu domin shi mai aikin kudi ne kuma bai damu da tumakin ba. 14 Nine makiyayi mai kyau, na kuma san nawa, nawa kuma sun san ni. 15 Uban ya san ni, ni ma na san Uban, na kuma bada raina domin tumakin. 16 Ina da wadansu tumaki wadanda ba na wannan garken ba. Wadannan, kuma, dole in kawo su, su ma za su ji muryata saboda za su zama garke daya da makiyayi daya. 17 Domin wannan ne Uban yake kauna ta: Na bada raina domin in same shi kuma. 18 Babu wanda zai dauke shi daga wurina, amma ina bayar da shi da kaina. Ina da ikon bada shi, ina da iko in dauke shi kuma. Na karbi wannan umarnin daga wurin Ubana.” 19 Tsattsaguwa ta sake tashi tsakanin Yahudawa domin wadannan kalmomin. 20 Dayawa a cikinsu suka ce, yana da aljani, kuma mahaukaci ne. Don me ku ke sauraronsa?” 21 Wadansu suka ce, wadannan ba kalmomin wanda yake da aljani ba ne. Ko mai aljani zai iya bude idanun makaho?” 22 Sai lokacin idin Tsarkakewa a Urushalima ya zo. 23 A lokacin damuna ne, Yesu kuwa yana tafiya a shirayi cikin haikalin Sulaimanu. 24 Sai Yahudawa suka zagaye shi suka ce masa, “Har yaushe ne za ka bar mu cikin shakka? In kai ne Almasihun, ka gaya mana dalla-dalla.” 25 Yesu ya ce masu, “Na gaya maku, amma baku gaskata ba. Ayyukan da nake yi a cikin sunan Ubana, su ke yin shaida a kaina. 26 Duk da haka baku gaskata ba domin ku ba tumakina ba ne. 27 Tumakina suna jin murya ta; Na san su, suna kuma bi na. 28 Ina ba su rai na har abada; ba za su taba mutuwa ba, babu wanda zai kwace su daga hannu na. 29 Ubana, wanda ya bani su, ya fi kowa girma, kuma ba mai iya kwace su daga hannun Uban. 30 Ni da Uban daya ne.” 31 Sai Yahudawa suka dauki duwatsu kuma domin su jajjefe shi. 32 Yesu ya amsa masu, “Na nuna maku kyawawan ayyuka masu yawa daga wurin Uban. Saboda wane daga cikin wadannan ayyukan kuke jefe ni?” 33 Sai Yahudawa suka amsa masa, “ba don wani aiki mai kyau muke son mu jefe ka ba, amma don sabo, domin kai, mutum ne, amma kana mayar da kanka Allah.” 34 Yesu ya amsa masu, “Ba a rubuce yake a shari'arku ba, 'Na ce, “ku alloli ne”'?” 35 In ya kira su alloli, su wadanda maganar Allah ta zo gare su (kuma ba za a iya karya nassi ba), 36 kuna gaya wa wanda Uban ya kebe ya kuma aiko cikin duniya, 'Kana sabo', domin Na ce, 'Ni dan Allah ne'? 37 In ba na aikin Ubana, kada ku gaskata ni. 38 Amma, idan ina yin su, ko ba ku gaskata da ni ba, ku gaskata da ayyukan saboda ku sani, ku kuma gane cewa Uban yana ciki na, ni kuma ina cikin Uban.” 39 Suka sake kokarin kama shi, amma ya yi tafiyarsa, ya fita daga hannunsu. 40 Ya yi tafiyarsa kuma har gaba da kogin Urdun zuwa inda Yahaya ke yin baftisma ada, ya kuma zauna a wurin. 41 Mutane masu yawa suka zo wurinsa, suka ce,”Hakika Yahaya bai yi wasu alamu ba, amma dukan abubuwan da Yahaya ya ce game da wannan mutum gaskiya ne.” 42 Mutane dayawa suka bada gaskiya gare shi a wurin.